part 50 to 55

466 38 0
                                    

🌎 '''MANAZARTA WRITERS ASSOCATION''' 📚🖊️
         *M.W.A*

*Kungiya d'aya tamkar da dubu, Masu Nazari da aiki da ilimi, burin 'kungiyar a ko yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.*🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________
*Note_* bamu yarda wani ko wata su juya mana labari ba tare da izinin mu ba

*Page 50 to 55*

Kwanan su 2 kenan daga su sai halinsu. Su kansu masu garkuwa da mutanen har sun fara gajiyawa da su.. dan haka yau suka ya ke shawarar sai dasu a matsayin bayi..

Babban cikinsu ne ya bawa wani yaronsa umarnin ya kwashe su yaje ya zuba su a ciki wata Truck, hakan kuwa akai sannna aka lullubesu da harawa bayan anyi musu allurar bacci. Ko motsi babu wanda yake yi a cikinsu. Haka aka kwashesu a bayan truck din nan har zuwa bakin teku..
Anan akayi cinikinsu sannna aka dura su a wani tampatsetsen jirgin ruwa aka soma tafiya dasu babu dare babu rana. Yau satinsu guda a cikin ruwa suna tafia kuma bbau lefi ana basu abinci saboda ma a saye su da daraja. Tun suna tsoro har suka fara sabawa da rayuwar jirgin ruwa.. 
Sai da suka kwana 13 sannan suka isa wata babbar fada da ke can kusa da kasar sin.. anan aka sake saida su kuma akayi sa'a mutum daya ne ya saye su.

"Ba wai bautar da zamuyi nake ji mana tsoro ba Zainab, zama a cikin mutane da ba al'adar mu daya ba, ba ma kalar fatarmu daya da su ba. Basu jin turanci ballatana hausa. Nikam ban san wacce irin kaddara ce tasa na baro Pasweek ba." Meeno ce take maganar nan ta kareshe zance da kuka mai tsanani.
Saukar bulalar da taji a bayanta ne yasa ta dagawa da sauri. Mutumin da ya saye su ne, a nufinsa su dago kafa suna bata masa lokaci.
"Ina jin ga fa nufinsa muyi sauri dan kinsan haka ake wa dabbobin da ake hawa idan ana so suyi sauri." Zainab ta fada cikin karyewa da sarewa.

Kafar suka daga suka fara tafiya kamar zasu tashi sama. Ba ma ya Meeno da bata iya sauri ba ko kadan.

An kaisu wani gida da yafi kama da kurkuku wai anan zasu zauna har sai sun iya yaren su.  Akwai wani tsoho da shi yana jin yare sama da guda 5000, shi ma bawa ne a masarautar kuma yana da baiwa. Shi yasa aka aje shi anan don ya dinga koyawa bayi idan an kamo konam sayo yaren su da yafi shige da Chinese..

Sunyi sa' a har hausa yana ji, don haka basu sha wahalar yin magana da shi ba. Dan dattijon da zai kai kimanin shekaru 76 ne ya shiga koya musu yaren babu kakkautawa..

Sai muce Allah ya bude wa su Meeno kwakwalwa a iya yaren da wuri.😫😫


A can Pasweek kuwa, anyiwa Suwaida aiki lafia an ciro mata 'yar ta kykykyawar gaske me kamata da Kanin Ubanta Usman, amma tayo farin Suwaida. Dan haka sai kyan nata ya zama abin kwatance.. Amma yanayin yadda jikin Suwaida ya saki ne ya bawa Chiroma tsoro. Idan ka ganta a haka lafia lau take tsaff zaka ganta, amma idan ka kura mata ido zaka gane me nake son cewa.
Murmushin karfin hali tayi sannan ta kamo hannunsa ta rike..
"Sannu ya jikin Wifey? Ina ne yake miki ciwo.", Chiroma ya fada yana dafa jikinta yaji ko akwai zafi. Sanyi kalau din da yaji ya sake firgita shi.
Murmushi tasake yi sannan tace. "Ko ina ba ya yi min ciwo Hubby.. ai naji sauki."
Ajiyar zuciya yayi sannan yace. "Allah ya baki lafia my wife.. Nagode da wanann santaleliyar yarinyar da kika haifo min. Ki gaya min yanzu me kike so na yi miki shi my darling wife."

Sake kankame hannunsa tayi sannan tace. "Komi bana so mijina alkawari daya nake so ka min."
Kanta ya shafa sannan yace. "Yau ranarki ce matata gaya min mene ne na miki alkawarin yi miki shi matukar bai fi karfi na ba ba kuma sabon Allah bane."
"Good." Ta fada sannan ta dora da cewa. "Ina ji a jikina Meenal tana nan a raye Hubby, so nake ka nemo min ita duk inda ta shiga a gadin duniya. Sannan ka min alkawarin auren ta bayan na tafi daga gare ka."
Hannu yasa ya toshe bakinta saboda kunnuwansa bazasu jure jin wadan nan kalaman nata ba.
"Ina zakije Matata?? Babu inda zakiyi muna nan tare har abada." Ya fada yana kokarin share hawayen da yake zirya a idonsa.

"Kayya! Nima zanso haka abin alfahari na, amma kasani Allah bai halicce mu dan mu zauna a duniya ba, dole ne mu amsa kiran nature, dolemu mutu dan haka ni ina ji a jikina lokaci na ya kusa. Alkawarin da ka min nake so ka cika min *KHALEEL*"

Gaba daya rudewa yayi dan tunda yake Suwaida bata taba kiran sunan sa haka ba. Sai yaji wani iri. "Ka min alkawari Baban Suwaida." Ta sake fada tana kankame hannunsa.
"Na miki alkawari indai hakan zai kwantar da hankalin ki." Ya fada yana goge zufar da take keto masa ko ta ina.
Salati ta dauka, tun yana tunanin abin na kare ne har sai da ya fita da gudu ya kirawao likita. Wannan shine maganar Suwaida na karshe. Tun daga nan harshen ta ya karye..

Kowa yazo ya ganta yasan lokaci kawai take jira. Da yake Allaha mai yadda ya so ne a haka ta rayu har akai kwana 7.

Ko da Mia martaba ya nemi wani suna za a rada mata shiru Chiroma yayi yana tunanin.
"Kayi min alkawari baban Suwaida." 
Maganar da ta dawo masa kwanyarsa kenan. Suwaida take so na saka mata kenan..

Gyaran murya yayi sanann ya dubi mai Martaba yace. "Sunan mahaifiyar ta za a saka mata, ita din ce ta nemi haka."
Da Suwaida aka yiwa yarinya huduba sai muce Allah ya raya mana Suwaida 'yar gidan Suwaida.

Kwanan Suwaida yau 9 a cikin Comma, bata san wa yake kanta ba ba ta kuma san me take ba. Numfashi ma sai da inji Oxygen take yi.. kamar kullum yauma yazo yana mata hira kamar wani zautacce, domin Allah ya sani yana son matarsa mai hankali. Ba auren soyayya sukai ba aure ne na hadi, hasali ma bai taba ganinta ba sai da aka zaba masa ita. Amma bayan sunyi aure yau kimanin shekaru 4 kenan gaba daya halayyarta yasa ta shiga ransa. Gashi uwa uba ta bashi farincikin sa ta haifa masa 'ya.

Ya a zaune yana gaya mata wai Baby Suwaida ta kara nauyi akan sanda aka haifo ta. Labarai dai kala kala. Gani yayi kamar idonta yana motsi.. likita ya fita ya kira a guje.. bayan isowar likitan ne ya tabbatar masa labarin da ya kusa yayi sanadiyar kurmancewarsa. Wai Suwaida ta rasu.

*Innalillahi wa inna ilahi raji'un.*

Wannan bakar rana da yawa take, wannan rana mai yanke kauna da soyayya, mai raba da mahaifi, mai shiga tsakanin masoya..

(Allah ina rokonka da sunayen tsarkaka kasa mu cika da imani, kasa mu mutu kana mai yarda damu, kasa mu koma gareka kana mai aminta damu.)

Tsayawa bayyana muku irin tashin hankalin da kowa na masarautar ya shiga ma bacin lokaci ne.  Haka aka tattara Suwaida aka kaita makwancinta gidan na gaskiya..

Yau akai sadakar arba'in din suwaida, amma har yanzu sabuwa dall Chiroma yaje jin radadi da Zogin mutuwar. Gaba daya in ka gashi ya chanja. Wannan walwalar duka babu.. Sai muce Allah ya bashi dangana Amin.

To ita ko Meeno har sun zama 'yan gari domin yanzu sun kware a yaren wadan nan mutane, idan kaji sunyi hausa to tana tare da Zainab ne.. gaba daya sun rungumi kaddara sun fara sakin jikinsu.. suna shan wahala da aikin bauta har sun fara sabawa. Matsala daya suke samu a bangaren Sallah. Domin asuba azahar kawai suke samun yinta s kan kari. Asuba idan sun tashi zasu tafi wajen aiki. Azahar kuma an basu break zasu ci abinci. Amma sauran la'asar, Maghreb, da Isha duk sai sunzo kwanciyar bacci suke..

*Pheener(Mrs Naseer)*


Namijin Zaki 🦁 Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora