part 21

372 38 0
                                    

🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁
*NAMIJIN ZAKI*
🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁

By
_Nafisa Aliyu_
*(mrs Naseer)*

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*📚🖊️

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.
'''🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
______________________________________

Page 20


"Gaskia hanyar nan da nisa, ni na rasa dalilin takawa da yake hana mu hawa jirgi indai mota zata je waje. Nifa tun da nake zan iya tuna sau nawa na hau jirgi." Chiroma ne yake ta wannan sake saken a ransa. Domin shi tunda yake bai taba ganin Abbinsa zaiyi tafiya ya hau jirgin Sama ba indai mota zata je waje to duk nisan waje mota suke hawa. To shi ya kasa gane dalili. Yasan dai kudi ba matsalar su bane, wannan tafiya kamar ta yada shege. Shi yasa fa shi bai fiye son tafiya ba.
Yana cikin wannan tunanin ne ya hange ta tana ta gyangyadi a mota. Da gani duk ta galabaita. Drivern ya bawa umarnin ya tsaya. Parkin yayi a gefen titi. "Meenal, Meenal, tashi ki dawo baya sai kin fi sakewa sai ki kwanta kiya baccin." Babu musu ta bude mufin mota ta dawo baya. Shirin fita yake ya koma gaban mota yaga ta dan yamutse fuska."dan Allah kada ka barni a baya nan ni kadai kaga dai dazuzzuga muke wucewa."
Dariya taao bashi. Kannewa yayi yace da driver su tafi. Tafiya tayi tafiya har Meeno bata san sanda bacci ya kwashe ta ba. Gani yayi ta kwanto kan cinyarsa har da gyara kwanciya. Zirrrrrrrrrrrrrrrrr yaji wani abu ya tsirga masa. Dake wa yayi ya cigaba da danna wayarsa amma sai ya kasa. Gaba daya ya kasa sukuni. Dabara ce tazo masa. Drivern ya umarta da yasaks parking, bayan yayi parking ne ya nemi car pillow ya dora kanta sannan shi kuma ya koma gaba mota suka ci gaba da tafiya. Ba ita ta farka ba har sai da suka isa wani dan karamin gari. Fitsari ne ya ciwo ta shi yasa ma ta farka. Rasa ta inda zata ce masa ya tsaya tayi fitsari tayi ta kasa. "Ka tsaya anan muyi salla, naga 3 ma ta wuce." Hamdala tayi a ranta. Bayan sunyi sallah sunci abinci ne suka sake daukar hanya. Ba su tsaya ba sai da suka isa Maleeta. Iskar garin kawai ta shaka ta bude ido tana Murmushi. Chiroma dake kallonta ta glass ne yayi murumshi shima.
"Ta iya Murmushi." Ya furta a ransa. "Yaya Chiroma amma gidanmu zaka fara ajiye ni ko"? Ta katseshi daga tunanin da yake.
"Eh." Ya amsa mata a takaice. To haka suka karasa cikin garin tanai masa kwatance har suka karasa dan madaidaicin gidan nasu.
Da gudu ta shiga gidan tana kwala ihun."Ammi, Ammi kina ina."?
Ammin da ke wanka a bandaki kamar daga sama ta jiyo muryar ta. Da gudu itama ta fito daure da zani a kirjinta. "Ameenatu. Kece Ameenatu? Yaushe a gari, ina auntyn taki? Alhamdulillah."
Rungumeta tai tana kwallar farinciki. "Ammina saka ko hijab ne yaya Chiroma zai shigo ku gaisa." Ita dai bata san waye wannan ba amma haka ta shiga ciki ta sako hijabi sannan ta fito ta shimfida masa tabarma. Bayan ya shigo sun gaisa ne ko minti 5 baiyi ba ya ce zai tafi. "Bazaka tsaya ka sha ruwa ba dan nan."
"Ai da yake sauri nakeyi ne. Amma idan na dawo daukar ta zansha." Chiroma ya fada tare da mikewa tsaye. Bayan tafiyar Chiroma ne suka zauna suka sha hirar yauahe gamo. Cikin hikima Ammin ta tambayi Meeno yanzu ma tana bacewa cikin dare.
Dariya Meenon tayi sanna tace."ai tunda Aunty Suwaida ta koya min Azhkar ban sake ganin su ba. Ko zuwa kusa dani basuyi, at times sukan yi attempting zuwa kusa dani sai wani wuta yazo ya shiga tsakanin mu sai kiga duk sun gudu."
Numfasawa Ammin tayi sanna tace."to yanzu ki bani labarin su waye su din."
Dariya tayi Meenon sannan tace." Nifa Ammi wallahi tun ina 'yar yarinya suke zuwa tayani wasa, to sai bayan na fara girma ne sai suzo wai su abokaina ne, ni kuwa bana jin tsoron su. Suna zuwa ne muyi ta hira. To sanda suka fara zuwa suna dauka na ba wani nisa muke yi ba, iyakar mu Zabbit palace. wani garden muke zuwa cikin palace din mu sha fruits sannan muyi hira. A can princess din su take ita ma kuma kawata ce. Dan tace da bikinta ma nice Maid of honor." Ta karashe zancen cikin dariya.
Ta kara da cewa."kuma Ammi they promise me zasu sa kiyi alfahari da ni, basa cutar dani, ni kuma kinsan kullum so nake kiyi alfahari dani. Yanzu ma fa dan sun dena zuwa kusa dani ne yasa nake gaya miki dan sun hanani gayawa kowa."
Mamaki ne da tsoro ya kama Ammin."kar dai abinda na aikata shekara 18 ne zai dawo ya farauce ni. Innalillahi wa inna ilahi raji'un."
"Ammi wai me ne naga kin tsorata? Na gaya miki yanzu ina azhkar bazasu iya zuwa waje na ba." Ajiyar zuciya Ammin tayi sannan tace."wace kika ce ta koya miki azhkar din."?
"Aunty Suwaida." Ta bata amsa. Ammin ce ta sake tambayar."wace kuma haka."
Anan Meeno ta kwashe labarin tun farkon tafiyarsu ita da Auntynta Bilkisa ahr zuwa tawowarsu yanzu. Ajiyar zuciya Ammin ta sake yi sannan tace."maza tashi muje ki kwanta kafin Allab ya kaimu zuwa gobe da safe. A cikin masu kwangilar dafa abincin bikin Fulani Nawwara har da ni. Bazan so na makara ba. Kije ki kwanta da safe sai muyi magana. Kiyi addu'a Allah ya tashemu lfia.

Sai muce Ameen...

*Ko menene wannan abin da Ammi take tunanin ta aikata? Ku biyo ni dan jin yadda zata kaya.*

Pheener(Mrs Naseer)
08060154424


Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now