part 31

442 65 6
                                    

🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁
    *NAMIJIN ZAKI*
🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁

   By
_Nafisa Aliyu_
    *(mrs Naseer)*

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*📚🖊️

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.
'''🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
______________________________________

Page 30

*Wannan page sadaukarwa ne gareki Ashque Namijin Zaki fans group whatsapp.. Allah ya bar kauna ya kara zumunchi.*

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya tsakanin wadannan ma'auratan cikin jin dadi da kwanciyar hanakali. Burin Fulani ya cika domin babu laifi yana bata kulawa dai dai gwargwado. Suna hada shimfida sannan ita kuma tana nuna masa tsantsar soyayya.
Shi kansa ya fara enjoying wannan rayuwar.
Ita ko Meeno gobe ne tafiyar su Zabbit ita Zahra. Duk wani shirye shirye sunyi shi sun gama. Duk da cewa Meeno tayi kokarin ta dinga zame kanta daga sha'anin 'yan gidan amma abin ya gagara domin ko dai Suwaidata aiko ko ta zo da kanta ko kuma Ummi ta aiko a kira mata Meeno wai tai mata tausa.
Yau ma sai wajen karfe 8 na dare ta dawo gidansu domin yanzu fafur ta dena kwana ba a gidan Auntyn ta ba. Haka kawai bata son ta dinga shishshige musu..
Tun da ta dawo gidan take murna don ko ba komi zata je Zabbit zata ga Gimbiya Hansa'u. Kai tsaye bayi ta nufa tayi wanka sannan ta zo dakin da ya zama kamar nata ta saka wata doguwar riga kana ta fito dan ta tarar da Auntynta. Hira suka dan taba sanna tayiwa Auntyn tata sallama saboda tanason ta kwanta da wuri dan ta tashi da wuri saboda sammako zasuyi gobe...

Washe gari kuwa da sasafe suka buga uban sammako suka dau hanya.  Ummi ta hada musu tsaraba da zasu kai wa Gimbiya saboda yanzu ta dalilin Meenal sun zama kawaye suna waya ma da ita lokaci zuwa lokaci.. sun sha tafiya mai nisan gasje kafin suka isa.. da yake an sam da zuwan su sun sami yarba mai kyawun gaske.
Da gudu Meeno ta tafi taje ta rungume G.Hansa'u. ita ma Gimbiyar Hugging dinta tayi tana cewa."yi a hankali Meenal kada ki balla ni kin san jikin tsufa."
Dariya Meenon tayi tace."Haba dai ur majesty wanne irin tsufa kuma?? Idan fa aka ganki sai a rantse shekarar ki 22."
Dukkanin su babu wanda baiyi dariya ba.
Yarima da yake tsaye yana kallonsu saboda Mamin sa ta na yawan yi masa maganar Meenal yau dai yaga Meenal..
Gata kyaykyawa masha Allahu..
Sakinta Gimbiyar tayi sannan ta kamo hannun Zahra ta rungume ta tace."ke ce Zahra ko?"
"Eh Nice Ranki ya dade." Zahran ta bata amsa sannan ta rusuna har kasa ta gaishe ta..
Kallon Zahra yayi, ai ko wannan ya gane fuskar ta.. amma da yake shi jininsu bai hadu ba sai ya dauke kansa yagi kamr ma bai ganeta ba.
Zama sukai suka sake gaggaisawa sannan Mami tayi introducing dinsu wajen Yarima Safwan..
Zahra ce ta dago ido ta kalleshi sannan ta nuna shi alamar ta sanshi."Kai ne dama."?
Kallonta Mamin tayi sanann tace."Ahh 'yata Zahra dama kin san shi ne."?
"Eh Mami ai Makaranta daya muke yi dashi."
Murmushi Mamin tayi. Shi kuwa gogan naka sai yace."Ni ban ma gane ki ba."
Wani kululun bakin ciki ne ya tsaya mata amma sai ta danne.
Meeno yake ta ja da wasa da dariya amma ita kuma tana nokewa saboda haka kawai wata irin kunyarsa take ji.. Zahra da ta fahimci ba ta ita ake ba awajen sai tayi sallama dasu tace zata je ta dan huta..
"Ya kamata ai saboda kun Sha hanya." Mami ta fada sannan tasa aka nuna musu masaukin su.

So haka suka cigaba da zama a burnin na Zabbit kowa yana nuna musu so da kauna.
Yau kwanan su 3 da zuwa.. a kwana 3 nan shaquwaa ta dan shiga tsakanin Yarima Safwan da Meenal. Kuma babu laifi yana dan sakarwa Zahra domin yanzu ta zama wata shiru shiru.

To a can gida kuwa Namijin zaki ne ya lura kwana 2 baya ganin Meenal.. gaba daya sai yaji baya jin dadi. Yaje wajen Ummi bai ganta ba, yaje wajen Suwaida ma bata nan. Shifa bai san ma ina zai ganta ba. Yanke shawarar tambayar Ummi yayi..
Yau da safe da ya tashi yaje su gaisa da Ummi ne yake tambayar ta."wai ko ni ina 'yar amanar nan? Yau fa wata na kusa. 2 kenan da faruwar wannan abun. ina so na mata wasu tambayoyin.."
Murmushi Ummi tayi sannan tace."Ayya Meenal ai tana Zabbit ita da Zahra."
"What! Zabbit fa kika ce Ummi?? Uban me suka je yi can din kuma yaya Chiroma yana nan gida?? Su da wa suka tafi? Ohh Ummi, yaushe zaki bar yar mutanr tayi irin wanann tafiyar? Gaskia zan bisu can din."
Yadda duk yabi ya gigice ne ya bawa Ummi mamaki hadi da dariya abin ya bata.. "To kai Usman mene damuwarka haka?? Yarinyar nan fa a hannun qanwar babanta take. Kuma ita ga amince taje ba ni na tura ta ba. Kuma kasan mene tsakaninta da Gimbiya Hansa'u ne?.. bai bari ta ida maganar ba ya katseta."Ohhhh Ummi, ba maganar wai ba kece kika tura ta ba. Magana ake ta tsaro da lafiyar yaran nan.. Yanzu zan shirya in tafi Zabbit Ummi. Na gama magana ni."
Yanzu kuma abin tsoro ma ya bata.. anya Usman lafiyar sa kalau.. to Allah dai ya sawwake..

Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now