part 12

399 55 0
                                    

🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁
*NAMIJIN ZAKI*
🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁

By
_Nafisa Aliyu_
*(mrs Naseer)*

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*📚🖊️

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.
'''🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
______________________________________

Page 12

Assalamu alaikum
Wannan page sadaukarwa ne ga
Aunty Binta Umar Abbale MWA
Aunty Jamila Jamee MWA
Aunty Erisco MWA
Aunty Beebat MWA
Aunty Milhat MWA
Da duk yan uwa na Manazarta writers association...
Allah ya kara baseera da zaqin hannu Ameen ya kuma bar zumunchi Ameen Thumma.

Gari ya fara haske, rana ta fara fitowa. Shirye shirye ake yi a cikin masarautar ta Maleeta ba kama hannun yaro. Yau din ma kamar jiya ko ina na bangaren Fulani da kuma Gimbiya Haleema ya dau gyara na kece raini. Sashen da Namijin zaki ma yake an gyare shi tasss. Dakin da yake bacci kawai ne ba a shiga ba, shima tsumayin fitowarsa akeyi kafin aje a gyara din.
Kamar yadda ya saba idan yazo Palace din, tare da mai Martaba yake cin abincin ko yaushe haka yau ma ta kasance. Bayan ya kimtsa ya fito sanye yake da Dogon wando blue jeans, sai farar t shirt a samanta kuma ya dora stripe jeans jacket mai blue da baki. Yayi kyau matuka gaya, ya fito a Namijin zakin sa.
Duk inda ya ratsa sai an kwashi gaisuwa shiko kaman ba da shi suke ba, domin ko kallon inda suke baya yi. Saeedu Turaki ne sa'an shi a palace din. Don haka tun jiya da yaji zuwansa yake rawar kafa, amma bai samu ganinshi ba domin ko da yazo baya nan, yaje zai dubashi kuma aka sheda masa yace kada wanda ya dameshi. So yau da safe shine ya dau aniyar zuwa ya tawo dashi dinning domin suyi breakfast.
A hanya sukai kicibis da shi
"Allah ya taimaki Yariman duk duniya." Cewar Turaki. "My prince dafatan ka tashi lafia." Namijin zaki ya fada yana mai mikawa Turaki hannu tare da sakin fuska. Gaisawa saukai sannan Turaki yace."dama zuwan zanyi na tawo da Yarima, duk an hallara a dinning kai kadai ne babu." Murmushi Namijin zaki yayi wamda babu wanda zai fahimci ma yayi. Shi dai Sarki Ameenullahi yana birgeshi. Allah ya hada jininsu tun yana yaro.
A haka suka karasa dinning din domin Saeedu ya fahimci Namijin zaki tass, shi yasa ma suke shiri. Dan shi Turaki ya iya zama da mutane saboda dan duniya ne ga iya siyasa da munafirci. Tunda suka shiga dinning Hall din babu abinda Fulani take idan ba kallonshi ba. Ta kura masa ido kamar mayya, Mummyn ta na lura dan haka ta faki ido ta mintsine ta. Sai a sannan ta dawo daga duniyar tunanin da ta lula.. Murmushi ne subuce mata sanna ta kalli wayart da tai beeping alamar shigowan message. Maaah! Taga an rubuta baro baro. Murmushi ta sake yo sannan ta dauka ta karanta."MAZA KI BARI YA RAINA KI, KIN WANI ZUBA MASA NA MUJIYA KAMAR BAKI TABA GANIN NAMIJI BA."
Dariya tai a ranta tace."ai ban taba ganin Namiji ba Mummy." A fili kuwa basarwa tayi ta ja plate gabanta. Shiko Usman da bai ma san akwai mace mai kama da ita ba ko kallon i.da take baiyi ba. Bayan ya gaisa da mai Martaba da Gimbiyoyi ne ya fara cin abinda yaga zai iya ci a wajen. Ba karamin baci ranta yayi ba. Duk wannan kwalliyar ma bazai kalla ba? Bayan ta gama timing a dinning zata sace zuciyar shi? Idea ce ta zo mata. Tari ta fara yi iya karfin ta alamar ta kware, idan ka ganta zaka rantse da Allah kwarewar tayi.
A gigice kowa na wajen yayo kanta idan ka cire namijin zaki da kuma mahaifiyar ta domin tafi kowa sanin dalilin tarin yar tata. A zuciyarta tace."Gado ba karambani ba, yarinya baki dauka a kasa ba." A fili kuwa gigicewa tayi tana kiran."na shiga uku, me ya sameki Fulani? Me yake faruwa wai."?
Baiyi niyyar ko dagowa ba amma jin yadda Gimbiya Haleema ke exaggerating abin ya sa shi dagowa domin ko ba komi shi din health personnel ne.
Tasowa yayi yazo wajen da take sai wani shishshidewa take tana drama, ya kalleta yace cikin husky voice dinsa."ku sake ta muga." Sakin nata kuwa sukai ya kalleta cikin ido idon nata duk yayi Jaa saboda kakari, yace mata."calm down ok, take a deep breath, relax and stop pressurising ur self." Dagewa ta sake yi ta kara kakai mai karfin tsiya, wannan karon sai da amai ya taho mata. "Kodai asibiti za a je ne Usman." Mai martaba ne yayi wannan maganar. "A'a ranka shi dade." Iya amsar da ya bayar kenan sanna ya sake kallonta. "What if she's not faking it."? Yayi wa kansa wannan tambayar. Hannu yasa ya taba jikinta yaji da dan zafi haka saboda ta wahalar da kanta ba kadan ba. Sumewa ne kawai Fulani batai ba jin hannunsa a wuyanta daf da kirjinta. Ai a take numfashinta ya danyi sama saboda shammatarta yayi kuma tana tsakiyar kakari ne. Sai da yadan razana ganin yadda numfashinta yayi sama. Ya tabbatar lallai tana jin jiki. Don haka yace da Mai martaba da a kamata a kwantar da ita flat a kan katifa, maybe ta dan yi relaxing. Mai Martaba yace da Turaki me kake jira baka kamata ba. Ai da yake Turaki dan duniya ne kuma hatsabibi ashe ya gano mai yar uwar tasa take nufi, tuni ya langwabe wai yayi buguwa a hannunsa bazai iya daga ta ba. Bai yi wata wata ba ya sungumeta domin a tunaninsa ceton rai zaiyi. Hanyar dazai kaita ya bukaci a nuna masa, ba musu Gimbiya Haleema ta wuce gaba, ga tunaninsa sashenta zasuy sai yaga sunyi wani sashen daman. Sashen Fulani ne. Bai raya komi ba yabi bayanta. Sai da ya samu ya ajiyeta sannan ta dan nutsu ta dawo daga duniyar data fada."sannu, howa are u feeling now."? Magana tazo yi sai ta kara sarkewa da tari shhhhhhhh, yayi mata alama ta hanya dora hannunsa akan lebansa. Shirun kuwa tayi kamar gaske tana dan tari kasa kasa. "She need to rest." Ya fada yana mikewa. Godiya Gimbiya tai masa sanna ta rakashi har kofar main entrance. Sai da ta dawo sannan kunya ta lullulbe Fulanin sai kawai tace bari tai lambo kamar gaske ne. Gimbiya ta kalleta tace."sai ki tashi ai ya tafi, Drama Queen." Ta karasa maganar da dariya mai kykyacewa. Tashi tayi zaune, sannan tace."Mummy ashe kin dago yawar."
"Haihuwarki fa nayi Fulani, na raineki komi zaki a nono kika sha ai. Kinsan hausawa sunce nono mazirarin hali." Dariya Fulani ta kyakyace sanna tace ya kikaga wannan performance din." Kai ta gyada yace."nice my princess." a haka suka ci gaba da hirar yadda zasu shawo kan Namijin zakin dan sunga zai basu wahala saboda miskilancin sa.
Shiko gogan bai koma dinning hall din ba, direct wajen wani pool ya nufa, tun yana yaro yana zuwa wajen idan yazo Maleeta. waje ya samu ya zau a gefen pool din ya zira kafarsa daya a ciki yana wasa da ita. Kamar a mafarki yaji motsi a wajen, yasan dai idan yazo tun yana yaro babu wamda yake biyo shi, tashi yayi yana juye juye, domin duk wanda yazo ya bata masa lokaci sai ya hukunta shi ko waye kuwa. Motsin yaji yana karato shi. Chak ya tsaya don ya tabbatar da inda yake jiyo mitsin domin wajen bishiyoyi ne ya kewashi. Sai kawai ganinta yayi ta fito da gudu tana dariya kaman wani ne ya biyo ta suna wasan tsere. "Ita ce."! Ya furta a dan razane, domin if he can remember wannan din ita ce maras kunyar yarinyar nan da Chiroma yace masa ajiyar mai martaba ce. "What the hell is she doing here? Ko dai har da ita aka hado a maids dinsa? Amma ai kamar ba Maid ba." To wace?
"Ke! Ya daka mata tsawa, kunshe dariyarta tayi sanna tace na'am. Shirun da taji ne yasa ta dago. "Shine" ta fada cikin ranta. "What the heck is he doing here? Goodness knows what he'll do to me this time around." Ta fada a ranta. "Zo nan!" Ya bata umarni ba tare da ya kalleta ba. Matsowa tayi sum sum sai da tazo dab da shi ya tsaya. "On ur knees." Ya bata Order. Ba musu ta zube a kasa tana mai marairaice fuska. "Dago ki kalle ni." Ya fada yana murmushin mugunta. Dagowa tayi fes da idonta ta sauke a kan fuskar shi. A tunaninsa bazata iya ba, domin shi maids dinsu basa iya hada ido da su. It's an abomination ba ma maids ba kowa ma na garin ya hada ido da basarake. So yasan it'll be a great punishment yace ta kalleshi dan a tunaninsa bazata iya ba. Kuma idan batayi ba yace ta saba umarninsa. Bit to his greatest surprise sai gashi tana kallonshi ido cikin ido. Bai gama tsinkewa da al'amarin ta ba sai da yaji tace."if u don't have something important to say, u should stop wasting my precious time ok?." Ta juya zata wuce, fizgo ta yayi da dukkan karfin da Allah ya bashi da niyyar ya mammake ta, ya fasa bakin fitsara, ai ko sai jinsa yai yayi loosing balance dashi da ita duk suka antaya cikin swimming pool din. Ita bata ita ruwa ba, so sai ta fara drowning ta fara shan ruwa. Ya dauka shakiyanci ne, sai da yaga da gaske kasa take yi tana facal facal a ruwa sannan ya dauko ta.
Bayan ya fito da ita ne duk kayansa a jike ga nata ma a jike ya rasa ya zaiyi da ita da shi kansa. Domin shi ba ma ta ita yake ba, yanzu ya za ayi yazo gidan mutane kawai a ganshi sharkaf da ruwa haka? Ai sai ya zama abin magana. Ga yar mutane tana rawar dari. Shifa malamin lafia ne, bazai bari wata cutar ta kama ta ba. "'yar banza, ai duk ita ta janyo wa mutane hakan." Ya fada a fili.
Idea ce tazo masa, wani Guard da suka zo tare daga Pasweek ya kira bayan yazo ne yace yaje ya dauko masa kayan shi set guda sai ya hado kuma ya hado masa da short nicker dinsa da T shirt. Ya amsa da go sanann ya je ya kawo masa. Ita ko bayan yayi kokarin fitar da ruwan da ta sha ne aka kawo masa kayan. Chanja mata yayi sannan yacewa Guard din nan yaje ya sa kayan su bushe da wuri kafin 10 mins. Hakan kuwa akai sannan ya dawo masa da kayan nata. A gaskiya a lokacin da yake chanja mata kayan jikinta da farko bai kula da komi ba domin duk shi a rude yake. Sai da yazo zai mayar mata da nata ne hankalinsa ya tashi. Domin a wannan karon ya dan dawo nutsuwarsa. Shiru yayi na wani lokaci sannan yace."to mene ma abin daga hankali akan wannan ficiciyar abar." Ta maza yayi sannan ya fara kici kivinzare T-shirt dinsa daga jikinta. Ita ko jagwalgwalanta da yake bai sa ta farka daga nannauyan baccin wahalar da ya dauke ta ba. Domin tunda ya gama fitar mata da ruwan da tasha bacci ya kwashe ta shiyasa ma bata san wainar da yake toyawaba. Ai cire rigar dayayi ne yasa hankalinsa mugun tashi domin wani abu yaji ya tsirga masa tun daga tsakiyar kansa har tafin kafarsa. Sanda ya cire mata kayan ya cire mata har under wears dinta saboda suma sun jike. "Innalillahi wa inna ilahi raji'un." Ya furta a dai dai lokacim da yaji kansa ya sara. Me hakan yake nufi. Maza yayi ya saka mata rigarta sanna ya saka mata skirt din ba tare da ya cire short nicker dinsa daga jikinta ba. Bai san kama ya zai ji ba idan yace zai zare wandon. Saboda haka hanyar lafia a bita da shekara.

Pheener(mrs Naseer)
08060154424

Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now