part 33

464 52 9
                                    

🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁
    *NAMIJIN ZAKI*
🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁

   By
_Nafisa Aliyu_
    *(mrs Naseer)*

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*📚🖊️

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.
'''🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
______________________________________

Page 32

Jikinta ne yayi sanyi jin maganganunsa.. idan akwai abinda ta tsani tunowa bai wuce ranar da Turaki yayi mata wannan abin ba.. domin ita kamta ta dauka ya lalata ta.. Hawaye ne ya shiga rige rigen fitowa daga cikin idanunta.. tana kokarin gogewa wasu sababbi na sake zubowa. Gaba daya sai taji ta tsani kanta. Tunda abin nan ya faru ta yanke qauna da rayuwa. Nasihohin da Ummi tayi mata ne suka shiga bujiro mata.
"Ki sani Meenal wannan ba shi ne karshen rayuwar ki ba, ba kuma shine zai zama dalilin rushewar rayuwarki ba.. ki dauki hakan a matsayin qaddara wacce Allah ya rubuta ta tun kafin ya halicce mu baki daya. Ki sani idan kika yi imani da Qaddararki kika rike ta hannun bibbiyu lallai Allah zai musanyi miki da alheri da biki taba tunani ba.. duk wanda Allab ya jarrabce shi yayi hakuri ya cinye Allah yace ayi masa albishir. Akwai Rahma daga gareshi da yayi masa tanadi. Ki sani Meenal, Allah yana tare da maj hakuri. Bare ke da aka zalinta aka cuta.. to Allah bazai wofintar da ke ba.."
Numfashi ta sauke sannan ta tuno sanda Ummi tasa tayi mata alkawari bazata sake ko tuno wannan abin ba a zuciyar ta bare ta bari yayi tasiri a ranta. Hawayenta ta sake gogewa sannan ta fada a fili."bazan zama me karya alqawarin da nayi miki ba Ummi.. Allah ma yasan nayi iya kokari na na kawar da wannan tunanin daga zuciyata. Yau gashi dan ki shine ya tuno min da shi Ummi. Allah ma yana gani.. wai har qaddara ta ta zama abin gori a gareni."
Jin kansa yayi yayi masa nauyi. Sake dafe shi yayi. Ta yaya zan mata bayani ta gane ba gori nayi mata.. ina so na kare mata mutumcin ta ne. "Ya Ilahee!."
Ya sake furtawa a fili sannan ya dora da fadin."Ban damu da yadda kika fassara maganata ba. Abinda nasan na damu shine, in kare miki mutumcin ki kada na sake bari wani abu ya sameki."
Ya juye ya shige bedroom din ya barta nan tsaye.
Ta kai kamar minti 10 a tsaye kafin ta juya ta fita daga dakin. Masaukinsu ta nufa. God so kind sanda ta shiga Zahra sallah take. Dan haka direct bathroom ta nufa. Wanka tayi sannan ta fitobdaure da bathrobe a jikinta. Ranta duk a dagule haka ta karasa wannan daren. Zahra taso tambayar ta amma ganin yanayin ta yasa ta tsuke bakinta.

To shi kuwa Usman tunda ya shiga dakin yake kaiwa iska naushi haka ya karaci fushin sa har zuwa wayewar gari.
Yau Chiroma zai iso birnin na Zabbit. Dan haka ana ta shirye shiryen tarbar sa domin an san yau ne ranar dawowar sa. Yadda ya zama kamar dan gida a gidan sarki Uwais ne yasa ake ta hada hadar saukar Yariman.

Shi kuwa gogan bai ma san me ake ba domin har yanzu kunchi yake ko waje bai leko ba.
Chiroma da yayi asubancin tawowa sai gashi daf da la'asar ya karaso. Bayan zuwan sa ne ya ci ya sha sannan ya kama hanyar guest house din da ya saba sauka. A hanya ne wani bafade yake gaya masa ai Usman yana nan. Da farko gabansa ne ya fadi dan ya dauka da wani mugun nufin Usman yazo amma jin dayayi ya kwana 2 yasa ya dan ji relief amma Allah Allah yake yaje yaji dalilin zuwan Usman din..

Yana isa ya karisa dakin da ya saba sauka. Sai da yayi wanka ya fito sanann ya nemi a nuna masa dakin da Usman din yake. Babu musu aka nuna masa ya kama handle din ya murda ba tare da yayi knocking ba.
A yadda Usman yake a hasale yayi niyyar ko waye yayi wannan gangancin shigowa ba tare da knocking ba sai ya fuskanci hukunci mai tsanani.. dagowar da yayi daga zaunen da yake ya kifa fuskarsa akan gado da niyyar ruwan bala'i. Ganin Chiroma ne yasa ta hadiye masifarsa babu korawa da ruwa.

"Ya Chiroma saukar yaushe kuma."?
Usman din ya fada kamar ransa zai fito ta bakinsa saboda hadiye fadansa da yayi.
"Yanzu." Chiroman ya takaita maganar tare da zama a gefen gadon..
Gyara zaman sa Usman din yayi sannan suka gaisa da Chiroman..
"Me ya kawo ka nan."?? Chiroman ya tambaya babu alamun wasa.
Shiru Usman babu alamun zai amsa masa.
"Nace mene ya kawo ka nan babu iznin ko mai martaba." Chiroman ya sake tambaya wannan karon ransa ya fara baci.
Shima Usman din da ransa ya kai kololuwar baci saboda tsawar da Chiroma ya daka masa amsa shi yayi a hasale.
"Ba dole Sai da Iznin mai martaba zanyi komi ba. Inada 'yancin zuwa duk inda nake so a duniyar nan tunda Allah ya hore min isashshen lafia." Ya fada yana mikewa zai bar dakin din idan ya cigaba da magana zai iya gayawa yayan nasa magana mara dadi kuma bazai so haka domin yana bashi girmansa matuka.

Ganin hakan yasa Chiroman shima ya mike tare da kamo Usman din ya rime kafadarsa."Kayi Hakuri ba wai dan ranka ya baci nayi maka wannan maganar ba. Kayi sauri ka koma gida akwai yakin da za ai very soon.. nd me Pasweek zata iya aikatawa ba tare da sarkin yaki Namijin Zaki ba." Ya karshe zancen cike da zolaya.
Shima Usman din sai yaji duk ya sauko domin dama bazai iya fushi mai yawa da yayan nasa ba.
"Allah da gaske yaya Chiroma akwai yaki."? Usman ya tambaya yana washe hakora.
"Chiroma bai taba karya wa dan kaninsa ba." Shima Chiroma ya amsa yana dariya.
Da haka duk bacin rai ya gushe a zukatansu Usman ya daura aniyar komawa gida gibe Idan Allah ya kaimu...

To ita ko Meeno da taimakon Mami gaba daya damuwarta ta tafi.. ita Mamin ta dauka damuwar baikon da Meeno tace anyi mata ne dan haka ta dinga kwantar mata da hankali. 
"Kimin alkawari daya ur majesty." Cewar Meeno
"Na mene fa Meenal."?? Inji Gimbiya Hansa'u.
Murmushi Meeno tayi sannan tace."Dan Allah so nake ki hada yaa Safwan da Yaa Zahra."
Shiru Gimbiyar tayi sannan tace."zan tuntube shi naji. kinsan dole sai yana da ra'ayi. Amma nima da naso hakan tunda Zahra tana da hanakali."

Murna Meeno tayi sannan ta tashi ta koma masaukin su.

*Washegari*
Usman yaje sallamawa Gimbiya kuma ya bukaci tafiya da su Meeno. Haka suka tsiri tafiya katsahan ba dan sun so ba.. itama Gimbiya bata so ba.. har sun fito zasu shiga motoci Meeno tayi tsaraf tace."Yaa Zahra bari naje nayi sallama da ya Chiroma."
Bata jira amsar kowa ba ta wuce guest house.
Sunyi sallamar sanann ya rakota har Mota. Kunya ce ta kama Zahra ta hau sunkuyar da kai domin ita da take 'yar uwarsa bata je sallama dashi ba.
Sarai Chiroma ya gane kunyar me ta ke dan haka sai ya basar da zancen. Ran Usman ne yayi mugun baci ganin yadda suke ta shewa da Chiroma da Usman da Safwan da yanzu yazo Mami ta sanar masa da tafiyarsu.. gaba daya ya tsani yarinyar nan mai son mazan tsiya. Sai washe wa maza hakora take yi. Sam bata da kamun kai, kalli dai zahra ita da take uwa daya uba daya da Chiroma amma bata shishshige masa sai wannan banzar mara kamun kai. Gaba daya ya tsaneta wallahi.. (ni kuwa nace anya tsana ce wannan Usman?)

Ku biyo ni dan jin yadda zata kaya.
*Pheener (Mrs Naseer)*
*08060154424*


Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now