part 22

365 41 0
                                    

🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁
    *NAMIJIN ZAKI*
🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁

   By
_Nafisa Aliyu_
    *(mrs Naseer)*

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*📚🖊️

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.
'''🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
______________________________________

Page 21

*Wannan page din gaba dayan sa sadaukarwa ne gareki 'yar uwa Fareeda ('Yar mutan Niger)♥ Allah ya bar qauna. Mun gode da cover page.*

Washegari akayi daurin auren Usman da Fulani Nawwara. Su Ammi sun fita tun asubar fari domin tafiya wajen Girkin abinci daurin aure. Sanda zata tafi Meeno bata ma tashi a bacci ba. Saboda haka sai ta bar mata note a gefen pillow dinta cewa idan ta tashi tayi breakfast ita tafi wajen aiki.
Ko da ta tashi ta karanta note a gaggauce ta dafa ruwan shayi ta hada da Fanke(Puff puff) din da Ammin ta soya ta sha. Tana gamawa ta fada bayi tayo wanka sannan tazo ta shirya. Duk gaggawan nan da take so take taje ta riski Ammin a gidan sarautar, domin tun tasowarta bata taba shiga gidan sarkin ba. Saboda haka yau ta sami damar shiga ita ma ta kashe kwarkwatar idon ta.

Da yake yau babban taro ake a masarautar yasa ba a wani tsaurara tsaro. Hakan ya bata damar kutsa kanta ciki, to bata taba ziwa ba, don haka bata ma san ina zata ga Ammin nata ba. "Ni ba waya ba bare n kirata naji ta wajen ina take, gashi kowa harkar gabansa yake ni bansan ma ya zanyi ba. Mchwww...." Ta ja dogon tsaki tare da nufar wani building da ta hango. "Maybe anan kitchen din yake." Ta fada tana kara sauri domin jiyo muryayoyin mata da tayi yana tasowa daga windown bayan building din. Tana karasawa ta kutsa kanta cikin dan karamin gate din wajen, ganin bata kowa a compund din ba yasa ta yanke shawarar shiga ciki. Karaf taji an chafko hannunta anyi wani dan corridor da ita.  Ihu ta daddage ta kwala tare ta tattaro duk wani karfi da Allah ya bata ta hankade wannan mutumin.
Sa'eedu Turaki na gani a kasa yana kokarin tashi.
"Waye kai."? Ta fada a dake tana kara tamke fuska.
Dariya ce ta kamashi, sai da yayi mai isar sa sannan yace."Relax baby, i mean no harm. Sunana Saeed Turaki, nasan in dai ke din 'yar nan haka ce to kin sanni, idan kuma bakuwa ce to nine 2nd born din sarkin nan...." Bata bari ya karisa ba ta dauke ahi da mari. "Kai wani irin wawa dakiki ne? Tsabar jakanta baka sanni ba bakai komi ba zaka kama hannuna ka janyo ni lungun nan. Inma uban me."?
Mamaki tai mugun bashi hadi da tsoro. Kar yaje 'yar wani sarkin ce itama ko kawar Fulani ce. gyaran murya yayi."Arrrmmmm kiyi hakuri yan mata kamar yadda na gaya miki i mean no harm. Zaki iya tafia." Ya fada tare da juyawa ya koma zuciyarsa na tafrfasa.

Ita din ma juyawar tayi ta fice tana kunkuni. A hanya ta hadu da wata maid ta tambayeta madafa ita kuma tayi directing dinta. Anan taje ta tarar da Ammin nata. Ta dan kama mata aiki..

Ango Namijin zaki na hango tafe da shi da abokansa sun dawo daga Fada, da alama kwasar gaisuwa suka je..  A cikin abokan nasa na hango Turaki suna magana da Chiroma Khaleel. Kamar ance ya kalli hanyar Madafa. Ganinta yayi ta tawo da tray a hannunta, da alama abinci zata kaiwa wasu bakin.
"Meenal." Chiroman ya kwalla mata kiran. Jin an kirata ne yasa ta dagowa, da sauri ta tawo tana. "Yaya Chiroma ashe kaine."
Ita sam ma bata lura da wasu mazan a gabanta ba. Ita dai tasan ta jiyo muryar Chiroma kuma ta ganshi. Aiko karasawar da zatayi ne da saurin ta sukai karo da Namijin zaki. Hakan yayi sanadiyar kwarewar miyar ajikin farar sabuwar shaddar sa, babbar riga ce taji ubansu aiki.
"Nasan dama ke kadai zaki iya aikata haka. Enemy of progress." Usman ya fada cikin zafin rai.
"Kayi hakuri wallahi ban san.." kafin ta kaisa ya kife ta da mari har sai da taga taurari suna wulgawa. Sanann yace."kafin na bude ido na bana son ganin wani stain ko daya jikin kayana, kisa harshen ki ki lashe tasss ya fita kamar kin wanke da omo da bleach."
Tsabar gigita bata san sanda ta kamo hannunsa ta fara lashewa ba, domin akwai miyar ma jikin hannunsa. Wani irin shocking yaji kamar wanda wutar lantarki ta ja shi. Tun daga kwakwalwarsa har zuwa tafin kafarsa. Ita ko bata fasa lashewa ba. Bata ma san me take yi ba tsabar zafin Marin da taji. Gaba daya ya sha'afa ya shagala da kallonta da kuma wata irin duniya da ya fada.
Fincike hannun da Chiroma yayi ne yasa shi dawowa daga duniyar tunanin da ya afka.
"Kayi hauka ne Usman? Wannan yarinyar zakayi wa wanann marin? Da ka kashe ta fa."? Gaba daya bashi da laka a jikin sa. Kawai wucewa yayi ya shige masaukinsa. Hannunta Chiroman ya kama yana bata hakuri sanann shima ya wuce da ita side din Gimbiya Ameera, domin shi Chiroma Allah ya hada jininsu. Kuma matar sa Suwaida yar uwar ta ce.

Pheener(Mrs Naseer)
08060154425



Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now