part 11

465 83 0
                                    

To a can Maleeta palace kuwa, bangaren Gimbiya Haleema ita da yar ta Fulani shirye shirye ake ta yi saboda sun san da zuwan sadauki kuma yariman Pasweek wato Usman(namijin zaki🦁)
Ko ina ka gifta a cikin sashen nan guda biyu kamshi ne zai daki hancinka, kama daga kamshin abinci kala kala sai kamshin daddadan turaren wuta da yake tashi, kasancewar Gimbiya Haleema Shuwa.
Duk da cewa ba a daya daga cikin sashen zai sauka ba, amma hakan bai hanasu gyarawa da kimtsa ko ina ba. shi ko part din da namijjn zaki zai sauka ba qaramin gyara ya sha ba.
Tun daga main entrance din wani sassanyan qamshi zai bugi hancinka.

Zaune na hango Fulanin a gaban dressing mirror dinta ta kurawa kanta ido. Tasha ado dan tsayawa fasalta muku irin kyauwun da tai ma bata lokaci ne. Ita kanta tasan tasha ado na kece raini. Saboda wannan mashahuriyar mai kwalliyar ce tai mata makeup wato AYNAS BEAUTY STATION, ga lalle da ta tsantsara mata kai abin ba a cewa komi. Ta fito ras da ita kaman mai shirin tafiya gasan sarauniyar kyau. Bugun tambura ne ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi, domin ko ba a gaya mata ba tasan namijin zaki ne ya shigo masarautar tasu, don su haka al'adar su take, duk sanda akai wani bakon saraki sai an buga tambari. A guje ta tashi ta nufi wani balcony da ya nuna mata katon farfajiyar gidan. Convoy din masarautar pasweek ta gani.. gyara tsayuwarta tayi tana jiran ta ganshi. Bayan guards sun fito tare da maids dauke da tray na gifts a hannunsa sai wani guard ya nufi wata hadaddiyar mota da ta kasance ta tsakiya ya bude owner's corner.. kafar sa ce ta fara dirowa, sai da yayi kaman 2 mins kafin dayan kafan ta sake fitowa. Duuuummm!!! Kirjin fulani ya bada. Bayan ya gama fitowa ne fulani tayi mutuwar tsaye... Wato kalar mijin da ta dade tana mafarki ta gani a tsaye. My Goodness ta furta a fili.. lallai ba ayi mata zabin tumun dare ba. Wani irin farin ciku ne ya lullube ta, a tame taji wani abu ya doki zuciyarta, sonshi da kaunarsa ya mamaye dukkan sashin jikin ta. Tunda Allah ya halicce ta bata taba neman abu ta rasa ba. Komi take so sai ya zama mallakinta, bata san wata kalma babu ba. Saboda haka da karfin gwuiwarta ta koma dakin ta. Ta sake kallon dressing mirror a karo na ba adadi tayi murmushin ta mai narka zuciyar mai kallomta sannan ta nufi hanyar main parlour dinta. Shi kuwa Usman direct sashen mai martaba suka nufa. Ba wannan ne zuwan sa Maleeta palace na farko ba, don haka ba laifi yasan kan masarautar. Dawowar mai Martaba daga zaman fada kenan yaji bugun tambari. Faffadan Murmushi yayi domin shi a ran sa yana kaumar Usman. Kuma kwarai yaji dadin wannan hadin domin kuwa ko ba komi Usman din mutumin arziki ne ga wanda ya san shi. Idan kana nesa dashi ne zaka ga kamar bashi da kirki. Domin shi dai baya munafurci ba kuma ya karya, sannan he's a man of his words. Wannan dalilin yasa ya shiga zuciyar sarki Ameenullahi. Ison da akai yiwa Usman ne yasa sarkin bada iznin ya shigo. Ya shigo shi daya babban parlorn mai martaba. Miqewa mai martaba yayi domin taro dan Aminin nasa kuma yaro magi soyuwa a gareshi bayan yayan da ya haifa. Usman din ma yasan kalar son da Sarki Ameenullahi ke masa. Haka kawai yaji jikinsa yayi sanyi da ya tuna da kudirin da ya zo wannan karon, shi kuma sarkin a tunaninsa kunya ce ke kokarin shiga tsakaninsu. Dariya yayi irin ta dattijawan arziki yace, Usman yau kuma kunya ta kake ji?? Sosa keya Usman din yayi a ramsa yace dole naji kunyarka mana, soyayyar da kake min tun ina yaro yau ace zan qi jininka?. Basarwa yayi sannan ya duka ya kwashi gaisuwa, mai martaba bai gushe ba yana jan sa da hira har sai da ya saki jikinsa. Sannan yayi umurnin a kaishi masaukin sa. Ba jimawa suka kama hanya. Har sunyi nisa kiran mai martaba ya iske shi, ba musu suka koma mai martaba ya bashi umarni yaje su gaisa da Gimbiya babba da qarama, kada kace sai kaje ka huta tukuna, kasan wannan zuwan ya banbanta da sauran zuwan da ka saba. Domin wannan neman aure kazo, kuma kada ka manta da halin mata. Kasan abin magana babu wuya.
Murmusawa yayi sannan su ka kama hanya zuwa sashen Gimbiya Ameera domin shi ne dama da sahen mai martaba. Sun gaisa kuma sun sami tarba mai kyau ba laifi. Kafin su karasa sashen Gimbiya Haleema har labari ya isar mata ai sashen Gimbiya Ameera suka fara zuwa. Ranta yayi matukar baci amma tsabar duniyanci sai ta kanne, ta maida komi ba komi ba. Ta tarbe su hannu bibbiyu sannan suka wuce masaukinsu. Shi kansa gyaran da akaiyiwa sashen ya birgesa. Haka ya shige dakin da ya saba sauka sannan ya bada umarnin kada wanda ya kusakura yayi ko kwakwkwaran motsin da zai dameshi. Haka ko wanne bawa ya shiga taitayinsa tun daga bayin da suka zo tare daga Pasweek har bayin Maleeta.

Tun Fulani na jiran azo ayiwa Yarima iso har ta gaji. Ga dare ya fara yi. Haka ta fito ta nufi sashen Gimbiya bayi na biye da ita. Ta na shiga kofar sashen duk wani bawa na sashen yayo waje. Tana shiga ta karasa a guje ta je ta kifa kanta a cinyar Mummyn tata ta rushe da matsanancin kuka. Dariya tasa bawa Mummyn amma sai ta kanne ta hau rarrashinta. Mena kuma Fulani ta?? Haba yar sarki jikar sarki kuma matar sarkin nan gaba! Dagowa tayi da sauri, mummy amma ai ba yarima Usman ne babba ba. Akwai yaya Chiroma ko? Taa ya zan zama matar sarki? Wani shu'umin Murmushi Mummyn tayi sannan tace, kin manta wace Mummynki kenan? To I'll never rest har sai naga na cika miki burinki na zama matar sarki..
But mummy how??
Dariya ta sake yi sannan tace Nice fa.. babu abinda bazan iya ba don gamin farincikin yata daya tilo. This is a mother's promise.
Murmushi Fulani ta sake yi a karo na ba adadi sannan kuma ta kwabe fuska zata sake kuka. Me kuma ya faru my princess?? mummy fa yarima Usman din bai nemeni ba. Kalli fa kwalliyar da nasha amma ko nemana baiyi ba. Kuma mummy I'm falling for him. Dariya sosai Gimbiya tayi sannan tace to shine me?? Gobe idan Allah ya kaimu ai dole ya nemeki. Kuma i promise u dole ya so ki. Domin nasan tunda yake bai taba ganin kykykyawar ya irinki ba. U r the most beautiful girl a duk duniya. Gaki fara, farar mace alkyabbar mata. Ga iya kwalliya, ga sarauta, ga gata, ga ga ga.. komi fa kin hada. Dariyar jin dadi tayi sannan tace I'm sleeping here mummy. Hmmm, Mummyn tace sannan tace to wuce waccan dakin kin kwanta. To sai muce Allah ya tashe mu lfia.
A dinga voting dan Allah.

Nafisa Aliyyu(pheener)

Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now