page 8

432 52 1
                                    

Kasancewar sarki Ameenullahi mutum attajirin gaske shi ya kulla amintaka a tsakaninsu da sarki Rasheed. Domin shi Sarki Rasheed ya kasance mutum mai capitalism din tsiya. Shi sa ko kadan bai shiri da talakawa. Wannan ne babban dalilin da ya sa idan kaji abokansa to ko dai basarake, ko kuwa hamshakin mai kudi. Dan ko a cabinet members dinsa ma babu mara arziki.

Matafiya Allah ya sauke su lafia. Domin kuwa gasu sun iso birnin pasweek dan tsakaninsu da Pasweek palace ma bai wuce tafiyar minti goma ba. Ko da su ka karasa palace din ma, shikam Chiroma bai bi ta kan Meenal ba. Kasancewar a gajiya ya dawo shi ya ma manta da wani zancen ta. Su kuwa sauran maids din da kowa ta san hurumin ta kowaccen su sai ta kara gaba a ka bar Meeno tsaye tana karewa mighty building din kallo. Juyowar da zatai taga babu sauran maids din da sukai tafiya dasu. Sai dai dai kun mutane da su wulgawa su din ma guards ne domin kuwa wajen qarfe 10 suka dawo na dare wanda akasarin jama'ar fadar kusan sunyi bacci don haka al'adar masarauta r take kowa da wuri yake bacci sai masu tsaron wajen da suke kai kawo.  Ta danyi jim kamar tayi tambaya To wa ma zan kama in tambaya? Ince masa me ma?? Hasbunallah. Ta furta rai a dakile. Ni duk gajiyar nan in sauke a ina?? Haka za a barni a nan?? How i wish my friends will come.. i wish u come over ko zaku sama min inda zan huta. Mchwww ta kara jan tsaki a karo na babu adadi kafin ta yanke shawarar bin wata hanya da taga bata fiye ganin guards din suna bi ba. Haka ta dinga bin hanyar nan domin ko ina na masarautar akwai haske gallele. Tana tafe tana yar wakarta kai kace ba a damuwa take ba.
A cikin wannan yanayin kawai taganta ta bullo wani dankareren part. A ranta tace nan ne sashen mai martaba kenana. Girman wajen yayi mugun bata mamaki. Har ta juya zata koma domin ita tasan nan sashen mai martaba ne, juyowar da zatai daga bangaren daman ta ta hango wani kayataccen lambu. Tunda take a rayuwarta bata taba ganin waje irin haka ba. Woooooo amma gayun nan baku kyauta min ba. Yanzu duk kyan wajen nan bamu taba zuwa ba. A gaskia sai na shiga wajen nan. Ta fada kamar wani take bawa labari tare da nufar hanyar garden din. Iya kayatuwa wajen ya kayatu. Haka ta kutsa kai ta shiga. Bata wani jima tana zagaye wajen ba domin ba wani girman azo a gani ke da wajen ba. Kana tayiwa kanta matsuguni tare da daukar ayaba takai bakinta hadi da lumshe ido. Haka ta yi ta ciye ciyenta har sai da ta take cikinta tayi hamdala sannan ta cire mayafin kanta ta lullube kafarta dashi ta gyara kwanciyar ta akan resting chair har zuwa sanda bacci ya dauketa.
Shi kuwa chiroma ko da ya koma sashen sa ya rage gajiya da watsa ruwa tare da cin abinci bai dade ba bacci yayi awon gaba dashi. Mai martaba ma da yaji shiru yasan gajiya ce dan haka bai nemi ganinsa ba.
Shi kuwa Usman a bangare daya murna yake da dawo war chiroma dayan bangaren kuma damuwar sa ce ta tsananta. Yana murna zai bar sha anin mulkin nan yana kuma bakincikin karatowar tafiyar wai wajen wata banza da sunan yaje neman aure. Mchwww ya kara jan dogon tsaki tare da kallon dankareren agogon bangon dake manne a falonsa. Karfe 11 da minti 23 ya nuna. Tsaki ya kara ja tare da daukar fresh milk ya nufi dan corridor din da zai sada sa da main kofar fita daga chamber din. Ko da ya fito babu wani sauran guard a wajen domin shikam babu wasu guards da suke tsaronsa. To ai shi kadai gayya ne shi yasa ma su mai martaba basu matsa masa ba akan maganar guards din. Direct hanyar da zata sada sa da wajen shakatawarsa ya nufa. Domim bai da wajen hutawa kamar garden din nan nasa. At least zaijk kukan tsuntsaye masu dadin sauraro. Da yake akwai wata kofar daga wajen hanyar shiga part dinsa tanan yabi ya shiga. Ya wuce inda ya saba zama domin shi kullum sha'aninsa akan kai'ida yake. Yaje ya nemi wajen zama ya zauna yana me daddana wayarsa. Yafi karfin awa 2 anan yana sake sake a ransa yana shakar iska mai dadin gaske kafin yaji ransa ya dan sarara. Sai a lokacin yaji zai iya kwanciya yayi bacci. Ai kuwa haka ya tashi ya fita ba tare da ya kula akwai mutum a cikin garden din ba. To waye ya isa ma ya shigo masa??
Sai muce Allah ya tashe mu lfia.

Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now