part 14

358 43 0
                                    

🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁
    *NAMIJIN ZAKI*
🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁

   By
_Nafisa Aliyu_
    *(mrs Naseer)*

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*📚🖊️

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.
'''🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
______________________________________


Page 14

Ko bayan tafiyar Jakadiya ma babu abinda Mai gado ta cewa Meeno, domin ita yanzu haka ma shakkar ta takeyi. Ta dai bukaci ta tashi ta shiga ciki zata kawo mata abinci taci. "Na qoshi." Ta bata amsa a takaice. Ita ma Mai gadon bata ce mata uffan ba ta cigaba da harkokinta.

A bangaren Namijin zaki kuwa, basu suka dawo ba sai wajen karfe 10 na dare. Baiwar Fulani tana lura dan haka da dawowarsu tai maza taje ta sanar da uwar dakin nata. Murmushin takaici Fulani tayi domin ita bacci ma ya fara daukar ta. "Tashi kije." Ta sallami baiwar sannan ta dauko wata 'yar kwalbar turare ta sake sakin murmushi. Budewa tayi ta zata dangwala ta shafa, ko me ta tuna kuma, sai ta fasa ta rike ta gamm a hannu sannan ta nufi sashen da Namijin Zakin yake ba tare da ta bukaci rakiyar kowa ba. Ko da taje kofar sashen ne tayiwa wani bawa inkiya, kafin kace me babu sauran bawa ko daya a wajen. Karisa shiga parlorn tayi sannan ta tsaya dibi dibi dan bata san a wanne daki yake ba. Motsin da taji yo na bude kofar bandaki ne yasa ta gane dakin da yake. Murmushi ta sake yi sannan ta tsaya ta dangwali wannan turaren ta shafa a fuskarta sannan ta kama handle din dakin ta murda ta shiga. Shigarta yayi dai dai da fitowarsa daga bathroom daure da towel iya kugun sa.
Hardewa kafafunta sukai kiris ya rage ta zube a wajen tsabar rudewar da tayi. This is her first time da taga namiji a haka a ido biyu. Saboda ita ma'abociyar kallon pornography ce (blue film) kasancewar zaman da tayi a kasar turai, so bata dauki kallon porn laifi ba. To ta kasance tana son namiji mai irin kirar Usman, sai gashi yau ta ganshi ido biyu ba mafarki ba, sannan kuma shi zata aura. Wannan dadi har ina? Shi kuwa da tsananin mamakinta ya hanashi magana sai tsayawa da yayi kallonta. Sanye take da dogowar riga mai maballi sandy color ta bude maballan har kasa, hakan ya bada damar kallon kayan da ta saka a ciki. Dogon wando ne pinging jeans kalar Ja, sai wata yar ficiciyar body hug golden color. Sai ta daure kanta da jan mayafi jelar gashinta a tufke, da ta wuce kafadarta tana ta lilo a bayanta. Katse shirun tayi da cewa."arrrrmmm kayi hakuri dan Allah bansan wanka kayi bbbb,,, ammm dama godiya nazo yi mak..." Katse ta yayi a tsawace."je ki nagode, sannan ya kamata kisan ana sallama kafin a shiga wuri tunda naga de ke din kamar musulma ce ko? Ko ma dai ba muslma ma bace ya kamata kisana ana knocking." Ya fadi haka yana kokarin zama a gefen gadonsa. Kalamansa sunyi mugun dukan zuciyarta saboda tana da saurin fushi, don haka sai ta juya fuuuuu ta fita, duk wamda tsautsayi ya hada su a hanya sai ta bashi hukunci bulala 20, haka tayi ta rabon bulalai ga bayi har ta karasa sashen ta sannan ta shiga dakinta ta banko kofa tare da rufe kanta ta ciki.
Shi ko gogan naku, sai yaji wani dadi a ransa, domin ko ba komi yasan ya kunna ta, dan haka yake jin ya fara rage aikinsa cikin sauki tunda ita din mai saurin fushi ce, kuma yaga alamun bata son raini. Dan haka zaiyi amfani da wannan weakness din nata ya cusa kiyayyarsa a ranta. To bayan wayewar gari ne aka hallara a dinning hall domin a ci abinci safe. Shiru shiru babu Fulani babu labarinta. Dan haka G.Haleema ta bada umarnin aje a  ga ko lafia. A nan wata baiwar ta ta sheda mata ai tun jiya ta rufe kanta a daki kuma bata fito ba. Idan ran Gimbiya yayi dubu to ya baci. Ana ta fara sababi."mene amfanin ku gaba dayan ku? Yanzu idan wani abu ya sameta fa? Ta kare masifarta tare da raba wa duk wani bawa da yake aiki a sashen Fulani bulala 25." Sannan ta tashi ta nufi bangaren Fulanin. Sai da ta lallashe ta da kyar sannan ta tashi ta bude kofar tare da rugume Mummyn sannan ta fashe da matsanancin kuka. Rarrashin ta Mummyn tayi tare da tambayar ta me ya faru. Anan ta sheda mata komi. Ran Mummyn ba karamin baci yayi ba kuma ta dau alwashin wulakanta Namijn zaki. Sanin irin son da diyar tata take masa yasa bata gaya mata qudurinta ba. Amma ta gaya mata wasu maganganu a kunne wanda ni kaina banji me ta gaya mata ba.

Tun da suka isa dinning hall din Fulani take zuba fara'a kamar wacce akai wa bushara da Aljanna. Shi ko Namijin zaki abin har mamaki yake bashi. Ya dauka zaiga tsananin bacin rai a fuskarta amma sai yaga sabanin haka. Bayan ta gaida manyan wajen ne ta nemi waje gefen Mummynta ta zauna. Ta fara cin abincinta cikin nutsuwa kafin har kowa ya karasa. Gyaran murya Mummyn tayi sannan tayi magana cikin salon da take yiwa mai Martaba ya amince da abinda zata fada."Ranka ya dade kasan kuwa me ya hana Fulani fitowa yau."
"Sai kin fada ur majesty." Sarki Ameenullahi ya bata amsa yana mai Murmushi.  Wai fa kunyar yayan nata Usman take ji, saboda jiya fa sun dai daita."
Kamar saukar aradu haka Usman din yahi zancen.
Dariya mai martab yayi irin tasu ta manya sannan ya juya ya kalli Usman din da tsantsar mamaki ya sa shi ya kware.
"Wai haka ne Usmanu."  Kasa cewa uffan yayi karaf G.Haleema tace."Haba ranka ya dade baka ga yanayin kunyar da yake ji ba. Ai dama abinda yazo yi kenan, juma gashi Allah yayi ma sun dai daita kansu." Murna ce ta kama mai Martaba sannan ya juya ya kalli Fulani yace."fulani ya ake ciki ne."?
Da gudu ta tashi ta wuce sashen Mummyn ta. Dariya mai Martaba yayi yace ja'ira taga dan nawa ba baya ba wajen kyau..
Dariya kowa ya saka banda namiji zaki da ya tashi ya nufi hanyar sashin sa. Kansa ne ya daure ya kasa gane meye dalilin Gimbiya na yin haka?

Pheener(mrs naseer)
08060154424

Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now