part 10

433 42 0
                                    

Ko da suka je wajen Gimbiyar ta karbe su da hannu bibbiyu. Tambaya ta fara yi mata kaman haka: ua sunanki? MEENAL, ta bada amsa kafin Chiroma ya dago da sauri ys kalleta "Meenal" ya maimata sunan a cikin ransa yana mai murmushi a fili. To bayan yan mintuna ne Gimbiya ta sa aka nunawa Meeno dakin da zata sauka.  To yau ya kasance kwanan Meeno biyu a sashen Gimbiya kuma duk kwanakin nan da tayi bata saka Chiroma ko Namijin zaki a idonta ba. Domin sau 3 kawai take zuwa gaishe da Gimbiya saboda itama Gimbiyar ba mai son karapniya bace. Duk da ba ya ganinta idan yaje wajen mahaifiyar tasa hakan bai hana sa tuna ta ba. Domin shi Allah yayi sa mutum mai tausayi. Shikam yana tausaya mata, Chiroma kenan, sarkin tausayi. Bai fiye son ya tambaye ta a wajen Ummin tasa ba, domin wani dalili da ya barwa kansa.
A kwana a tashi babu wuya wajen Allah, yau ya kama tafiyar Usman zuwa Maleeta palace. Though baya son dalilin da zai kaishi amma haka kawai yaji yana nishadin tafiyar kaman ba shine wanda baya son zuwa din nan ba.
Yaje yiwa Umminsa sallama ne ya hangeta a main parlour din Ummin tana faman goge gogen center table.
Har ya wuce yayi reverse domin ya tabbatar da abinda ya gani. Wace wannan maid din da taje da guts din zama babu uniform?? Ke! Ya fada a tsawace, juyuwa tayi a nutse ta kalleshi sannan ta sadda kanta kasa. A zatonsa ta fahimci dalilin kiranta da yayi. Domin shi a tsarinsa zaiyi wuya yayi doguwar magana da maids. Ita ko da bata gane me yake nufi ba tsayawa tayi tana wasa da duster dake hannunta. shirun da taji yayi yawa ne yasa ta dago ido ta kalleshi, hakan yayi dai dai da dagowar idonsa shima, kallon kallo suka tsaya yi, ita mamakin kyau irin na wannan mutumin takeyi, shi kuma mamaki yake yi, ita wannan me take nufi da wata kodaddiyar fuskarta, so take tace bata gane me yake nufi bane?? Kwafa yayi sannan yace da ita uban wa ya baki damar zama a palace din nan ba tare da uniform ba. Kut! Wato shi a tunaninsa ita din maid ce?? Look at how arrogant this man is. "Uban da ya baka damar shigowa mutane babu sallama, sannan kake kallon mutane ka wani kura musu ido" ta karashe maganar da mugun bugun kirji domin sai a lokacin ta lura da yanayin shigar sa. Kayana ne irin na saraki, daga sarki sai dan sarki sai wani hamshakin. Kar dai ace shima dan sarki ne?? Kifta ido tayi ta hadiyi yawun wahala. Shi ko tsananin mamaki ne ya mamaye shi. Domin a tunaninsa ba mutum ba ko aljani bai da ikon mayar masa magana a cikin palace dinsu. This is my territory, kai ko a ina a fadin duniya babu wanda ya isa ya daga masa yatsa. Lallai ba gaskiya bane, ko a mafarki wannan abin ua faru sai ya nemo ko mai kalar wannan halittar ya ci mata mutunci. Bai gasgata kansa ba sai da yaji an dafa shi. Chiroma ne, me kake yi nan tsaye tun dazu ina magana ka kura wa waje daya ido??
Dago idanunsa da sukai jajir kamar garwashin wuta yayi ya kallesa, anan Chiroma ya tabbatar da abinda yake zargi. Meenal ta saki baki a gaban wanda baya jure raini. Gyaran murya yayi sanna yace Ahhhmmm Meenal, je ki kawo min ruwan sanyi. Amsawa tayi da to duk da kirjinta bai bar faduwa ba. Wacece ita?? Namijin Zaki ya tambaya rai a dakile.. arrrmmmm Sunanta Meenal. Chiroma ya fada. Ba Sunanta nake so na sani ba?? Who is she? Where the hell is she taking her self to?? I mean yar uban waye da kuma me take taqama da?? Ajiyar mai martaba ce! Chiroma Khaleel ya fada ba tare d ya san maganar ta subuce masa ba.
Ita ko Meeno da ta samu ta kawo ruwan sum sum ta zameta wuce dakin ta. "Ajiyar mai martaba"
Usman ya sake maimaitawa. Shiko sai ya binciko wace wannan din. Kuma yayi alkawarin sai ta dandana kudar ta a hannunsa. Ko da kuwa hakan shine abu na karshe da zaiyi. Bari dai yaje ya dawo daga wannan tafiyar. Da wannan shawarar ya danji sukuni. Shi kuwa Chiroma a yau yayi alwashin sauke nauyin amanar da sarki Uwais ya dora masa. Domin ya kusa komawa birnin na Zabbit. Haka suka hadu a parlorn Gimbiya na karshe. Sukai gaidata. Usman yayi mata sallama tai masa addu'a sannan ya kama hanya. Shi kuwa  Chiroma gyara zama yayi sannan ya dubi Ummin tasa ya gaya mata qudirinsa. kai ta kada Ummin sannan tace haka ne, sauki nauyi yana da kyau dan haka sai ka tura a nemo maka Aunty n ta. Shiru yayi sannan yace to ni a girman birnin nan ma ta ina za a fara nemota?? Gashi tace ita sam bata san ma a ina take ba. Dan tace bata taba zuwa ba. Wannan mai sauki ne Khaleel, indai a birnin nan take ganinta bazai zama tashin hankali ba. Sunanta kawai Meenal din zata fada da na mijinta sai ka bada chigiyar ta. Murmushi yayi na jin dadi sannan yace what will i do without u maa?? Ita ma murmushin tayi sannan ta shafi kansa. Da haka suka ci gaba da hirarsu ta da uwa.
Ita ko maras kunhar tana daka a kulle a kudundune a cikin blanket tsoronta daya kada ya nemota. A haka har baccin wahala ya kwashe ta.

To su Usman sunyi nisa a tafiyarsu sai muce Allah ya sauke su lfia a Maleeta palace.

Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now