part 27

356 45 0
                                    

🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁
    *NAMIJIN ZAKI*
🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁

   By
_Nafisa Aliyu_
    *(mrs Naseer)*

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*📚🖊️

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.
'''🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
______________________________________

Page 26

*Wannan page din sadaukarwa ne ga Maman Mufy da Maman Baby. Allah ya bar kauna. #onelove*💖♥

Kwana daya kwana 2 shiry shiru babu angi babu labarinsa. Tun abin yana bawa Fulani haushi har ya fara bata tsoro. Ita kam ya zatai da rayuwarta??  Wayarta ta dauko domin kiran Mummyn ta. Tayi dialing number kenan Zahra ta shigo parlorn da sallama fuskarnan babu yabo babu fallasa. Ita ma Fulanin amsawa tayi, tana ganinta tasan wace ita domin ko babu komai sun bala'in kama da masoyinta.  Tashi tayi taje ta rungomota."Oyoyo little sister." Ko da Zarah taga haka sai tayi kokari ta sakin fuska sanan tace."Sister in-law kina lafia."?
"Lafia lau kanwata ta kaina. Ya gajiyar biki kuma ya dawainiya."?  Murmushi Zahra tayi tace."gajiya tabi lafia, ya kuma bakunta? I hope dai babu wata matsala."
Washe baki tayi Fulanin sannan tace."Ahh ba wata matsala wallahi. Kawai dai naji ki shiru ne har an kwana 2. Da dai har nayi fushi, amma yanzu tunda gaki na huce."
Kama kunne Zahra tayi sannan tace."Tuba nake Sisi." Dariya dukan su sauka saka sannan daga bisani saka cigaba da hirarsu kaman dama sun san juna. Anan kowa take shedawa 'yar uwarta kasar da tayi karatu. Ta dan jima a nan wajen Fulanin kafin daga bisani ta tashi tayi mata sallama sannan ta nufi wajen Umminta.
A wajen Ummin tata ta sanu Meeno ta tasa Ummin a gaba tana kuka wai ita a kira mata Gimbiya Hansa'u ta Zabbit wai ya akai ta tafi basu sake haduwa. Hakuri Ummin ta bata sannna tace."bani da number ta ne Meenal da na kirata ko a waya ne. Kuma kinga bikin nan shine haduwa ta da ita a farko ba wani sabawa mukai da ita ba." Shiru Meeno tayi kafin daga bisani ta tuna da Katin da Gimbiyar ta bata sanda zata baro Zabbit din ita da Chiroma.
Ita kuma Zahra shigowarta kenan taga wanann yarinyar tana kuka Ummi na bata hakuri bata san akan mene ba. tana shirin tambayar Ummin wace wannan ne taji Meeno tace."Ai ina da katin da ta bani na numbobinta sanda zan baro Zabbit din. Bari ba dauko yana kayana ma."
Jin an ambaci Zabbit ne yasa Zahra juyowa da sauri domin ita kam Allah ya jarrabce ta da son Yarima n Zabbit din. A kasa daya suke karatu dashi sai dai shi bai ma san tana yi ba. Domin shi mutum ne da ya tsani yaga bil Adama yana gurman kai. Ita ko Zahran dibi'arta ce shi yasa baya shiri da ita.
Bayan Meeno ta kawo katin ne aka kira Gimbiya Hansa'u a waya. Sallama Meeno ta rangada tare da cewa."ur highness kin gane ni."? Shiru Gimbiyar tayi sanna tace."kamar naso na dauki muryar. Wace dan Allah." Bata rai Meenon tayi sannan ta turo baki kamar tana ganinta tace."Nasan dama mantawa zakiyi dani bayan da kince min kamar 'yar da kika haifa kike kallona. Ta ya Uwa zata mance muryar 'yar ta." Ko ba a gaya mata ba tasan wacece yanzu.
Dariya tayi mai sauti sannna ta jinjina kai tace."Ohhhh ni Allah. Allah ka nunan rananr da yarinyar nan zata koyi sakawa bakinta linzami, kada taje ta janyo kanta na jaki. Meenal ba wai ban gane muryar bane, kwanta min muryar tayi kuma kinsan abinka da jikin tsufa."
Dariya Meenon ta saka sannan suka cigaba da hirarsu ta yaushe gamo. Ita ko Zahra sake sake take tayi a ranta. Ita dai tasan a Zabbit Da daya sarkin ya haifa shine muradin ranta. Ita ko wace ce wannan haka da take waya da Gimbiya a sake haka? Lallai zatai kokari ta shiga jikin wannan ko wacece ita tunda har tana da kusanci da Masarautar Zabbit haka.
Suna cikin wayayrne Gimbiya ta tamabayi Meeno wayar ta ce haka? Amsawa Meenon tayi da."ba wayata bace Ramki ya dade ta Her Majesty ce." Anan ne ma Gimbiyar ta bukaci a bata su gaisa sa Gimbiyar. Bayan sun gaisa ne sukai sallama da Meeno akan zata ringa kira suna gaisawa time to time kafin ta zo.
"Wai wacece wannan haka Ummi."? Zahra tayi tambaya tana mai nuna Meeno. Anan gimbiya ta fayyace mata komi sannan ta kara da cewa."Dama ita nake so na bar miki a matasyin mai debe miki aiki tunda ke baki son bayi."
Murna ce ta kama Zahra take ta hau cewa." Kai amma nagode Ummi, kuma kinga ba wai ma bauta zata min ba. Kawai ba sami abokiyar hira na kuma yi kawa a palace din mu." Ita dai Ummi mamaki ne ya kamata. Zahra ce yau take cewa wata wacce tasan ba 'yar sarki vace wai kawarta. Lallai Zahra ta canja. Bata gama mamakin ba Ummin sai da taji tace."Ya sunanki my dear."?
"Meenal." Meeeno ta bata amsa.
"To yanzu zaki tashi muje chambers dina ne ko na barki anan. Kinga fa sai na baki dakin kusa da dakin danake kwana in yaso sai ki koma can ko."? Dariya Meenon tayi tace to Nagode.
Ummin kam mamakinta ne ya ki karewa.  Hama suka tashei suka rankaya zuwa part din Zahra da ke kusa da side din yaya Chiroma.

A kwana a tashi babu wuya a wajen Allah yau gashi satin Namijin Zaki daya da auren sa. Kuma tun daga ranar luncheon din nan Fulani bata sake saka shi a idon ta ba. Abun ma ya wuce tunani. Ta sanar da mahaifiyar ta inda ita ma abin duniya ya tarar mata sannan ta bata wata shawara wacce nima banji me suka ce ba. Na di ji shewar da Fulani tayi tana cewa."I'm so grateful Mummy. Gaskia ke din ta da bance. Allah ya bar min ke Mmummyna." Sanan  sukai sallama tare da katse wayar.

Da safe yau Zahra ta tashi ta shirya. Wajen karfe 10 ta leko dakin Meeni sannan tace."Zaki rakani side din yaya Chiroma sannan idan mun fito muje side din yaya Lion." 
"To." Meenon ta amsa dashi sannan ita ma ta soma shiryawa.
Bayan sunje sun gaida Aunty Suwaida ne take tsokanar Meeno."Wata Meenak Zahra dai tazo ta kwace min ke, babu komi zata tafi ta barmu dake, lokacin sai ki dawo min ko."?
Kwabe fuska tayi Meeno tayi kalar tausayi ta fara magana."Allah Aunty Suwaida ba haka ne ba, kinga de Ummi ce ta hada mu da my princess, idan so samu ne ai nafi son kullum nazo musha shafta." Dariya Zahra tayi sanann tace"wato Meenal so kike kice ni na hanaki zuwa wajen sister In-law ko."? Daruya duk suka sa.
A hanya sukai karo da Chiroma suka gaishe shi, shima ya tsokani Meeno sannan suka wuce don zuwa shashen Zaki.
Sunje sun tarar da ita taci kuka ta gide Allah. Tana ganin su ta sake fashewa da kuka wai ita gida take missing. Hakuri Zahra ta shiga bata. Da kyar ta samu tayi shiru sannan ta tambayeta ina yaya Usman?
"Yanzun nan ya fita na dauka ma kun hadu dashi a hanya." Inji Fulani.
Dariya Zahra ta saka sannan tace."ko ma dai wannan kukan na missing din yayan ne ba na kewar gida ba." Duka Fulanin ta kaiwa Zahra da pillow sannan suka cigaba da hira. Duk hirar da suke kala Meeno bata ce ba.
Juyawa Fulani tayi ta kalleta a wulakance sannan tace."wacece wannan kike yawo da ita haka? Hala kurma ce ana ta magana ta wani yi shiru." Kallonta Fulani tayi sannan tace." Meenal kenan. Kuma kinga ma 'yar garinku ce." Sake kallonta Fulani tayi tace."'yar wace a Maleeta."?
"'Yar ba kowa." Inji Meeno.
"Au kina 'yar talakawa nake zaune kan kujera ke ma kike zaune? Ko kin mance wacece ni?? I am ur princess, 'yar sarkim garinku sanann kuma matar yariman garin da kike zaune. Sauka ki zauna a kasa my friend."
Baki a sake Meeno take kallonta. Lallai yau sai ta koya wa wannan nunar ranar hankali.
Sauka kasa kan carpet tayi ta zauna kamar yadda Fulanin ta bukata. Tsawa fulani ta sake buga mata sanna mn tace." Uban wa ya baki izinin hawar min carpet?? Waishin wacece ke haka? Me kike ji dashi? Zahra me kike yawo da wannan abar take miki? Uban me ma kike yi anan."?
"Ubanki nake yi. Jahila wacce bata san darajar dan Adam ba." Meeno ce ta bata wannan amsar. Ba Fulani ba dai dai da Zahra sai da ta girgiza dawannan batan batamaa da Meeno tayi.
Tsaki Meenon taja sannan ta tashi, direct sashin Chiroma ta wuce. Itama Zahra tashi tayi tabi bayan ta. Domin bazata bari akan wata fulani ba plan dinta ya rushe akan Meeno. Taci alwashin sanadin Meeno sai ta samu muradin ranta.

_ku biyo ni dan jin yadda zata kaya tsakanin Fulani da Meeno_
_Taku har kullum_
*Pheener*

Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now