chapter 1-5

100 7 2
                                    

💮💮💮💮💮💮
FAYROZ
💮💮💮💮💮💮

MALAKAR
ASMA'U NANA (NASMERH)💕💕
AND
FATIMA USMAN BAUCHI

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*
**********
PAGE 1-5
Wow 😲 Masu karatu tunda farko zan so ku ga irin kyau na FAYROZ , kwance take Akan Wani gado , gadonta royal bed ne , FAYROZ kyakkyawa ce ajin farko, lkcn da muka ganta na tsorata sosai saboda kyanta ya wuce tunanin me tunani , bana tunanin yar Naija ce ita .

Lullube take cikin bargo , fuskarta ta bayyana yadda kowa zai iya gani , gashin kanta ya kwanta sosai , hancin ta dogo ne , barci takeyi hankalinta kwance , duk Wanda ya ganta yasan dukiya ke magana ajikin ta , iya kyau da haduwa ta hadu , gashin idonta zara-zara ne .

Bude dakin akayi aka shigo wata tsohuwa nagani da akalla shekarunta zasuyi 80 aduniya , sanda take dogarawa , da Alama mahaifiyar FAYROZ ce , sbd naga farin fatar su iri daya ne , sannan kuma tsayin hancin su iri daya ne Banbanci kawae FAYROZ ta fita wannan tsohuwar kyau so dubu .

Bubbuga ta takeyi ahankali ;"astaiƙaz FAYROZ, Daena nadhhab litanawul al'iftar" (ki tashi FAYROZ muje muci Abinci), Bude idon ta take yi, Masha Allah, yanzu na ƙara tabbatar wa ido na ɗaya daga cikin siffar kyau , duk da barci ta tashi amma idon ta masu kyau ne, dadaran ido gareta, masu kamar ruwa sun kwanta a cikin.

"ya ummi Daeni, 'aghsal 'asnani, wa'akhadh himami "(Bari na wanke baki na, sannan nayi wanka) ta fada cikin murya ta mai sanyi da dadin ji.

NASAN MASU KARATU ZAKU CE WANE YARECE ITA.
TO LABARIN MU A KASAR LARABAWA YA KAI MU.

Tashi Ummi tayi wato mahaifiyarta, Fita tayi zuwa parlor domin jiran yar lelen ta.

Wanka FAYROZ tayi sannan tashirya cikin wata doguwar riga abaya Black, kwalli ta shafa, gyalen rigar tayi Rolling , Masha Allah tayi kyau sosai.

Parlor tazo ta same Ummi Abinci suka ci sannan ta tashi dan tayi latti fita gurin aiki, Kiss tayiwa Umminta agoshi sannan ta wuce, ni mamaki na shine yadda suke rayuwar su su biyu kawai sai ma'aikata acikin tafkeken gida haka.

SAUDI BASIC INDUSTRY Naga an rubuta a gaban wata haddadiyar ma'aikata

Wanan ma'aikatar na daya daga cikin manyan ma'aikatar da Saudi Arabia ke ji da ita.

Shiga tayi cikin takun ta na isa, gaisawa take yi da mutanen gurin, a gurguje saboda Mai company din yana da matukar tsanani.

Gaban office din ta ta tsaya wani kati naga ta nuna gaban kofar, budewa kofar tayi, sannan ta shiga, ta fara aiki a gaggauce kasancewar akwai wasu baya mai da ma'aikatar ke bukatar ta tura, kafin su shiga meeting.

**********************

Wani kyakkyawan saurayi gani, da aƙalla zai yi shekara 35 a duniya, sanye yake cikin wasu kaya masu na alfarma, tsadaddar suit ce cikin shi, kayan sun amshi jikin shi. ( ohh readers I have never seen someone as handsome as that man).
Tafiya yake yi ba alamar murmushi a fuskantar shi, sai take mishi baya ake yi.

Sai gaida shi ake yi amma ko a jikin sa.

JAHMEEL kenan the owner of Saudi basic industries.

JAHMEEL namiji ne jarumi , hamshaƙin me kudi, mutum ne da baya son mutane kusa dashi, haka ne yasa ko aure beyi ba, haka zalika ma bai taɓa soyayya ba.

Mutanen ma'aikatar sai gaisuwa suke kwasa amma ko kallon su beyi, masu take mishi baya ke daga wa Alamun ya amsa gaisuwa. Bakarya JAHMEEL akwai izza da isa.
A duniya idan ba ƙanwar shi AIDAH ba, ba wadda yake magana da ita sosai, itama aida din kafin taga dariyar wani aiki ne.

Shiga yayi conference hall din da ake meeting.
Yana shiga aka kulle, dama shi yake shiga, daga can kan kujera na hango FAYROZ zaune akan kujera.

Meeting aka Fara, bayanan da aka tattara, JAHMEEL ya fara duba, watsi yayi da ita, dagowa yayi da idon shi ya dako da suka canza kala suka koma kallar jaaa, FAYROZ yake bi da wani mugun kallo, ita kam ta tsorata sosai.
"waye ya hada bayanannan ya tambaya". cikin muryarta me sanyi tace "Ni ce yallaɓai ". Wani wawan mari ya sauke mata tassssss kake ji ko ina nagurin ya dauki kara "ke wace irin dabba ce ya za'ayi ki maimaita bayanai"

Idon ta da suka ciko da hawaye ta saukar ƙasa, sai yanzu ta lura da takardun da ta kawo, gurin sauri ta dauko waɗannan takardun.

" 'ana 'asaf "(yi hakuri) ta fada tana share hawayen da suka zubo mata, wannan shi ne karo na faro da aka mareta, Ummi bata taba marin ta ba ko da wasa. " 'ahkraj min hadhihih alqaea" (fita daga cikin hall din nan) JAHMEEL ya fada a tsawace.

Fita tayi daga ciki, tana tafiya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki.

Yinin ranar gaba daya FAYROZ bata sake ba, Sai miya sa JAHMEEL ko yaushe yake jiran ta ne, duk tayi laifi sai ya tabbata ya wulakanta ta.

Yau bata ma dauki lkc a gurin aiki, around 5:40 ta bar ma'aikatar, Saboda yau sun aje zasu fita ita da kawarta NAASHEETA.

............

NAASHEETA yar sarki Saudi Arabia ce, ita ce babba kawar FAYROZ tun da ta fara aiki a basic industry Na JAHMEEL.

..........
FAYROZ da NAASHEETA ne suka fita zuwa wani city center mall, acikin gurin akwai abubuwa da dama.
Cinema suka shiga suka kalli best movie din su, Daga gefen su kuma pop corn ne.

Suna gurin DALEEL ya kira NAASHEETA, "Hello ahki " (hello Dan uwa)" NAASHEETA ta fada tana magana da yayanta, "NAASHEETA kina ina ", "Ina city center mall, me ya faru", murmushi yayi sannan yace "dafatan kina tare da FAYROZ ". "eh muna tare ko zaka zo", "Eh dole kinsan ƙawarki akwai mutuncin". "Hmmmmm DALEEL fada min gaskiya anya ba son FAYROZ kake yi ba", kashe wayar yayi yana murmushi, Allah ya sani yana son FAYROZ, Amma baya tunanin zata so shi.

Harara FAYROZ ta bita da shi, "kin cika mutane da surutu sai kace masaurauta". NAASHEETA tace " fada min gaskiya ke dai, kinji dadi ne Saboda DALEEL zai zo, ai ni na Dade da halbo jirgin ku ". Banza FAYROZ tai mata, sbd burin NAASHEETA ne ayi musu.

Cikin 30 minutes DALEEL ya shiga ciki, ya sani sarai ba zasu wuce cenima ba, shiga yayi acan ya hango su, labari suke yi suna dariya. Gaban su ya tsaya, a firgice FAYROZ ta dago,NAASHEETA tace "kace dama kana kusa ", murmushi yayi da sai da ya bayyana hakoransa;"eh Wlh ina kusa dama". Gaida shi FAYROZ tayi, zuwa yayi ya zauna kusa da ita, sai suka saka ta tsakiya shida NAASHEETA.
"Hello beautiful " ya fada...........

Sai ku ji mu a next chapter.

Vote.
Like.
And comments.

HADIN GUIWAR
QUEEN NASMEH &, FATEEY USMAN 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂.

ALQALMI YAFI TAKOBI✍️🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


FAYROZ❤️❤️Where stories live. Discover now