Part 34 to 50

460 40 0
                                    

🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁
    *NAMIJIN ZAKI*
🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁

   By
_Nafisa Aliyu_
    *(mrs Naseer)*

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*📚🖊️

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.
'''🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
______________________________________

Page 34 to 50

  *Assalamu alaikum masoya. Dan Allah kuyi hakuri da rashin ji na da kukai kwana 2. Ina yin typing din amma ban samu damar posting ba. Amma gashi nan na harhade muku pages da yawa. Zakuga typing din yawa to na hade pages ne. Domin na ma kusa kammala muku wannan labari. Ayi karatu lafia.*

Direct part din Aunty ta Bilkisu ta wuce. Fura ta samu tana dakawa Ummi. Tsayawa taje tayi kusa da ita tana share kwalla.
"Ke kuma lagia kika zo kika tsaya min a ka ahaka kikam kamar wacce ta hadiyi sa sanda." Aunty Bilki ta fada tana cigaba da dakan furarta.
"Ba lafia walh Aunty. Ki maida ni inda kika dauko ni kawai. Ni wajen Ammina zan koma." Ta karashe zancem da matsanancin kuka.
Shewa aunty bilki ta saka tana tafa hannaye.
"Lallai yarinyar nan naki wasa ne wlh. Ai idan kinga na maida ki wannan gidan to ki tabbatar na gama kwakwular abinda zan kwakwula a hannun mutanen gidan nan. Da yaushe na samu sukuni ko ganin Gimbiya amma yanzu dalilin ki gashi na zam babbar hadimarta har sirri take dani. Babu abinda ba ta min wanda na tambaya da wanda ban tambaya ba. Ai ko kinyi kadan kice zaki koma wajen uwarki."

Batai mamakin kalaman Auntyn ta ta ba illa iyaka daki da ta shige da gudu tana kara rizgar kuka.
"Baki gaji bane yarinya ko kukan jini , zakiyi bani maishe ki wajen uwarki. Haka kawai gashi nan daga zuwan ki har kin nutsu kin dena yawon banza, ko kin manta sanda na dauko ki nemar ki ake ana rasawa kin tafi yawan ta zubar. To bazan maida ki ki koma 'yar gidan jiya ba." Ta karashe maganar da gutun murmushin mugunta a gefen bakinta.

Ita dai Meeno tana daki abin duniya ya taru ya mata yawa. Gaba daya ta rasa ma tunanin me zata yi. Bakin cikin da kanwar babanta take kulla mata ko kuma ci mata zarafi da ya Usmanu ya so yi.
"Ban taba zatan kaima dan iska bane ya Usman. Allah sai ya saka min." Ta kara rushewa da kukan takai ci.
Sautin kukan ta ne ya sake tunzura Aunty ta ta kara balbale ta da masifa.
"Wallahi Aminatu baki isa ki tisani haba kina min kukan iskanci babu gaira babu dalili ba. Wato kin matsu ki koma wajen uwarki saboda a can kina samun daurin gindin tafiya yawon iskaci cikin dare ko?? To wallahi bazan maishe ki ba. Idan ma zaki rufe min baki gwara ki rufe min."
Usman da zuwan sa kenan sashen nasu domin ya bawa Meenal hakuri yaji auntyn ta tana surfa mata wannan masifar mutuwar tsaye yayi. Wato dama yarinyar nan ta saba bin maza. Ashe Turaki ma ba lalata mata rayuwa yayi ba dama can lalatacciyar ce. Lallai yayi ragon azanci da bai gano haka ba tun da. Wata kils ma ita takai kanta wajen turakin. Ai ko ita ce ma ta kai kan nata domin ya akai ma ta shiga daki wajen turakin.
Tsaki yaja a fili sannan ya juya ya fita. Chief guard din masarautar ya kira ya bada umarnin a fito da Turaki a kuma bashi kulawa na kwana 3 ya murmure kafin daga bisani a sallameshi.
Da yake dama ya gayawa sarkin Maleeta sarki Ameenullahi wato baban Fulani cewa ya tura Turakin kasar waje domin ymzai bude sabon company. Duk duniya babu wanda yasan Turaki na rufe sai Ummi sai kuma Chief guard din nan.
Wannan kenan.

Ko da aka sallami Turakin da ya koma masarautar su babu wanda ya ganshi a iyayen sa. Sai da ya kwana 3 ya sake murumre sannan ya bayyana kansa. A fada ya tarar da Babansa wati sarki Ameenullahi.

"Kaga mutanen kasar turai." Sarki Ameenullahi ya fada da fara'a a fuskanshi.
Shima Turakin fara'a ya kirkiro domin tsoransa kar yaje Usman ya gayawa babansa abinda ya akaikata.
"Yaya hanya ya kasar turai ya turawa. Saukar yaushe haka babu labari kuma ko Usman din bai gaya min da zuwanka ba." Sarkin ya fada yana fadada fara'ar tasa.
Jin haka yasa Turaki daukar haske dan haka ya ci gaba da bi da Sarki duk inda ya dosa. Da haka ya fahimci Usman bai sanar da aika aikar da ya tafka ba.

Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now