part 15

347 42 0
                                    

🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁
    *NAMIJIN ZAKI*
🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁

   By
_Nafisa Aliyu_
    *(mrs Naseer)*

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*📚🖊️

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.
'''🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
______________________________________

Page 15

Abin duniya ne ya taru yayi wa Usman yawa."me wannan matar take nufi dashi ne? Shifa dama yaji ana cewa bata da kyawun hali, domin kuwa shi dama haka kawai jininsu bai hadu ba. Taci darajar mai martaba." Ya fada tare da yin kwafa.
A bangaren Fulani kuwa, ji take duk wani damuwar ta ya yaye. Mahaifiyarta ta gama yi mata komi, lallai tafi kowa sa'a a duniya idan ta auri yarima Usman. Haka tayi ta murna yinin ranar har bayin ta ma sai da suka fahimci haka, domin yau babu wannan rashin mutumcin da ta saba yi musu, babu tsangwama in fact murna ma bai bari ta fahimta ko kayi mata ba dai dai ba.

Shi kuwa Usman yau wunin daki yayi domin ko lokacin lunch ma da aka aiko kiransa cewa yayi a kawo masa daki kawai. "Laaaa! ranka ya dade, ba dai wai kunya ce ta shiga tsananin ka da dan naka ba."? G.Haleema ce tayi wannan tambayar wa mai martaba tana wani kashe murya. Dariya mai Martaba yayi sannan yace."tun ranar da Usmanu yazo naga yana kokarin fara jin kunyata, banda abin Usmanu ai ni bazai taba zama suruki na ba, kamar dan da na haifa haka yake a wajena har abada." Ita dai G.Amira tunda aka fara wadan nan dramar tun daga zuwa Usman Namijin zaki masarautar nan ko uffan bata ce ba. Domin ita bata shiga abinda bai shafe ta ba.  Ita dai tana ganin rashin gaskia a lamarin amma bazata ce komi ba. Kuma ko sabgar bikin aka zo idan ba a saka ta ba bazata shiga ba.

Kamar G.Haleema ta san me Gimbiya Ameera take ayyanawa, sai cewa tayi."Your Majesty banji kince komu ba akan zancen auren 'yar taki. Ke ce fa uwar amarya, fulani ai bata da wata uwar da ta wuce ki."
"Ni fa na tsani munafurci, a gidan uwar wa Fulani take 'ya ta? Idan da gaske 'yar tawa ce me yasa bata taba takowa part dina ta gaishe ni ba? Idan har ba gaban main martaba bane kuwa ko zamu bangaji juna a hanya bazata gaida ni ba. A hakan take 'ya ta."? G.Ameera ta fada a hasale..
"Ya isa! Nace ya isa haka!" Mai martaba ya dakatar da Gimbiyar da mugun bacin rai. Ki kuma tashi ki bani waje. Tashin kuwa tayi, kuma ita ko a jikin ta domin tasan gaskia ta fada. Kuma babu wanda ya isa ya hanata fadar gaskia a duniya. Signal Gimbiya Halima ta yi wa Fulani ai a take Fulanin ta fashe da kuka tana cewa."Daddy kaga irin abin ko? Kaga me nake gaya maka, tunda nake ban taba nuna bambamci tsakanin Mami da Mummy ba. Amma kalli yadda bata dauke ni a matsayin 'ya ba. Ni wallahi Mami kamar ita ta haife ni haka na dauketa." Ta karashe zancen tana shshsheka.
"Ya isa haka my princess, it's okay. Tashi kije ki huta kada kuma ki sake bata ranki, ni nasan hukuncin da zan dauka."       Haka G.Haleema da Fulani suka tashi suka tafi ran kowa fari tasss..

Washe gari da safe ne a dining hall Usman yake shedawa mai Martaba shifa yau zai koma Pasweek. Da mamaki Gimbiya Haleema take tambaya ko lfia?
Sarki Ameenullahi ne ya katse ta da cewa."ina kece kika sheda min sun dai daita a tsakaninsu kuma sun fahimci juna? To ai bukatar maje hajji sallah. Dama abinda ya kawo shi kenan kuma lallai akwai abinda zai koma yayi ne. Tunda dai Usman idan yazo nan baya son komawa amma tunda kikaga zai koma da wuri haka to yana da uzuri."
"Haka ne Abbi, Namijin zakibya bawa sarki Ameenullahi amsa."
"To shikenan ai sai kai Turaki kasa a fara shirin tafiyar tashi ko."? Da haka aka watse a zaman karin kumallon.
Duk da Fulani bata ji dadin yadda zai tafin ba maganar arziki bata taba hada su ba amma bata tayar da hankalin ta ba, domin tasan with her mum by her side komai mai sauki ne.

_To ita ko Meeno gaba daya zaman gidan Aunty Mai Gado bai mata ba, domin ita a gaskia bata son matar nan. Gata dai qanwar mahaifinta amma gaskia bata son ta. Don ma dai tana zuwa gaishe da Ummin su Chiroma ne, kuma yanzu har shashen Chiroman tana zuwa wajen Aunty Suwaida matar yaya Chiroma. Kuma Aunty Suwaida tana sonta sosai domin jinin su yazo daya._

Pheener(mrs naseer)
08060154424

Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now