Part 5

1.6K 96 8
                                    

Yau ya kama kwanan su Baana 2 a gidan baffah, yau din ne kuma Baana take shirin komawa gidanta. A zaune ta tarar da Meeno tana karatun wani english novel, ta zauna kusa da ita ta dafa kafadunta tace yake yata, kiyi sani cewa inada haqquna akanki da Allah ya dora maki kaman yadda nima kike da naki hakkunan. Yin biyayya yana daya daga cikin haqqin mahaifiya akan dansa. Saboda haka nake miki Umurni idan har kinsan Allah ne ya wajabta maki yin biyayya a gareni to ki gaggawar gaya min inda kike zuwa da kuma yadda ake kake zuwa, ki kuma yimun alkawarin baza ki kuma tafia ba.... Ta karashe zancen tana me goge kwalla daga idonta. Ko da Meeno taji haka take hankalinta ya dugunzuma, ta mike tsaye jikinta sai mazari yake gumi ya lullubeta kai baka ce akwai na'urar sanyaya daki ba a dakin, tace ki sani ya mahaifiyata, babu abinda bazan iya yi ba dan naga na faranta maki, bani da ikon da ya wuce naga walwalarki, yin biyayya a gareki farillata ne. Dole yanzu nan zan gaya miki duk wani abinda yake faruwa. Amma ina so ki fara saka wa a ranki cewa nothing in this world last forever. Kaman yadda kike bakin ciki da bacin rai akaina a wannan rana ki sani wata rana zan zame miki alfahari, zan zamto sanyin idaniyarki. Banso kikai involving kowa cikin minor case irin haka ba. I just don't know what u were thinking da kika fadi ma Yagwalgwal Bilki labarin nan. Na dauka kinfi kowa sanin halayyar mutanenmu nan, bata ida fadin abinda take shirin fadi ba Baana ta kwasheta da wasu zafafan mari guda 3
Tace me na tambayeki? Kim fada min abinda nake neman sani ko sai na kwashe maki albarkatun kanki baki daya?? Anan Ameenatu ta bude baki ta fara magana kaman haka:
Bazan taba iya tuna ranar da na fara ganin su ba, ya kasance kusan kullum sai na gansu muddun na kwanta bacci. Suna zuwa ne zuga guda. Ban san me yasa ba, ko kadan ban taba firgita da ganinsu ba. Saboda zan iya cewa tun tasowata nake ganinsu. Wannan yana nuni da na saba ganinsu kenan tun yarintar da bazan iya tunawa b..  Kafin ta kare sentence in taji wani duhu ya lullube mata kai. A take ta dena fahimtar komi. Duk wasu ma'aikatu da suke aiki a jikin ta suka tsaya cak. Ita dai Baana ta kasa kunne tana jin labari taji shiru. Juyawar da tai ta riski Meeno ta yi poster ko idon ta baya motsawa. Da fari ta dauka pretence ne amma sai ta lura da idon nata a kakkafe suke. Babu shiri ta kurma uban ihu mutanen gida suka yo kansu ana sallalami.
Wannan kenan.

A can kuwa birnin Pasweek, tun barin Ciroma gida Yarima Usman Namijin zaki 🦁 bai samu nutsuwa. Shifa gani yake kawai an shiga haqqinsa?? Ta ya za a Che shi ya zauna a gida a aika Ciroma?? Bayan wannan aikin nasa ne. Ciroman da ko rabin rabin sa ba kai ba a jarumta? Haka kawai shi an kakaba masa wata sarauta. Gaskia shima sai ya nemo waje zuwa. Ina!!!
Yana cikin wannan hali daya aciki.masu tsaron kofansa yake nemawa Mahaifiyarsu iznin shigowa. Ba musu ya gyara yanayin zamansa yake tsammanin shigowarta. Ko da shigowarta sai Usman ya miqe domin girmamata. Bayan ta zauna ne ya nemi waje a qasa daga gefen qafanta ya zauna tare da doro kanshi akan cinyarta. Tayi murmushi ta fara shafa kansa domin ta gane ko mene. Tun yana yaro indai yana da damuwa sign in da yaje mata kenan ta gane. Bai taba ce mata yana damuwa ba sai dai tayi figuring out da wannan sign in. Ta jima tana shafa kanshi kafin daga bisani ta fara magana
USMANU, Shin ko zan iya sanin mene matsalar?? Bai ko dago kanshi ba ya amsa kaman wannda aka tilasta da cewa wallahi Ummu nikam ba a kyauta min a fadan nan. Dariya ce ta kufce mata amma haka ta daure tace wa ya isa ya bata ran Namijin zaki 🦁? Ka manta ko kai waye?? Zaki kake fa, ko a dawa kai sarki ne. Ya dan murmusa jin irin kirarin da yake so daga bakin mahaifiyarsa yace Ummu, wallahi Abbi ne. A nan daria ta kufcewa Ummu. Sai da tayi mai isarta sannan tace ashe Uban Zakin🦁 ne ya kuskuro Zakin🦁. Shima sai da abin ya dan bashi daria amma ya kanne yace yanzu fisabilillahi kyautawa kenan? Ummu ki duba fa dan Allah. Ta kara fashewa da dariya sannan tace banda abin Usman ina ni ina shiga tsakaninku? Anjima fa tare zan ganku. Ko qala bai sake cewa ba dan gogan naga alama ba qaramin miskili bane. Anan ma ya samu kira daga wajen mai martaba ya tashi suka kama hanya.
Wannan kenan.

BIRNIN ZABBIT

A can kuwa birnin Zabbit, sako ya dade da isowa sarki Uwais daga bangaren Ciroman Pasweek. Saboda shi Ciroma Khaleel yadda Allah ya halicceshi baya son rikici. So a hanya ne ya aiki wani amintaccen bawansa kan yayi sauri ya rigasu karasawa birnin yaje wajen sarki Uwaisu yayi musu iso. Ko da Sarki yaji su waye tafe sai hankalinsa yayi kololuwar tashi. Saboda dakarun Pasweek tauraruwa ne mai wutsiya. Ganinsu ba alheri bane. Amma la'akari da yayi da wannan da Yazo yayi musu iso sai ya dan samu nutsuwa. Ya shirya musu tarba mai kyau. Ko da su Ciroma da tawagarsa suka iso sunyi mamakin kalar tarbar da suka samu. Ga masauki mai kyau ga tarba mai kyau. Anan Ciroma ya sake gasgata lallai sarki Uwaisu yafi mahaifinsa sarki Rasheed gaskia a wannan sabgar.
Bayan gabatar da kai ne kuma Ciroma ya fara bayanin zuwansu. Sarki Uwais ya murmusa yace daman nasan ruwa bazai tsamin banza ba. Yanzu mene abinda mai martaba yace ayi?? Ciroma ya kada baki ya fadi abinda mai martabar yake so. Sarki Uwais yayi murmushi yace ya Ilahil alameena yanzu dan mutum ya fika karfin iko sai ya dinga zaluntarka kayi shiru? Naji ma yanzu ba ta baya nake ba, yanzu fisabilillahi shi Sarki Rasheed zai yadda da haka a tasa kasar?? Wannan maganar ma aka je masa da makamanciyarsa basai ya yaqi ko waye ba? Amma ba komi, ni bazan so a yake ni ba. Dan ko ba komi ina daraja mutanen dake karkashin mulki na. Kamar yadda ya turoka to ka tsaya har na watannin da ya umurceka ka yi abinda ya turoka. Amma ka sani bazan taba yafe masa ba ranar gobe kiyama. Al'umata ma baza su yafe ba.
Ko da sarki Uwais yazo nan a zancensa sai duk kunya ta kama Ciroma. Yayi dana sanin zuwansa. Sam shi baisan haka abin yake ba da bai zo ba.
Kai amma san zuciya bacinta. Ya raya a ransa.

To can kuwa gidan Baffa bayan an yiwa Meeno taimakon gaggawa ne ake neman ba'asin me yake faruwa ne? Anan Baana ta sheda musu yadda tasan anyi. Ai nan Baffa ya tashi fada ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Ya qarewa Baan tanadi tass. Daga bisani kuma yace ya yanke shawarar barin Ameeno birnin. Zata bi qanwar ubanta ne inda take aure anan zata fi samun ingantacciyar tarbiyya.

To fah🤔🤔🤔 ko ina nan inda za akai Meeno?? Ko su waye wadanan mutane da Meeno ta fara labari??
Ku biyo dan sanin wannan.
Follow on Wattpad @mss-pheener

Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now