part 7

493 47 1
                                    

A dayan bangaren kuwa tuni Bilkisu (mai gado) ta koma gidan mijinta, ta sheda masa abinda ya faru ya kuma bata shawarar kada ta nemi su Baffa ta sanar dasu gudun tashin hankali. Haka kuwa akai tace daga baya idan Allah ya bayyana Meeno tayi musu jawabi.
Yau ta kama ranar tafiyar su Chiroma (komawar su gida birnin pasweek) shirye shirye kam har an gaji dayin sa. Domin kuwa idan kaga mutanen Zabbit zakai tsammanin wani gagarumin taro akeyi. Domin kuwa kowa burinsa bai wuce ya kawowa chiroman Pasweek kyauta ba. Shikam Chiroma abin har mamaki yake basa yadda mutanen garin suke kaunarsa.(bahaushe kam yayi gaskia da yace halin mutum jarinsa). Kamar yadda aka tsara haka ko ya faru. Domin kuwa yar amana ma an kimtsa ta. A kuma zaman da tayi ta shaku da Gimbiya Hansa'u (uwar gidan sarki Uwais) domin ko mai martaba ne da kansa yace a bata special treatment. Hakan yayi sanadiyar zamanta a sashen Gimbiyar. Ba laifi Meeno ta kasance yarinya mai shiga ran mutane. Dan zaman da tayi na sati guda a wajen Gimbiyar tayi masifar shiga ranta. Ko dan bata da diya mace ne. Kawai tana sha'awar ina ma dan su daya tilo ya aure ta? Domin haka kurum yarinyar tayi mata. Lafia lau ce bata da matsala. Ita din ma Ameenatu ta saba da Gimbiyar domin ita ma Gimbiyar lafia lau ce. Ita ko meeno tana san mutum mai saukin kai. Gata dai ita ce Queen amma batta matsala. She's very cool. "Dama ni a barni wajenki your majesty"  Meeno ce tayi wannan maganar. "Kiyi hakuri Meenal" inji Gimbiya Hansa'u da yake Meenal take kiran ta. kinga ai ya kamata ace kinji wajen Auntyn naki, at least zata sami nutsuwa tasan an ganki, ni dinma da sona ne a bar min ke anan. But hakan bazai yiwu ba. Aikk Meeno ta turo baki gaba tace cikin muryar shagwaba "ur majesty mene bazai yiwun ba? Na zauna wajenki? Kece fa matar sarki. Sai dai idan baki niyya ba" ta fada ciki ciki. Ita ko Gimbiya tsayawa tai tana kallon ta. Ba laifi akwai tsiwa. Ta raya a ranta. Aiko kamar Aminan taji mai tace tace da ita "ba tsiwa na cika ba ur majesty, i always say my mind ne" ai ko Gimbiya ta kwashebda dariya yanayin yadda tai maganar ne ita irin bilhaqqi da gaskiar nan. Tace haka ne Meenal. Yanzu dai yadda za ayi ki je auntyn ki ta ganki. In yaso zan baki card dina idan kinje sai muna waya ko?? Idan kuma Auntyn naki ta yarda sai kina zuwar mana hutu ko baby girl.. har ga Allah Ameena taji dadin statement din (domin this is the only place da take samun nutsuwa dan bazata iya tuna san da ake kawota garden din nan na gida saukar bakin sarki ba. tun tana yarinyabake daukota a kawo ta. yau gashi zata na zuwa a ido biyu) dan haka ta yaye baki ta saki dariya har da rike ciki. Tace haka ne ranki ya dade. Yauwa kuma U supposed tk be out there waiting for Chiroma kinsan Saraki basu jira. Tabe baki tayi tace to ai ke dai kam baki da wannan girman kan ranki ya dade. Dariya Gimbiyar tayi tace to ai ni ban gaji sarauta ba. Auren sarauta nayi. Kala bata ce ba ta dauki kayyakin da Gimbiyar ta bata ta nufi hanyar fita. Da mamaki Gimbiyar tace Meenal ba sallama?? Juyowa ta danyi tace i don't want to cry ur majesty. Sai na kira din. Ta juya ta fice.
Ko da fita batai minti 2 ba chiroma ya fito. Suka gaida shi suka fara duruwa cikun buses din da suka zo dasu. Haka itama ta shiga cikin ayarin maids din ta shiga Bus daya suka dauki hanya. Fatan mu dai Allah ya sauke su lafia.

To bari mu leka fadar Maleeta mana daga nan ma sai mu jiyo labarin Baana(Maman Meeno)

Kun dai riga da kunsan yaya Birnin yake, so no need na gaya muku yadda abin yake ba. Gadan gadan masarautar na nufa domin ban taba zuwa wannan masarauta ba. Aiko nasha mamakin ganin wannan fada haka. Idan ba ku manta ba iyakar mu gidan mataimakin mai martaba mai wakiltan Kanurai. To yau de gamu gidan mai martaba. Tsayawa kwatanta muku yadda fadar ta tsaru ma bata lokaci ne. Sai dai ku ganta gata nan.  Sarkin birnin Maleeta mutum ne mai adalci kamar yadda na gaya muku baya. Sarki Ameenullahi shine sarkin wannan gari. Yana da mata 2 da  'ya daya tilo mai suna(Nawwara) wacce akw kira Fulani sai yayenta maza da yarima Kamal da yarima Saeedu(Turaki). Duk wadan nan 'ya'yan uwargida Gimbiya Haleema ne domin ita amaryar sarki Gimbiya Ameera bata taba haihuwa ba. A yadda labari yake zagayawa ma cewa ake wai uwargidan ce ta hanata haihuwa dan kuwa tana da kwantaccen ciki a jikinta. 
Tafe nake ina shawagi domin nemo muku rahoton da zai kayatar daku kawai naga wasu bayi sunata zuba uban sauri, karaf na rike rigar daya nace baiwar Allah zuwa ina haka?? Aiko ta bangajeni tace dalla malama ki barni kada ki shafa min kashin kaji. Baki gani Fulani ce ta aike ni so kike taga na dade ki ja min bala'i. Ba shiri na zabura na kade jiki na na bi bayanta don ganin wannan Fulani da ke ta labarinta.
Ina tafe ina hardewa tsabagen saurin da wannan baiwar take bugawa. Ban ankare ba naga mun nufi wani dankareren sashi a gidan sarautar. Ya ilahi, na furta a fili. Ai ko ban gama rudewa ba sai da muka bude wata royal door muka kutsa kai cikin wani makeken falo. (Ko dai batan hanya mukai nan ce fadar sarkin) aiko ido na ya sauka akan wani tafkeken zanen wata kykykyawar matashiyar budurwa.. tabarakallahu ahsanil khaliqeen. Haka na furta ina mai karewa wannan beautiful Damsel din kallo. Ita dai yarinyar nan tafi min zubi da indiyawa. Tasha ado na alfarma. Haka na dinga bin ko ina na falon ina kare masa kallo. Komai na wajen fari ne da Gold. Amma gold din ya danfi yawa. Ko ina sai sheki yake kai kace komi na wajen sabo ne. Haka na karasa har zuwa wani dan corridor inda naga wannan baiwar tabi. Ina kure wajen naga wani hadadden karamin garden. Anan na iske Fulanin tana hutawa ga kayan marmari fal gabanta. Tana nuni ana daukowa ana mika mata. Haka na kare mata kallo sai naga ma a fili tafi kyau. Tsarki ya tabbata ga mahaliccin wannan halitta. Domin har wani daukar ido takeyi tana sheki. Jana ganin yanayin skin dinta zaka tabbatarbda hutu ya zauna. Wannan itace ake son hadawa da Namijin Zaki?? Lallai sunyi matching. Masha Allah. Na fada cikin raina.
Wannan kenan..

Bayan fitowa ta daga bangaren fulani kai tsaye wani sashe na nufa da ban san ko na wane ba. Uniform din bayin wajen ma ya banbanta dana bangaren Fulanin. Ina shiga tangamemen falo idona ya sauka kan wata matsahiyar mata. Da ganin ta bazata wuce shekaru 33 ba zuwa 34. Ita din ma kykykyawar gaske ce ajin farko. Kyau iri na zallar fillo. Domin hausrta ma ba kwarai take fita ba. Tana zaune bayi suna ta hidama ana gyara mata yalwataccen gashin kanta. Komi na palorn nata Terracotta ne da beige. Masha Allahu. Da ganin ta kaga yar boko wacce boko ta ratsa. Komi na zubin yan boko ne.  Ban tsaya wata wata ba na gane Gimbiya Ameera ce baiwar Allah. Matar akwai ta saukim kai da iya mu'amala. Sai dai bata da hakuri idan ka taba ta. Wannan dalilin yasa ake mata kallon masifaffiya. domin bata iya munafurci ba. Ko wane kai ka shiga gonarta sai ta taka maka birki. Unlike Gimbiya Haleema da ta kasance mace mai kissar tsiya da zafin kishi. Amma kuma baka isa ka gane ba. Domin ko da wasa bata taba kai karar Ameeran ba. koda tasu ta hada su Ameeran takai kara ta sunje gaban mai martaba zata fara bata hakuri tana haba yar uwa duniyar ma nawa take Allah ya huci zuciyarki Gimbiya. Farat farat take ga kowa. Hakan yasa kullum mai martaba yake ganin Ameera ce mara gaskia.

To ko a 'ya'yan ma kashe mu raba akayi, domin kamal halin mai martaba yayi sak, shiko saeedu Turaki halin uwarsa yayi. Ita ko Fulani she's unpredictable. Kowa dai yasan masifaffiya ce. Amma baza kace bata da gaskia ba. Akwai Izza da takama da son mulkin tsiya ga raina na kasanta. Iyaka abinda aka sani game da ita kenan.

Wannan kenan.

Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now