part 23

340 42 0
                                    

🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁
*NAMIJIN ZAKI*
🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁

By
_Nafisa Aliyu_
*(mrs Naseer)*

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*📚🖊️

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.
'''🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
______________________________________

Page 22

To ko a bangaren Gimbiya Ameera ta sami kulawa. Sai bayan ta dan dawo nutsuwarta ne tace da Gimbiyar tana so taje ta wajen Ammin ta.
"Wacece Ammin naki."? Gimbiyar ta tambaya da dan Murmushi a fuskarta.
"Anan garin take, Baana sunanta tana cikin wadanda aka bawa kwangilar abinci daurin aure."
"Baaana, Baana! Ni kuwa ina na taba jin sunan nan."? Gimbiya ce tayi maganar nan kaman mai tuna wani abu.
Shiru ita ma Meeno tayi saboda bata san me zata ce ba.
"Kuma bata da hadi da gidan sarauta."? Gimbiya ta sake hefo mata wata tambayar.
"Kwarai ranki ya dade bata da hadi... Sai dai kuma shugaba mai wakiltan Barebari yaya ne a wajenta." Inji Meeno
Gimbiya ce tace."Ko da naji, ai amaryarsa Falmata tare mukai Secondary school da ita. To da yake har yanzu muna zumunchi da ita to a bakin ta nake yawan jin Baana. Domin ita ce ma tace min tana son wajen mutun daya a masu a abincin biki. Ashe Ammin ki ce."
"Eh." Meeno ta gajarce zancen.
Shiru ne ya sake ratsawa na kamar minti 10 sannan Meeeno ta yunkura tana yiwa Gimbiya Ameera sallama.
"Ban san sunan 'yar tawa ba." Inji Gimbiya.
"Ameena amma ana kira na da Meenal." Meeno ta fada tana washe hakora.
Bayan Meeno ta fito direct kitchen ta nufa. Ta tarar da Ammin nata har sun kammala gaba dayan aikinsu.
"Ina kika dade haka Ameenatu? Daga mika abinci sau 1 shine haka baki dawo ba sai da aka gama serving. Allah dai ya shirya ki."
Uffan bata ce da Ammin nata ba ta dauki jakar kayanda Ammin ta ta chanja suka nufi hanyar fita a masarautar. Bayan sun koma gida ne ta fara tariyo abinda ya faru tsakaninsu. A gaskia Wanann kanin Yaya Chiroman ya fiye mugunta.
"Allah ya isa tsakani na da kai mugu azzalumi mai siffar aljanu." Ta karashe zance da dariya mai sauti.
Bayan ta gama yan gyare gyaren daki ne ta fito ta nufi wajen Ammin ta suka cigaba da hira.

To a bangaren Fulani Nawwara kuwa tun tana jiran Angonta yazo har ta sare. Kuka kam tayi shi har ta gaji. gashi Mummyn ta tana da baqi da yawa da taje ta sanar mata halin da take ciki. "Kada ki batawa kanki rai Fulani yau ranar farincikin ki ce. Kuma kin san dai yadda wannan bawan Allah yake qaunarki tunda har shi ya yanke shawarar auren ku a qurarren lokaci.." haka tayi ta rarrashin kanta har zuwa sanda ta dan huce domin friends dinta sun fara taruwa.

Shi kuwa Namijin zaki tunda ya koma masaukinsa abin duniya ya taru ya masa yawa. Ya ma rasa me zaiyi. Bathroom ya nufa ya saki shower a kansa duk dan ya dan sami sauki.
Kamar ma kara masa damuwa ruwan yake yi. Gaba daya ya gama susucewa. Ya rasa me yake masa dadi. Bai taba tsintar kansa a irin wanann yanayin ba. "Ya Salam." Ya furata yana kaiwa kofar bayin duka da kafa.
Daga kafar bayin yaji ana masa magana."chill man, ni kaina haushin yarinyar nake ji. Ka fito mu tattauna me zanyi mata mu huce." Turaki ne yayi wannan magana.
A gaggauce ko ya fito, yana fitowa ya samu guri gefen Turakin ya zauna tare da furta."ina jinka." Shiru Turakin yayi tare da cewa."wacece ita."?
"Ajiyar Abbina ce." Namijin zaki ya amsa a hasale saboda ya fara gajiya da magana da Turaki. "Ranka ya dade ka bani ikon hukunta ta da hannuna idan munje Palace dinku." Turaki ya fada yana satar kallon Usman din ta gefen ido.
"Na baka my prince." Usman din ya fada tare da tashi tsaye. Sanna ya dora da cewa."ta dade tana shigar min hanci da kundundune ban samu damar hukunta ta. Anytime i tried sai nayi failing ko dai yaya Chiroma ya hananu ko ta gudu. Ina so ka hukunta min ita."
"An gama ranka ya dade." Cewar Turaki yana mai Murmushin mugunta. Daga nan ya tashi ya fita.
Shiko Usman a daki ya wuni bai fito ba har washegari.

Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now