Chapter 71-75

27 4 0
                                    

💮💮💮💮💮💮
FAYROZ
💮💮💮💮💮💮




✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Page 71-75

******************

Shige da ficen da akeyi ne agidan su JAHMEEL, mutane sunyi yawa da alamu anyi gayya da yawa, yau ake Arabian night ɗin Aidah da Mahboob,, cikin gidan na shiga, kai tsaye ɗakin Aidah na wuce, murmushi takeyi sai sheƙi takeyi irin na amare, da alama ta ji gyaran jiki, wata mata naga ta shigo ɗakin, ɗauke take wata rubo sai ƙamshi ke tashi da alamu ruwan da amarya ke wanka ne da su, "Aidah ki tashi kiyi wanka wuri na ƙurewa, dangin ango na hanyar su ta zuwa" faɗar matar.

Toilet ta shiga, cikin ruwan ta shiga a bathtub tajima a haka, sannan ta canza ruwan wanka, wanke jikin ta, zuwa tayi aka shirya ta cikin wata Arabian gown gown black sai sheƙi takeyi tayi matuƙar yin kyau masha.

Mahboob ne ya shigo sanye da wata riga iya guiwa white sai wando black yayi matuƙar yin kyau masha.

Tafiya yakeyi cikin takunshi na ƙasaita har iso gareta tana tsaye a madubi tana kallon kanta, "wow masha my wife is looking beautiful ".
JAHMEEL ne da shigowarsa kenan yace "masha Allah karka cinye min ƙanwa", da wani mugun kallo Mahboob yabishi "ni fa bana son shisshigi, nida matana amma ana damuna "Mahboob ya faɗa yana riƙe dariyarshi, JAHMEEL yace " ashe da rabon na hana auren nan", Aidah da tasan halin yayanta, tasan ba ƙaramin aikin shi bane yace abar ɗaura auren sai nan da sati ɗaya, ita kuwa iskan da ke janta ba abunda take buri irin ta ganta aɗakin ta, dan haka tayi saurin cewa " haba habeebty yayan nawa "ta ƙara sa maganar tana kashe wa Mahboob ido, JAHMEEL kuwa da ya riga ya halbo jirgin ƙanwar tashi yace "kya de ji dashi, ƴar soyayyar yarda bance ba", dariya Mahboob yayi yace muje mubata wuri za'a zo da ita parlor, JAHMEEL yace "wa zai jira ta, yanzu zata bimu mu wuce, dama na shigo ɗakin ne dan ta zo mu je", murmushi Aidah tayi sannan suka fita.

Hannun ta cikin na JAHMEEL, wai ita me yaya,a parlor suka sami dangin ango sannan suka shiga cikin mota zuwa hall ɗin da aka kama domin taron, Mahboob motar shi daban, Aidah ma haka.

Da isar su gurin aka fito da amarya, ango ma ya fito suka shiga gurin.

Madhs Allah taro yayi taro an watse lafiya, gobe za'a ɗaura aure💃💃💃💃💃💃💃💃💃.

**********
NAASHEETA

Kwana biyu mamaki ya cika ta, tunanin inda FAYROZ ta shiga takeyi, gashi yanzu ta dawo aiki amma bataga FAYROZ ba, saboda haka ta yanke hukuncin zuwa gidan su yau.

Bayan ta bar gurin aiki, kai tsaye gidan su FAYROZ ta wuce, nan Ummie ke sheda mata FAYROZ tana gurin mahaifinta Nigeria, NAASHEETA bata ji daɗin hakan ba, amma ba yadda ta iya.

Gida ta wuce.

**********

Ummie kuwa kewar ƴarta takeyi, damuwa duk ta kamata, tana so ta koma wa Jaalal amma kuma bata san da wane ido zata kalle shi ta bashi haƙuri ba.

***********

Yau aka ɗaura auren Mahboob Munir & Aidah Lateef, akan sadaki mafi girma.

Mahboob kuwa ya kasa rufe baki saboda murna, he can't explain how he's feeling, he is over excited (ya kasa misalta yadda yake ji, farinciki ya mishi yawa).

Aidah kuwa tunda akace an ɗaura take farinciki amma a ɗayan gefen kuma tana jin ba daɗi,ita bata ma san su waye iyayenta ba, JAHMEEL ne kawai mamanta, kuma shine babanta, gashi yau zata barshi, bata san lokacin da hawaye suka zubo mata ba, ji tayi an miƙa mata handkerchief, ɗagowa tayi taga ashe yayanta ne JAHMEEL, rungume shi tayi tana kuka, be hanata kuka, haka ya Barta tayi me isarta.

Bayan tayi kuka me know isarta ne ya ɗago ta ya zaunar da ita gefen gadon ta, idon shi da suka canza launi zuwa ja ya zuba mata, yayi 5 minutes yana kallon ta, kafin ya danne zuciyar shi yace "Aidah this is a new life u are starting (wannan sabuwar rayuwa ce da zaki fara), kar ki yi wasa da damar ki, kiyi wa mijinki biyayya dai-dai gwargwado sannan ki kyautata masa, nasa ƙarin bayani kawai nakeyi amma kin san duk wannan, ina miki fatan alkhairi ki tashi yanzu kibi dangin mijinki, zan turo wata daga cikin su ta fito dake sai ki wuce ", be bari yaji me zata faɗa ba ya fice daga ɗakin.

Kamar yace Aidah ta cigaba inda ta tsaya, ai kuwa tasa kuka kamar ranta zai fita, yanzu sai take ji kamar kar ta bar gidan.

Wata tsohuwa ta shigo ɗakin kama hanunta matar tayi suka fito , nan aka saka ta a motar da Mahboob yake, tana kallon JAHMEEL ta waje yana tsaye yasaka hannun shi a aljihu ya duƙar da kai, ɗago kan da zai yi, ya ganta tana ɗaga mai hannu, juya wa yayi saboda bazai iya ganin tafiyar su ba.

NI KUWA QUEEN NASMERH NACE AIDAH YAU ANBAR AKHI 😂😂😂😂.

MU HAƊU ANEXT CHAPTER DAN JIN RAYUWAR DA JAHMEEL ZAIYI DA ALAMU YA FARA MISSING AIDAH.

DA KUMA RAYUWAR FAYROZ.

TSARA LABARI BY:QUEEN NASMERH.

ALQALAMIN MU NE.
QUEEN NASMERH & MOM MUSAYYID.

LOVE U ALL MY READERS ❤️❤️❤️❤️❤️❤️.

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️💞💞💞💞💞💞💞💞💞

FAYROZ❤️❤️Where stories live. Discover now