part 6

685 60 1
                                    

Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.
Ina mika sakon godiya ga masoya masu bibiyan littafina na namijin zaki. Nagode kawarai Allah ya bar zumunchi ya kuma kara kauna. Na samu sakonni maras adadi na fatan alkhairi da tsumayi na. Nagode kwarai. Sannan ina so nayi amfani da wannan dama na baku hakuri bisa ji na da kukayi shiru kwana 2. Wanda har na shiga wani sabon rubutun ban karasa wannan ba. An samu tsaikon ne bisa wani personal dalili. Kuyi hakuri ayi min afuwa. Kuma in shaa Allahu yau zan dora daga inda na tsaya. Wassalamu alaikum.

Bayan Ameenatu  ta kammala shirin ta na tafiya tare da  kanwar mahaifinta ne, taje ta sami mahaifiyarta domin suyi sallama. Ta fara da cewa kiyi hakuri Ummana, na sani cewa tun farkon tasowa ta, baki kasance a cikin kwanciyar hanakali ba, kullum cikin fargabar yadda zaki tashi idan gari ya waye kike. Fargabar ki da tashin hankalinki bai wuce kai na ba. amma ki sani nima ba wai da san raina nake abinda nake ba. Kuma wata rana zaki alfahari dani. Addu'ar da kike min baza ta fadi kasa banza ba. Ta karashe maganar tana mai kukan bankwana da mahaifiyar ta ta. Ita ko Baana ko kallon inda meenan take batai ba ta cigaba da hade kayanta tunda itama komawa zatai inda ta fito.
Daga gidan Baffa zuwa gidan Auntyn Meeno tafiya ce kamar ta yada shege. Domin kuwa tafiya ce ta kwana guda da wuni 1. Haka driver ya fito dasu daga gidan Baffan ya nufi mahayar mota dasu inda suka dauki hanya. Sai muyi musu fatan Allah ya sauke su lafia.

A can kuwa birnin Zabbit chiroma ya kasance abin birgewa ga mutanen kasar. Domin kuwa kowa kaunarsa yake yi sabida kaunar na kasan sa da yake. Gashi kowa na garin karrama sa yake. Su fa yadda labari yazo musu ma cewa ake mutanen kasar pasweek ba abin da suka sani face yaki da kashe kashen mutane. Sai gashi dan sarkin gari yarima mai jiran gado for that matter yazo yana shiga cikin talakawan gari. Bayan sarkin su sarki (Uwais) ya gargade su akan su girmama yarima kuma ciroman Pasweek fiye da yadda zasu girmama shi. Gaba daya ma shi kamar ba saraki ba. Sam bashida girman kai.
Al'amarin da ya janyo masa farin jinin jama'ar garin kenan. Shi sai yake jinsa ma kamar kada ya koma paskweek, domim shi nan ma yafiye masa kwanciyar hankali. Gasu da al'adu. Kuma dai ma baza a hada su da pasweek ba ko kadan fannin cigaba. Domin kasar pasweek na daya daga cikin kasashen da suka fi kowacce kasa cigaba da kuma tarin dukiya da kayan alatu na more rayuwa. "Ashe kwanciyar hankali ma shine babbam jigon more rayuwar duniya?" Maganar da ciroma khaleel ke fada kenan a ransa bai ankara ba yaji Huzaifa (dan galadiman Zabbit) wanda ya kasance shi ke raka ciroma duk inda za ya je ya amsa da kwarai kuwa yallabai. Kwanciyar hankali yana daya daga cikin jigon jin dadin duniya. Ciroma ya numfasa yace lallai na aminta dakai, domin kuwa kasar mu ta kece nan kasar ta kowanne fanni. Amma zama na ana yasa naji kamar kada na koma. Domin gashi yanzu kusan kwana na 15 banji anyi maganar fada ko yaqi ba. Kowa hankalinsa a kwance yake. Huzaifa ya murmusa yace haka ne, domin kuwa a tarihin kasar mu mai albarka, yau kimanin shekaru 1259 da kafuwarta, sau 2 rak aka taba yaki. Shima kuma sai dai a kawo mana farmaki. Mu mutanenmu mun kasance masu son zaman lafia da kwanciyar hankali. Ciroma ya jinjina kai domin a tarihin kasar su basu taba shekara guda ba tareda sun fita yaki ko an kawo musu farmaki ba. Shidai a gaskia rayuwar kasar nan tayi mishi. Inama ana yake. Da wannan tunani yayi sallama da Huzaifa ya nufi makwancinsa.

Su kuwa matafiya sun riga sun yada  zango a wani dan karamin gari da ke karkashin sarki Uwais domin biyan bukatunsu da kuma yin salloli. Bayan tsayuwarsu ne a bakin kasuwa inda akwai masallacin matafiya da kuma bayi, Bilki ta kama hannun Meeno domin suje bangaren masallacin mata su kama ruwa suyi sallolinsu sai suci abinci. Bilkisu ta bawa Meeno jakarta tace ungo rika min in kama ruwa dan wallahi a mugun matse nake ga yunwa da take ci na, barin maza in fito sai ki shiga kinga dai minti 30 direba ya bamu. Meeno ta amsa yar jakar ta bilkisa ita kuma ta shige bayin. Bayan ta fito ta daura alwala  juyuwor da tai tace da meeno taje itama tayi ta neme ta ta rasa. Abu kamar wasa sai da ta zage kasuwar nan tas babu Ameenatu babu labarinta. Anan hankalin ta yayi kolo luwar tashi inda ta dora hannu a ka ta rusa uban kururuwa. Nan da nan aka taru kanta ana tambayar baasi. Babu musu ta zayyane musu cewar bata ga yar amana da suka tawo tare ba. Anan wasu mata suka bada shedar cewa aiko sun gansu tare kuma yanzu yanzu kamar walkiya yarinyar take tsaye anan da yar jaka amma babu ita babu labarinta yanzu. Abu kamar afi? Inji wata mata. Ita dai Bilkisa bata ce komi ba sai faman kuka take tana kiran ta banu ta lalace. Abokan tafiyarta kowa ya gama abinda yake lokacin da za sau cigaba da tafia yayi. Aka kara mata minti 30 shiru. Aka sake mata minti 40 shiru babu yar amana babu labarinta. Anan wasu daga cikin abokan tafiayar suka fara korafin gaskiya a tafi dan akwai doguwar tafia kwarai a gabansu. Haka ko akayi. Ita dai Bilkisa tace bata ga ta tafia babu yar mutane ba. Dole anan suka barta direba ya bata yan chanji domin tayi korafin yarinyar da jakarta ta bata.  Wannan kenan.

Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now