Part 4

1.2K 78 0
                                    

Sarki Rasheed na hango zaune akan kasaitacciyar karagar mulkinsa a cikin fada. Fadar kewaye take da dakaru ko ta wanni bangare. Fadawa da sauran mukarraban sarki suna zaune suna zuba fadanci.
Zaman fada yana tafia lafia kaman yadda ya kamata. A gefen sarki Rasheed na hannun dama na hango Khaleel zaune hankalinsa gaba daya yana kan sha'anin fadar da ake gudanarwa inda daga hannun hagunsa na hango namijin zaki 🦁 zaune fuskarnan a murtuke kaman kullum. Kana ganinsa da yanayinsa kasan hankalinsa baya kan wannan sabga da ake. Shifa in kana so kaga walwalarsa to fa ana shirye shiryen shiga fagen fama ne. Bayan an kammala komi ne fada ta watse sarki Rasheed ya nemi ganawa da Khaleel da Usman (namijin zaki 🦁)
Bayan sun kwashi gaisuwa ne sarki Rasheed ya fara magana kaman haka Dafatan kowa yana cikin koshin lafia. Dalilin wannan tara ku danai shine kai Khaleelu ina so na tura ka wani aikin birnin Zabbit. Domin sarkin garin naga yana neman ya kawo min cikas a cikin wani alamari dana saka a gaba. Saboda haka zan aika a matsayin ka na babban daa kuma mai wakilta ta a ko ina. Kaje ka kaiwa sarkin Zabbit jan kunne tare da tsoratarwa kan cewa ya fita sha'anina. Ko da sarki Rasheed yazo nan a zancensa sai Khaleelu ya duqa yace an gama ranka ya dade. Sannan sarki ya kaara da cewa kai Kuma Usmanu ina so ka maye gurbin Ciroma kafin dawowarsa. Dan nasan tafiyar tasa zata kai wajen wata 2. Take naga kammanin Usman sun sauya, ya shiga tunani me yasa Abbinsa zai masa haka?? Shi fa ba wai san shiga sha'anin mulkin nan yake ba. Me yasa shi baza a aike shi ba. Ga abinda yafi muradi. Watakila ma yaki ya barke a can birnin da Khaleelun zai je. Shi kuwa zaiso ace shi zai je wannan birnin. Shi ina shi ina wata sarauta. Kai bazai yiwu ba. Sarki yana lura dashi da sauyawar yanayinsa amma ya share dan ya riga yasan dalilin sauyawar tasa. Kuma yana sane yayi hakan saboda yasan namijin zaki 🦁 ba wai fiye son shiga harkar sarautar yake ba. Shi yasa yayi wa Ciroma Khaleel wannan aiken dan shi Usman ya dinga shiga harkar fadar.
Bayan sun gama wannan zama ne kowa ya watse. Ciroma ya kmaa hanyar shashin sa shima Namijin zakin yay tasa hanyar.
Bayan kwana 3 da faruwar hakan ne Ciroma ya fara shirin tafiya inda shi kuma namijin zaki 🦁 abin duniya ya taru yayi masa yawa.
Yau lahadi ta kama rananr tafiyar ciroma birnin Zabbit. Da sassafe bayan yayi sallama da iyalinsa ne ya shiga sashin mai martaba. Bayan an masa iso ne yaje ya duqa yace mu munyi haramar tafiya ranka ya dade. Sarki ya jinjina kai yace Allah ya kiyaye hanya ya kai daana. Allah ya dora ka akan makiya. A kiyaye fa. Banda shahsancin nan naka wai kai mai tausayi. Kana zaune kana sokanci makiyi zaici galaba akanka. Saboda haka ne ma yasa nafison irin wannan tafia na tura Usmanu. Amma saboda wata manufa tawa yasa na tura ka. Ciroma ya jinjina kai yace inshaa Allah Abbi. Yana mamakin mahaifin nasa wai taysayin na kasa ne shashanci. Shi abin ma mamaki yake basa. Da haka yayi sallama da Abbinsa ya tashi ya kama hanya. Inda ya samu rakiyar dakarun sojoji masu yawa.

Birnin Maleeta

Washegari da sassafe kuwa Baana ta tashi suka hau shirin tafia gidan Baffa. Ko da ta leqa dakin da Maigado da Meeno suke a kwance anan ta tabbatawa da kanta cewa yau ma Meeno ba gida ta kwan ba. Gefe guda kuwa ga Maigado kwance tana ta sharar baccinta. A gigice ta tashe ta tana kuran Maigado kinga irin abinko? Kin gani ko?? Yauma yarinyar nan ta fita. Kuma zo kiga gashin nan gidan a rufe yake mukullin a ina kika aje?? Maigado ta tashi a firgice tana kiran Allah. Tana wallahi ga dan mukullin nan a gefen zanina na daure shi. To ta ina ta fita?? Anya kuwa ba aljanu bane suke a tattare da wannan yarinyar ba kuwa?? Anan suka zauna suna ta tattaunawa. Suna cikin wannan zullumi har kusan azahar kafin daga bisani sukaji sallamar Meeno. Bayan ta shigo ta bisu daya bayan daya ta gaida kowa. Ita dai Maigado binta kawai take da kallon mamaki. Yarinyar du du du nawa take?? Allah da iko yake, Ta furta a fili ni Bilkisa yau ina gnin ikon Allah. Wannan lalacewar tarbiyya har ina?? Sai kuma ta fashe da kuka ta hu cewa saboda kawai kasa ta rufewa Yaya ido yasa akai skaci da trbiyyar yar nan? Laa ilaha illa anta subhanaka inni kuntu miszzalimin. Da nasan haka za a bar yarinya ta lalace da banmu barta a hannun mace ba. Mu dai ba a mu Fulani ba. Wannan rashin kunya da rashin tarbiyya b asan Fullo dashi ba. Shi yasa tun da farko muka ki amincewa yaya ya auri babarbariya. Amma tsautsayi baya wuce ranarsa. Da jin wannan batun ran Meeno yayi mugun baci. Tayi niyyar fadar maganganu wa yagwalgwal din ta Bilki. Amma sanin ran mahifiyarta zai iya baci yasa ta daure.

Baana bata ce qala ba tace da Meeno maza shiryo ki fito kizo mu tafi zamu wajen Baffanki na tudu. Ta amsa da to sannan ta shiga ta shiryo tazo suka dau hanyar gidan Baffa. Bayan tafia mai nesa suka isa gidan baffa daf da maghriba. Sun samu tarba me kyau tunda an san da zuwansu kuma baffa yana da hali sosai.
Bayan sunyi sallah sunci sun sha sun huta suka zo suka gaggaisa da mutanen gidan. Sun dan jima suna hira kafin dgaa bisani kowa ya koma masaukinsa sukai sallar isha sannan suka sake dawowa inda suka samu Baffa a parlorn kasa suka sake gaisawa. Inda ya umurce su da su koma su huta gobe d safe sai su tattauna. Gidan baffa gida ne mai girma inda a bkin gate ma sojoji ne suke gadinsu sama da su 5.
Washegari da safe bayan sun tashi sun gaisa sunci abinci anan Baffa ya nemi ganawa dasu. Bayan sun gaisa ne yake tambayar me yake faruwa?? Anan Maigado ta zayyana masa komi da komi kai kace ita aka tambaya. Baffa ya tambaye Baana ko haka ne?? Ta amsa da eh. Nan yafara tambayar Meeno cikin lislama me yake faruwa. Meeno ta kyekashe kasa taki tayi magana. Akai akai da ita amma tyi shiru. Daga karshe Baffa ya ynke shawarar zamata anan gidansa n tsawon wata guda ko za a samu tayi magana asan meke faruwa. Kafin daga nana asn abin yi.
Baaana tayi kukan bakin ciki ta gode Allah. Bayan sun dawo daki tayi tayi da Meeno ta gaya mata meke faruwa amma yarinyar nan kamar kurma. Taki tayi magana.

Pheena 👑

Namijin Zaki 🦁 Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin