part 32

393 54 0
                                    

🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁
*NAMIJIN ZAKI*
🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁

By
_Nafisa Aliyu_
*(mrs Naseer)*

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*📚🖊️

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.
'''🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
______________________________________

Page 31

washe gari da sassafe Usman ya dau hanyar Zabbit ko sallama bai yi wa mai Martaba ba amma ya bar sallahu wajen Ummi... To Fulani ma tayi tsantsar mamaki saboda tasan tafiyar su Zahra can din. Amma da yake lallaba shi take sai bata tsawaita masa tambayoyi ba.. sai muce Allah ya sauke shi lafia.

A zaman fada da akai an tattauna wasu muhimman batutuwa ciki kuwa har da yakin da Sarki Rasheed yake so ayi da wani dan karamin gari da ke makoftaka da garinsa. Domin gari Allah ya albarkace su da man fetur. Wannan dalilin ne yasa Yau kimanin shekaru 15 kenan da sarki Rasheed ya saka musu ido. Yau kuma ya yanke shawarar yakarsu akan wasu daga cikin mutanen garin sun shigo Pasweek ba tare da izni ba saboda zalinci irin nasa.
An tattauna an gama amma babu sarkin Yaki Namijin zaki babu labarinsa. Bayan an watse daga zaman fada ne sarki je tambayar Chiroma ina dan uwan nasa.
"Ranka ya dade Amale ban san ina ya shiga ba. Yau nima ban saka shi a ido na ba. Kuma naga Amaryarsa ma wajen Suwaida ta wuni dan haka kaga baya gida." Shiru mai Martaba yayi sannna ya sallami Chiroma. Bayan zuwan Ummi ne tayi wa mai martaba bayani.. to shi abin ma mamaki ya bashi. Wannan wacece haka da ta samu matsayi a cikin ahalinsa da bai taba jin labari ba.
"Amma ita din wacece wacce sukai tafiya Zabbit ita da Zahra?? Nasan dai da tafiyar Zahra Zabbit ammma bansan ita da wata zasu tafi ba bayan bayin ta." Sarki ya gada yana mai gyara zamansa a saman gadonsa.
Anan Ummi ta kwashe labarin Meeno tun daga farko har karshe ta gaya masa saboda ranan nan ta zaunar xa Meeno ta tambayeta tarihinta tass. Shiru mai Martaba yayi. Haka kawai yarinyar bata kwanta masa ba. Amma jin Zahra ta amince da ita yasa shi yin shiru domin yasan halin autar sa Zahra da rigima. Kuma haka kawai Allah ya dora masa son Zahra autarsa kamar akan ta ya fara haihuwa.

A can Zabbit kuwa abin duniya ne ya taru yayi wa Zahra yawa. Saboda yanayin shaquwar dake tsakanin Safwan da Meeno tana iya ganin tsatsar soyayyar Meenal a idon Safwan. Amma a yadda taura ita .eenon ba wai sonshi take ba. Saboda haka ta yanke shawarar sanar da Meenal halin da take ciki saboda idan tayi wasa Meenal din na dab da fara son Yarima Safwan din..
Bayan sunyi karin kumallo ne suna zaune gaba dayansu suna hira Zahra tayi wa Meenal text message a wayarta da Yarima Safwan ya siyo mata shemaram jiya. Ta rubata mata kamr haka: 'MEENAL ina so muyi magana dake kuma naga Mami kamar ba yanzu zata sallamemu ba.'
Karantawa Meeno tayi sai ta basar na kamar minti 2 sannan ta kalli Gimbiyar tace."Bari muje masaukin mu ur highness."
Bata rai Gimbiya tayi sannan tace
"tun yanzu yarana? Nasan dai Zahrana bata son tafiya amma ke kije Meenal tunda naga kamar Zahran tafi so na."
Kwabe fuska Meenal tayi sannna tace."Allah Mami ba haka bane kawai dai zamu dan tattauna ne da yaa Zahra."
Dariya Mamin tayi sannan tace."To kafin ku tattauna bari ni mu tattauna da ke Meenal."
Tashi sukai suka nufi wani dan karamin falo ita da Mami. Kallon Meenal din tayi a nutse sannan tace."Yayanki Safwan ne yace na tayashi kawo kokon bararsa wajenki Meenal. Domin tun kafin ya ganki ya fara kaunarki dalinlin kaunarki da nakeyi."
Ji tayi gabanta yayi mugun faduwa. Ita idan tace Safwan bai mata ba tasan karya take. Ko bai mata ba ma dole ta so shi saboda shi din jinin Gimbiya ne.
"Ya naji kinyi shiru daughter?? Look, ba wanda zai miki dole. Ki fada min tsakani da Allah Safwan yayi miki."?
A guje ta tashi ta fito daga dakin tana dariya. Itama dariya Gimbiyar tayi tare da furta."Alhamdulillah."
A masaukin su ta iski Zahra. Zama tayi kan coach sanna tace."yauwa Yaa Zahra ke kuma mece taki maganar." Ta karasa zancen ds Murmushi yare da lumshe ido.
Zahra da bata kyra da yananyin Meenal din ba ta gara zance kamar haka."Meenal temako nake so ki min ni kuma na miki alkawarin yi miki duk abinda kike so a duniya."
Dafata Meeno tayi sanann tace."Yaa Zahra, go straight to the point pls. Ai yanzu cewa nake mun zama daya."
"Yarima Safwan nake so."
Dammmmmmm gaban Meeno ya fadi.
"Yau kimanin shekara 3 kenan tun farkon kaini Makaranta. Meenal ina cikin tashin hankali, na rasa Yarima Safwan wallahi haukacewa zanyi ko na mutu. Bana iya tunanin komi sai shi. Naga taku tazo daya ke dashi ki temaka ki cusa kaunata a ransa. Sai ki fada min ko me kike so idan ina da iko a duniyar nan sai miki shi."

Shiru Meeno tayi. Ta dauki mamar mintu 2 kafin tace."To Yaa Zahra."
Washe hakora Zahra tayi tare da furta"Gaya min mene kike so a duniya."

Murmushi Meeno tayi sannan tace."Ni bazan fada yanzu ba. Amma kimin alkawari duk sanda na bukata zaki min kamar yadda na miki.."
Ba tare da tunanin komi ba Zahra ta furta."Na miki alkawari Meenal. Na miki."
Dariya Meenon ta sake yi a karo na 2 sanann tace. "promise."?
"Promise." Zahra ta fada tana jin dadi.
Sanarwar zuwan yariman Pasweek ne ya gauraye masarautar ta Zabbita. Da Zahra da Meeno duk sun dauka Chiroma ne.
Da gudu Meeno ta nufi motocin da suke parking a farfajiyar masarautar tana fadin"Ya chiroma oyoyo.!"
Turus tayi ganin Usman a tsaye yana muzurai..sai bayan ya ganta ne ma ya fara tunanin shiko meye ma yasa shi tawowa?? Amma yayi wauta ma.
Kare hade fusk yayi sannan ya fada a ransa."kanwata Zahra na biyo ba wata can ba."
Zahran ce ta karaso tana fadin."Yaa Usman ashe kaine."
"Wa ya baku iznin tawowa nan."?
"Mai martaba." Ta fada tana turo baki dan tasna hali. Domin itama gwana ce a jin kai.

Bayan an masa iso ne wajen mai Martaba yake sanar dashi a hanya yake ssi yace bari ya tsaya a nan ya dan huta kwana 2 sai ya wuce. Anan aka bashi masauki mai kyau sannan suka sha hira da Yarima Safwan domin sun dan saba lokacin bikin Usman din.

Da daddare ne bayan sallar Isha ya fito ya dan ga gari ne ya hango ta Zaune ita da Yarima Safwan suna hira kamar yadda suka saba. "Amma dai Mami ta miki bayanin komi ko Meenal." Yariman ya tambaya.
"Ta yi min ya Safwan amma dan Allah kayi hakuri akwai matsala."
"Matsala fa kika ce Meenal." Yariman ya tambaya a gigice.
"Kwarai matsala. Domin a dangin mu anyi min baiko da wani." Ta karasa zancen da kikina saboda ita bata iya qarya ba.
Har ga Allah ya yarda don haka sai baiji haushin ta ba. Ta kara yi masa dadin bakin ita wallahi yayi mata 100% ina ma babu baikon wani a kanta wane ya mutu wane ya taso..
Shi sai ya fara jin tausayi ta ma.
Karkatar da ki tayi tare da cewa."Yaaa Safwan dan Allah ka min wata alfarma mana."
"Ina jin ki kanwata" ya amsa tare da kallon ta.
"Mai zai hana ka so yaa Zahra tinda naga itama tana da.."
Bai barta ta karasa ba ya katseta."dare ya fara tashi kije ki kwanta." To ta masa dan bata son ta yi masa musu.
Bayan ta tashi ta fito ne taji an jaa hannunta da karfom gaske an shigar da ita gueat room. Usman ne yake ta faman huci.
"Uban me kike a tsohon daren nan." Ya fada yana huci.
"Ban gane ba kuma." Ita ma ta fada tana kallonsa.
"So kike shima ya lalata miki rayuwa kamar yadda wannan dan iskan Turakin yayi? Me yasa bazaki kare mutunci ki a matsayinki na mace ba? Ko wannan abinda ya faru dake bai ishe ki ba?? Kinsan ke din kina attracting maza dan me zaki dinga kebewa dasu? Me yasa?? Mene yake damunki ne?? Ya ilahee.!! "
Ya karasa zancen tare da dafe kansa....

Pheener(Mrs Naseer)
08060154424

Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now