Chapter 61-65

29 3 0
                                    

💮💮💮💮💮💮
FAYROZ
💮💮💮💮💮💮




✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*******

Page 61-65

******************

Wanka FAYROZ tayi ta shirya tana jiran Abbu, sanye take da riga doguwa fara mai duwatsu blue, masha Allah FAYROZ kyakkyawa ce sosai, parlor ta dawo ta zauna, ko minti biyu batayi da zama ba, Abbu ya shigo parlor, da murmushi ɗauke a fuskar shi har yazo ya zauna, saukowa tayi daga kan kujera ta zauna kusa da shi kanta acinyar shi tace "ina kwana Abbu", "lafiya ƙalau Love ya kwanan Nigeria", "alhamdulillah "ta faɗa a taƙaice, abinci aka kawo musu suka ci sannan ya gyara zama yace "FAYROZ yanzu zaki ji asalin labarina".

TUSHEN LABARI
His excellency Jaalal Janyau, ɗan ƙaramar hukumar Demsa ne acikin jahar Adamawa, shi ɗin ɗa ne agurin Alhaji Musa, rayuwar shi ta taso ne cikin jin daɗi da walwala, sannan shine mafi soyuwa agurin iyeyen shi, su huɗu ne agurin iyeyen shi, Junaid shine ɗa na farko agurin Alhaji Musa, sannan Jamal sai Jaalal, da kuma ƴar autar mata Jaseena, Jamal da Jaseena ƴan ɗaki ɗaya ne sunan mahaifiyar su Falmata, sai kuma Junaid da Jaalal Mahaifiyar su ta rasu tun gurin haihuwa Jaala, Fiddausi macece mai haƙuri da kawai ci(wato mahaifiyar su Junaid) , agidan bata da walwala, tun da ta haifi Junaid take fuskantar baƙinciki kala-kala agurin kishiyar ta Falmata, wanda aka haɗa auren Falmata da Alhaji Musa bayan auren su da wata biyu, haka yasa haihuwar su ta farƙo suka yi tare, Falmata ƴar uwar Alhaji Musa ce tare suka tashi, saboda haka ne ta nace sai ta aure shi, wanda shi baya sonta amma bayan anyi auren shi da Fiddausi ne mahaifinshi ya haɗa shi da ita ba yadda ya iya dole ya haƙura ya karɓi auren.

Falmata bata son Fiddausi, kuma da suka haihu ba ƙaramin haushi Falmata taji ba saboda ko kaɗan bata so aka Fiddausi ta haifi na miji ba, ba abunda yafi damun Fiddausi irin yadda suka gurɓata tunanin Junaid yazama mai baƙin hali kamar Jamal.

Tunda daga lokacin basu sake haihuwa ba har akayi shekara biyar sannan Fiddausi ta samu ciki, nan ta dinga fuskantar tsangwama gurin Falmata cikin ikon Allah ta haifi ɗan ta Jaalal, wanda agurin ta riga mu gidan gaskiya, Junaid yayi ƙarami ya fahimci ciwon rashin uwa amma duk da haka yayi kuka saboda angaya mishi bazata sake dawowa ba 😭😭😭.

Jamal yace mishi "Ummanka ta mutune saboda jaririn da ta haifa kaga be kamata ka so shi ba ", ai kuwa haka akayi tsana sosai ta shiga tsakanin shi da Jaalal, shi kuwa Jaalal ba abun da ya dame shi, akwai far'a da mutunci , gurin mahaifin shi kawai yake zuwa yaji daɗi shi kuma Alhaji Musa ya ɗauƙi son duniya ya ɗaurawa Jaalal, kullum sai ya mishi wannan furucin "kaine asalin jinina kuma Kaine magaji na da yardar Allah "haka da yake yi yana matuƙar konawa Falmata rai.

Bayan an haifi Jaalal da shekara bakwai Falmata ta haifi ɗiya mace, wanda tayi na damar haihuwar dan acewar ta da ta haifi mace gara tayi asarar duniya da ta lahira.

Jaseena da Jaalal suka haɗa kansu, Jaalal yake kula da ita, yana son ƙanwar shi baya so wani abu ya same ta.

Junaid yafara hankali dan yanzu shekarar shi 13 a duniya, saboda haka ya daina muzguna wa ƙanin shi, saboda haka ne Jamal da mahaifiyar shi suka ɗauki Junaid suka jefa a rijiya, Jaalal yayi iya ƙoƙarinshi na ganin ya cece rayuwar ɗan uwansa amma abun yaci tura, ko kafin aciro shi, ya riga mu gidan gaskiya, Jaalal yayi kuka kamar zai rasa ranshi, Jaseena ke aikin lallashi, saki uku Alhaji ya mata, hannun Jamal taja tace "tafi nono fari, zo muje ɗana "kwace hannun shi yayi yace " ni ba inda zani, ina gidan mahaifina", cikin suɓutar baki tace "dallah can waya ce maka Musa ne ubanka, Jaseena kawai ce ƴar shi", saurin rufe baki tayi dan bata so asirinta ya tonu ba, tsare ta Alhaji Musa yayi yace "sai kin faɗa min gaskiya ", shiru tayi kafin ta buɗe baki tace "bayan kayi aure naji na tsane ka haka yasa naje nafara soyayya, amma cikin rashin sa'a sani ya cuce ni yamin ciki ya gudu, haka nazo na faɗawa mama shine aka bani magani cikin ya kwanta sai da na aure ka sannan ya tashi na haihu.

Jamal yayi kuka sosai, amma ba yadda ya iya dole ya bita su wuce.
NI ASMA'U NACE AGOLA SAI A BAR WA SU JAALAL GIDA 😂😐BAMU ZAMA DA SHEGE

Baya shekara huɗu, lokacin Jaalal yana da shekara 11,ita kuma Jaseena tana da shekara 5, Alhaji Musa ya ɗauƙe su zuwa Saudi Arabia, wanda wani aiki ya kai su can.

MASU KARATU KUYI HAƘURI DA ƘARANCIN CHAPTER.

I LOVE U ALL
SADAUKARWA GARE KU MY READERS.

TSARA LABARI :QUEEN NASMERH

RUBUTAWA.
QUEEN NASMERH AND MOM MUSAYYID.

KAMAR YADDA NA FAƊA MUKU MOM MUSAYYID ZATA RIƘA TAYA NI TYPING, KASANCEWAR FATY USMAN NA KARATU BAZATA SAMU TAYA NI BA.

MU HAƊU A NEXT CHAPTER DAN JIN CIGABAN LABARIN.

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️🖋️💕💕💕💞💞💞💞💞💞

FAYROZ❤️❤️Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz