part 20

441 42 0
                                    

🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁
    *NAMIJIN ZAKI*
🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁

   By
_Nafisa Aliyu_
    *(mrs Naseer)*

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*📚🖊️

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.
'''🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
______________________________________

Page 20

To yau ya kama ranar da Chiroma zai dawo gida. Shirye shirye a bangarenAunty Suwaida babu kama hannun yaro. Ita da Meeno suke ta bawa maids order din abinda suke so ayi. Sun kira shahararriyar mai kwalliyar nan mai suna *'Aynas Beauty station'*
Tazo tayi musu zanen lalle na zamani sannan ta cancadawa Aunty Suwaida kwalliya ta gani ta fada. Ihu Meeno ta saki da taganta ta fito.
"Aunty na, kece kuwa ko chanjo ki akai."? Meeno ta fada da sigar zolaya.
"Chanjo ni akai din, 'yar rainin wayo." Itama Suwaidan ta bata amsa. Shagwabe fuska Meeno tayi tare da cewa."Dan Allah aunty Suwaida nima ta min kwalliyar wallahi sha'awar yi nake kinga ban taba ba."
Dariya Suwaidan tayi sannan tace da Aynas Beauty station din tayi mata kwalliyar.
Ko da akai aka gama ai sai da ita kanta Suwaidan ta tsorata da kyau irin na Meeno. Gaba daya sai ta raina kanta. Gani take yi kamar wata sabuwa ce ba Meeno ba. Tuni shedan ya soma rayo mata tare da bijiro mata da wasu tunaninnika. A take ta yaqe shi da yake ita ma'abociyar ambaton Allah ce. Amma duk da haka zuciyar ta bata bar raya mata wasu abubuwa ba. (Kun san mata da kishi).
Haka kawai ta tsinci kanta da cewa."Meenal, tashi zakiyi kizo ki tafi. Saboda na dade ban ga miji na ba. Ina so idan yazo mu kasan ce mu 2 kawai. Ki tashi ki sallami duk bayin da suke cikin part din nan sanna kema sai ki tafi. Ya zama masu tsaron kofa ne kawai a wajen."  Ita Meeno bata kawo komi ba, saboda haka tashi tayi daga kujeran da take zaunetana dariya har da rera waqa saboda tsokana tana cewa."soyayya dadi yafi zuma dadi." Dariya itama Suwaidan tayi ta tashi ta bita da gudu.
Gudu itama Meeno ta saka ta nufi kofa. A bakin kofar sukai kicibis dashi. Har ga Allah da farko bai ganeta ba. Sai da ta saka ihun murna tana."Oyoyo yaya Chiroma oyoyo."
Muryar ya dauka sannan ya tsaya ya kare mata kallo.
"Meenal." Y furta da mamaki a fuskarsa. Suwaida ce ta karaso da gudu ta rungumeshi. Sai a sannan ya dawo daga duniyar da ya fada. Ita ko Meeno tunda taga haka ta sulale ta fita tare da sallanar maids din part din kamar yadda Auntyn tata ta bata umarni.
Tun daga ranan ko Meeno tazo part din bata ganin Chiroma domin kuwa shirye shiryen bikin kanin nasa ya boye shi.

To a kwana a tashi babu wuya a wajen Allah. Yau ya kama saura kwana daya a daure auren Usman da Fulani Nawwara. Idan ka ganshi baza ka iya tantance a wani hali yake ba. Shi dai yasan ba faranciki yake ba, amma kuma ya nemi wannan bacin ran nasa ya rasa. Mai martaba ne ya kirashi tare da bashi dumbin dukiya wai ko yana da bukata. Ba musu ya amsa tare da yi masa godiya sannan kowa ya shiga motar da zasu wuce Maleeta palace din. 
Da yake daurin aure kawai za ayi a can shi yasa iya maza ne kawai zasu je. Daga nan sai a tawo da amarya da danginta sanna azo nan Pasweek ayi shagulgulan biki. Da yake haka al'adar su take.
Chiroma na gani ya fito a gaggauce daga bathroom daure da bathrobe a jikinsa. Suwaida ce ta shigo tana yamutse fuska domin wannan cikin nata yasa bata son qamshin sabulun da yake wanka dashi. Kallonta yayi sannan yace."ya dai Mummyn baby."
Dariya ta dan yi sannan tace."wallahi bana son wannan qamshin sabulun."
Dariya shima yayi sanna yace."ayi hakuri to na dena wanka dashi ranki ya dade. Kinga fa na makara fa. Nasan su main martaba ba sun dau hanya. Kawai kin makarar dani."
Kwabe fuska tayi tace."ka dai makarar da kanka, ba kai ne kaki ka barni na huta ba tun dare kake abu daya." Bayan tayi maganar ne kuma kunya ya kamata da gudu ta fada jikinsa tare da boye fuskanta a kirjinshi. Dariya yayi ta mata.
Qamshin sabulun da ta shaqa ne ya sa ta kwara masa amai a jikin sa. Sannu ya hau yi mata sannan ya dauke ta yayi bathroom din da ita. Bayan ya wanke ta ne ya fito da ita sannan shi ma ya sake wanke jikin sa ya fito ya shirya a gaggauce.
A parlour ya same ta da ita da Meeno tana gyarawa Meeno gashinta. Saboda ita Suwaida tana son gashi, ita kuma Allah bai hore mata ba saboda haka take yawan gyarawa Meeno nata. Dauke kansa yayi dga gashin nata domun shi ya kasance ma'abocin son suma kamar dai irun ta Meeno din. Tunanin ya katse da cewa."mu zamu wuce.". Sai a lokacin ta san ma ya shigo parlorn. Gaishe shi tayi ya amsa kadaran kadahan.
"Yaya ina zuwa kuma haka na ganka da jaka."?
"Maleeta." Ya bata amsa a takaice. Dariya tayi sanna tace."Hausawa sunce kyan alkwari cikawa, yau zaka cika min to. Zan bika Maleeta ina so naje naga Ammi na dan Allah."
Katseta yayi. "Bazan iya ba Meenal, tafiyar kwana 2 ce zamuyi. Auren Usman ne zai kai mu. Kuma babu mace ki daya cikin tafiyar.".
Fuska ta shagwabe sannan ta dubi Suwaida da saura kadan ta fashe da dariya tace." Ki sa baki Auntyna."
"Ko ta saka baki ko bata saka ba babu inda zani dake. Ki tambayi wani abun ab dai zuwa Maleeta ba yau. This is my final decision."
Bata san san da ta fashe da kuka ba ta fada jikin Suwaida. Shi mamaki ma ta bashi. Daga wannan maganar sai kuka. Suwaida ce take ta lallashinta sanna tace."Dan Allah Hubby ka tafi da ita, ni bazan iya da rigimar ta ba wallahi ka tafi ka barni da ita wuni zatai tana kuka."
"Tashi mu tafi." Ya fada yana fita daga parlorn. Ihu ta saka sannan ta cire mayafin kan Suwaida ta yafa dama doguwar riga ce a jikinta. Dariya Suwaidan tayi sannan tace Allah ya shirya Meenal.
Driver ne  yake tukawa, da yake qaramar mota ce. Baya chiroma ya shiga ita kuma ta shiga gaban motar. Suwaida ce ta musu addu'ar dawowa lfia sanna ta kima ciku su kuma suka dau hanya.
Pheener(Mrs Naseer)
08060154424

Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now