part 9

446 50 1
                                    

A lokacin da aka kwala kiran assalatu a babban masallaci dake masarautar, yayi dai dai da farkawar Meeno, sai a lokacin taga ta tintsiro kasa. Domin ko tana da nauyin baccin, haka ta tashi tana dubi dubi kafin idonta ya sauka kan famfo. Wajen ta nufa tare da tsinko wani icce a jikin wata bishiya. Ta goge bakinta tas da asuwakin kafin ta kunna famfon danyin alwala. Ta gama alwalarta a tsanake kana ta nufi wajen da tayi bacci, ta tsaya tayi kuri tana tunanin to ina ne gabas?? Shiru tayi na wasu yan dakiku kafin ta yanke shawarar kallon inda zuciyarta tafi amincewa nan ne qibla tare da kabbara sallah.
To ko shi ma Usman a kunnemsa aka kira sallar haka ya mike yaje bathroom ya dauro alwala sannan ya fito ya nudi masallaci. Shiko chiroma tsananin gajiya yasa ya kusan makara domin kuwa sau 3 matarsa tana tashinsa kafin ya tashi din. Bayan sun idar da salla ne suka fito a jere, Chiroma Khaleel ya mikawa Usman hannu dan suyi musabaha suka gaisa. Usman din ya tambayeshi ya hanya ya kuma aiki ya amsa da lafia lau. Suna tafe suna dan taba hira. Duk wanda suka ci karo dashi sai ya kwashi gaisuwa, Chiroma kadai ke amasawa shi ko namijin zaki ko kallo basu isahe shi ba. A haka har suka karasa marabar da ta raba su domin kowa ya karasa sashin sa. To, bayan wayewar gari ne wasu bayi masu kula da lambun nan suka zo domin sharewa da gyarawa. Aiko anan suka ci karo da Amina akwance domin har wani baccin ya sace ta. A figice suka juya domin a iya sanin wadan nan maids din babi wannan yarinyar a masarautar nan, ita ba baiwa bace domin ba irin uniform dinsu ke jikinta ba, ba kuma su da masaniyar zuwan wata bakuwa dan haka suka juya suka je suka sanar da wasu guards. Kasancewar duka bayi maza ba ma bayi duk wani namiji da ya kwan ya tashi a birnin na pasweek jarumi, haka yasa ko dar basuji ba suka nufo garden din. Ko da zuwansu daya ya daka mata tsawa, a gigice ta farka tana rawar dari ta juya ta kallesu tare da fara muzurai. Ya tambayeta daga ina?? Itako ta ja bakinta ta tsuke. Tambayar duniyar nan yarinyar nan ta ki cewa uffan. Haka suka tattara ta suka nufi wajen aikinsu suna jiran Usman ya fito domin basu da ikon da zusuje suyi knocking wa Usmanu kofa. Haka kowa ya cigaba da sha'aninsa ita ko tana takure waje daya idanu ya raina fata. Shi ko Usman har sai zuwa 12 na rana ya samu fitowa. Ko da ya fito wani bawansa ne yayi kokarin yi masa bayani cewa an samu wata yarinya a cikin garden dinsa kuma anyi anyi tayi magana taki. Yallabai inaga yarinyar nan tafi kama da aljanu domin kyawunta kadai ma ya isa ya bayyana haka. Yallabai aljana ce. Tsawa Usman ya dakawa wannan bawan kafin yace kayi haukane? Ina ruwan wani da ko mutun ce ko aljana?? To koma wace ce wannan yarinyar sai tayi min bayani dalilin ta na shiga Garden dina. Ko kurma ce ita yau sai bakinta ya bude. Saboda i see no reason da wata can daban zata shigar min garden ba tare da izinina ba. Ya fada kamar baya son yin magana tare da wucewa don ya karasa fada. Ko da shigar sa fadar ya kwashi gaisuwa wajen takawa. Bayan anyi abinda za ayi a fadar ne takawa ya nemi ganawa da duka 'ya'yan nasa. Bayan sun kara gaisawa ne Chiroma yayi bayani game da tafiyar sa. Kwarai mai martaba yayi murnan jin cigaba da aka samu. Shiko Usman hankalinsa kaf baya wajen don haka Allah Allah yake a sallame shi ya bar wajen. Sarki Rasheed ya fahimci hakan sai ya kalli Usman yace ya maganar tafiyar taka Usmanu?? Namijin zaki sa hankalinsa ke kan ya koma yayi hukunci wa wannan yarinyar yace next week ne Abbi nake son tafiya m. Sarki ya jinjina kai cikin gamsuwa yace Allah ya kaimu tare da shi musu albarka kana ya sallame su.  Sai bayan ya baro fadar ya tuna da katobarar da yayi. Next week fa nace wa takawa zanje wajen wannan abar?? Lallai nayi wawta.

Haka ya karisa part dinsa ransa a dagule, lallai yarinyar nan sai ta amshi hukunci mai tsananin gaske. (Ni ko nace kamar itace tasa za a maka auran dolen).yana komawa ya bada umurnin a kawo masa wannan yarinyar, bawan da ya tiso ta a gaba ne ya durkusa domin gaishe da chiroma, kamar anve ya kalli bayan bawan nan ya ganta, aiko wannan itace yarinyar da ya taba gani a Zabbit har ta masa rashin kunya. Ita dinma ta tuno shi saboda haka sai ta sunkuyar da kai.  Murmusawa yayi kafin ya tambayi bafaden ina zasu je?? Yace yallabai ai wannan yarima Usman ke nemanta, ta shiga lambun sa ba tare da izini ba shine yake nemanta ya hukunta ta.
Da yake taji an ambaci chiroma sai tayi wuf tace, Allah ya taimaki chironi ce yar amana da aka hado ku da ita daga birnin Zabbit domin ka kawoni wajen Auntyna, to jiya sai na bata bayan dawowar mu gashi dare ne, saboda haka sai na tsinci kaina cikin lambun nan. Shiru Chiroma yayi na wani dan lokaci kafin yace haka ne, kai ka barta nan wajena kaje ka gaya wa Usman wannan din bakuwa ta ce. Yayi hakuri bata tayi bata san garden dinsa bane. Ya fadi haka yana mai nunawa Meenal hanya domin ta wuce su tafi. Hakan kuwa akai, duk da Usman baiji dadin yadda bai hukunta ta ba amma babu yadda ya iya. Shiko Chiroma ko da tisa ta gaba basu zame ko ina ba sai bangaren Umminsa. Yaje suka gaisa daga bisa ya fito ya sake tisa ta agaba sai suka wuce wani dan karamin gini mai kyawun gaske. Guards suka vude kofa ya shiga gidan. Nan ne wajen ganawa da bakinsa kuma anan yake hutawa. Bayn sun shiga cikin parlon ne ya zauna akan coach ita kuma ta nemi waje a lasa ta rakube. Ya kalleta ya ganta duk a takure yayi murumshi ciki ciki sannan yace dago ki kalleni mana rasa kunya. Zaro ido tayi, kar taje dai ya gano ita din ce fa. Sai ta kara sunkuy da kai kamar mutuniyar arziqi tace Allah ya taimaki Chiroma kayi hakuri, wallahi tallahi ban san kai bane, kuma wallahi da nasan kaine... Bata karasa ba ya katse ta da kin san nine me?? Ko nine ko ba ni bane ya dace ki kalli kamar ni ban haifeki ba ki min fitsara?? Ni fa na tsani karya, a yaushe ka isa ka haife ni?? Maganar da take a cikin ranta kenan bata ma san ta fito fili ba. Kara kallonta yayi da mamaki. Lallai kin cika fitsararriya, sai a lokacin ta lura ta yi babban kuskure, toshe bakinta tayi da dukkanin hannunta tana kara zazzaro manyan idanunta. Ya sani sarai subuce mata maganar tayi, dan haka sai bai ji zafi ba ko kadan, amma a zahiri sai ya kare hade rai, yace lallai yau zan miki hukunci mafi tsanani a rayuwarki. Dafe kirji tayi tana mai marairaicewa, haba ranka ya dade kayi wa girman Allah kada ka sa a buge ni, wallahi ba ma kai ba kowa ma bazan kara yi wa maganar banza ba. Dariya taso bashi amma sai ya kanne yace silly girl a zuciyarshi a fili kuwa kara tamke fuska yayi yace ahhh ki ma kara. Kuma da ace bugunki zansa ayi ai da ya fiye miki koda bulala 100 ce. Ai sai kin gwammace ayi miki bulala 300 akan horon da zansa ayi miki. Kace kashe ni kawai zakai. Ta kara fada ba tare da san ta fito fili ba. A'a sam ni bana kisa. Amma dai kam kin kade a hannuna. Ya fada kamar ba da ita yake ba. Wani yawu mai daci ta hadiye sannan ta muskuta, bari tayi masa dadin baki, ta fada a ranta sannan ta karkatar da kai tace: yallabai ni fa sam ba haka labarinka ya iske ni ba tun ina Zabbit. Ance nin kai mutum ne mai adalchi da sanin mutumcin na kasa da kai. Kuma sannan kan da tausayi, ko kadan baka zalinci saboda haka nasan bazaka zalinci yar marainiyar Allah ba. Ta karasa tana mai goge kwallar munafirci. Duk da yasan Bribe ne maganganunta amma kiran kanta da marainiya da tai sai tayi matukar bata tausayi, sai tsintar kansa yayi yan cewa waye naki ya rasu, yawu ta sake hadiyewa sannan tace Babana. Babana ya rasu tun ina yar shekara 3 inji Umma na. Tausayi tasake bashi sannan yace to yi hakuri ki dena kukan. Allah yaji kansa. Ameen tace tare da sauke boyayyiyar ajiyar zuciya. Yanzu bari na kai ki wajen Ummi na idan yaso bayan kwana 2 sai na sa a nemo Auntyn naki ko?? Tace Uhhmmmm amma fa ni da an maida ni wajen Umma na da yafi min. Mamaki ta bashi sannan yace ko me yasa?? Ranka ya dade ni bana son zama wajen ta. Haka kawai taje ta rabo ni da mahaifiyata bayan tasan ni kadai na rage mata. Yanzu haka ban san a wani hali Umma take ciki ba. Ta fada tana kallonsa ta kasan ido dan taga ya zai respond. Jinjina kai yayi yace bana shiga family matters din mutane, butbari ki huta gobe sai ki bani labari me ke faruwa. Ta amsa da to sannan ta tashi tabi bayasa don su tafi wajen Gimbiyar. Wannan kenan.

Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now