part 26

353 40 0
                                    

🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁
    *NAMIJIN ZAKI*
🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁

   By
_Nafisa Aliyu_
    *(mrs Naseer)*

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*📚🖊️

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.
'''🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
______________________________________
*Wanan page din sadaukarwa ne ga Maman Tasleem (Namijin Zaki fans group) Nagode da irin Kauna da Addu'o'inki. Da duk sauran 'yan Namijin zaki fans group. #OneLove*💖

Page 25
Gaba daya ma kansa ya kulle ya rasa ya zaiyi, ga 'yar mutane cikin wani mugun hali. Bathroom din dakin ya nufa, ya shiga ya hada ruwa mai zafi sannan ya dawo ya dauke ta cak ya nufi bathroom din da ita.  Bayan ya gasa mata jiki ne ya sake dauko ta ya fito da ita daga dakin. Direct Bedroom dinsa ya nufa da ita. Warm milk ya bata babu musu ta amsa ta sha sannan ya tambayeta ko akwai inda yake mata ciwo. Amsawa tayi da."Eh, duk jiki na ma ciwo yake." Pain reliever ya bata sannan ya mata sannu. Ya kuma umarce ta da ta kwanta tayi bacci zai je ya dawo.

Bayan ya fito daga dakinsa ne ya bada umarnin a kira masa chief guard. Ko da shugaban Guards din yazo sai ya bashi umarnin ya biyo shi. Ba musu ya bi bayan shi suka nufi BQ. Da suka shiga dakin da Turaki yake bai farfado ba. Ruwa ya samu ya sheka masa ya farfado a gigece. Juyawa yayi ya kalli guard din nan yace."Jail him. And bana son kowa yasan ka rufe shi. Ka kaishi kurkukun dake can bayan gari kada kowa yasan yana can har sai na bada iznin.
Ba musu guards sukai kamar yadda Namijin zaki ya fada. Bai koma inda ake bikin ba, dakinsa ya sake nufa. Yana zuwa ya tadda ta tayi bacci.

Wani mugun tausayin ta yaji ya dira a zuciyarsa. Lallai Turaki ya isa a kira shi Animal, jahili, dakiki kuma mara imani. Rape! Rape!! A masarautar sa? Kuma ma shine sanadin da hakan ta faru. Da bai bawa Turaki dama ba da bai yi ba. Ashe ba Turaki kadai ke da laifi ba. Ya zama dole ya kyautatawa yarinyar nan tunda shine sanadin bacin rayuwarta.
Yanajin zai gayawa Ummin sa. Gaskia ya kamata ya gaya mata. He can't handle this alone. Da wannan tunanin ya juya ya nufi hall dun biki.  Yana zuwa ya tarar ana ta shagali, ajiyar zuciya Fulani ta saki domin ta dauka da bazai dawo ba. Wajen da su Ummin suke ya nufa. Gabanta yaje ya durkusa sannan ya rada mata."There is a huge problem out there, ki temakeni ki bar bikin nan kizo muje asan ya za ayi."
Yadda ta ga muguwar duwa a tattare dashi ne ya sa ta tashi da sauri tare da kama hannunsa sukai waje.
"Me ya faru Usman mene ne? Tell me what's bothering u pls..." Ta karashr maganar da matsanancin damuwa a fuskanta.
"Relax Ummi pls, idan kika ce a haka zaki cigaba da tashin hankalinki bazamu sami mafita ba pls." Shima yayi maganar da damuwa a fuskanshi. Sannan ya kara da cewa "Muje kiga mene."
Wucewa yayi ta bi bayansa. Bayan sun shiga part nashi ne taga Meeno kwance kan gadonshi sanye da bathrobe dinsa. Tsoro abin ya bata. Bakinta na rawa ta ce."What's wrong with her? Na shiga uku."
"She's been raped. Zuwa nayi na tarar ana mata fyade." Ya fada jiki a sanyaye.
"Wanne Bastard, shameless, disgusting Human ne yayi mata wannan danyen aikin?? Wane wannan dan akuyar gaya min yanzu ko wane Usman." Gimbiyar ta fada da mugun bacin rai.
"Turakin Maleeta. Yayan matar dana aura." Ya gaya mata yana kau da kai.
Salati Gimbiyar ta saki tana tafe hannaye.
"Ummi kuma nine silan yi mata fyaden." Usman ya fada yana mai nadamar abin.
Mari ta dauke shi dashi. Sanann tace."yi min bayani, gaya min ta yadda akai ka zama dalilin yi mata fyade."
Anan Usman ya kwashe komi ya bata labari. Taga laifin dan nata sannan ta gwada masa kuskuren sa. Shima kuma ya nuna mata yayi nadama. Shiru tayi sanna tace dauko ta muje ka kai min ita chamber dina. Da to ya amsa sannan yayi yadda tace.

A haka akai biki na kwana 3, duk abin nan da akeyi ango sam bashi da wata walwala, burinsa bai wuce yaga Meeno ba ya tambayeta ko akwai wata matsalar. Amma hakan bai samu ba sakamakon taron jama'an biki. 'Yan biki sun fara watsewa an kai amarya dakinta. Yadda aka kaita ita kadai haka ta kwana ita kadai a dakin. Ita ba ma wannan ne ya dame ta ba. Yadda kawayenta zasu zo da safe dan su ga ya ake ciki ne bata san ya zatai dasu ba. Tana jin shewarsu daga parlorn ta ta tashi ta hautsina gadon da take kai sannan ta yamutsa gashin kanta. Ko da suka shigo suka tarar da ita a haka sai suka hau shewa.
Kallonsu tayi ta marairaice wai ita ba abinda yayi mata. Wai yace mata akwai gajiyar biki a tattare dasu dan haka ya daga mata kafa ba yau. Kara sa shewa sukai suna kiran lallai an sha love. Irin wannan tausayi haka.. da haka suka karaci shakiyancin su sannan sukai mata sallama dan yau zasu koma garinsu. Kudi ta bude bed side ta dauko wai gashi yace ta basu sa sayi ruwa a hanya su sha. Godiya sukai suka tafi kowa tana yaba irin sa'ar da Fulani tayi na miji..


Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now