Chapter 226-300

25 3 0
                                    

💮💮💮💮💮💮
                     FAYROZ
              💮💮💮💮💮💮

Tsara labari da rubutuwa :Queen Nasmerh
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

_INA MA’ABOTA KARATUN LITTATTAFAN HAUSA? WANDA ZAI NISHADANTAR DAKU, YA FADAKAR, YA KUMA TSUNDUMA KU A KOGIN LOBAYYAR KAUNA? TO KU MATSO KUSA... DOMIN MUNZO MUKU DA ALBISHIR DIN WANI GANGARIYAR LITTAFI.. DAYA NE TAMKAR DA DUBU.. YAZO DA WANI SALO NA DABAN WANDA ZAI SANYAYA ZUKATAH.._

_LITTAFIN *UNCLE NE...* LITTAFI NE FIRST OF ITS KIND, DA YAZO A WANNAN SHEKARA TA 2021. AN BAJE KOLIN BASIRA A BOOK DIN UNCLE NE.._

_”Wait... Queen nasmerh, Kina nufin NIMCYLUV, dai shararriyar murubuciyar nan itace tazo da wani salon rubutun..?..”_

_”Kede bari Heroine Tsaya kiji kanun labarin a tak’aice..*NIMCYLUV* Tace book din a ta’kaice labarin *UNCLE NE* ne yana tafe:_

_Da farko yana mata kallon uwa wacce ta haife shi kuma jigon rayuwarsa, ashe itace silar rushewar rayuwarsa😢yarinyar da yakewa kallon ƙanwa uwa ɗaya Uba ɗaya ita aka wayi gari ta zama MATAR SA🙆🏻‍♀️ ƙaddara ta haɗashi da (Ahlil kitab) kiristan ya bata farin ciki, kulawa, soyayya, harya samu ta musulunta, Dalilinta sbd al'ƙawarin aure da yyi mata,ashe ba sonta yake ba🤔yaje birnin NUFAR domin kai masu tayin Muslunci, sun amince da hakan amma sharaɗin dole ya kwanta da ƴarsu,🤦🏼‍♀️gashi bashi da cikakkiyar lfy mazantakarsa bata aiki😫 ashe mahaukaciya ce ta haife shi.._

“_Kai lalle akwai runguntsumi acikin wannan littafi..  Ba za’ayi babu ni ba, Domin Za’a sha lagwadar romon dadi. shin tayaya ake biya Hansatu?_”

_”Ai Heroine..LITTAFIN *UNCLE NE* Naira 300 ne, Idan kuma kana son vip inda za'a ake posting sau biyu a rana kuma za'a baku littafan data rubuta na kuɗi sai ka bada 600 mai ma kon 1k.. number asusu wato bank account details: 0116886423 : account name sulaiman Na’ima S. Bank name: unioun bank: Sai a tura shedar biya ta 08119237616... A nuna mata ƙauna ta hanyar turowa ta account🤲🏻kamar yadda Za’a  faranta maku a littafin UNCLE NE_
_(Best romantic love story of the year//Had’adden labarin kauna na shekarar 2021)_

Chapter 226-300
***********************************
Ummien Fayroz ta kasa zaune ta kasa tsaye, tunda Fayroz ta kirata, maganar ta kawai ke dawo mata “duk lokacin da kika shirya zamu zo mu zo mu ɗauke ki ni da Abbu ", gaskiya bazata ɓoye ba, tana son Alhaji Jalal, wannan ita ce damar ta ko dan ta samu ta kusanci ƴar ta.

  A ɓangaren Fayroz kuwa Abbu kawai ta ke jira ya dawo su yi magana, tana zauna suna fira da Fareed, da yanzu ya fara saki akan mutawar Farhan ɗan uwan haihuwar shi, Faiha da Fareeha suna taya ta gyara kayanta, Farzana kuma na kwance kan gado, “Fareed ka je ka duba min idan Abbu ya dawo ", “idan na dawo zaki bani sweet?", murmushi tayi tace “har da chocolate ma ", Faiha da ke gyaran kaya tace “mayen sweet kawai, ba ka abu dan Allah sai dan sweet", Fareeha tace “kamar ana yi gaban ki, kullum a bashi sweet ", FAYROZ tace “kar ku dame shi fa, yi maza my love ka dawo", wucewa yayi da gudu, yana fita ya ji ƙarar horn, ai kuwa ya fara tsalle yana murna, “Abbu oyoyo, Abbu oyoyo ", buɗe gate ɗin aka yi ya shigo, parking yayi ya buɗe mishi part ɗin maman su Faisal ya nufa, “Abbu sannu da zuwa" yaji muryar Fareed daga can gefen, murmushi yayi yace “yauwa ɗan lele na zo nan ", zuwa yayi, Abbu ya rungume shi, yace “kai min wannan gurin Mamanku, gani nan zuwa", karɓa jakar ya yi ya nufi gurin maman su, “Mommy gashi Abbu yace a kawo miki ", Mommy da ke zaune ta sha ado, ɗinkin rigar ta yayi matuƙar yin kyau, tashi tayi ta nufi ɗaki ta aje jakar, ɓangaren maman Fahad ya shiga ya mata sallama, dan yau zai koma ɗakin Maman twins, tuƙun-tuƙun tayi da ranta, girgiza kanshi yayi kawai ya fita.

     Fareed ne ya shiga ɗakin Fayroz da sallama, “sister Fayroz, Abbu ya dawo ", chocolate ɗin da ta ɗauko da sweet ta miƙa mishi “thank you love" ta faɗa, Abbu kuwa kai tsaye ɓangaren Maman tweens ya nufa, Yanzu na parlor ya same ta, murmushi ta yi tace “Abbun Fahad sannu da dawowa "murmushi ya mayar mata yace “yawa ƴar aljanna", ɗaki suka nufa, wanka ya shiga ita kuma ta fiddo mishi jallabiyar da zai sa.

     Bayan ya shirya ne ya kira Fayroz a waya “hello Fayroz, ki zo da su Faiha mu ci abinci " ya faɗa, “ ohk Abbu" ta faɗa, “Faiha mu je part ɗin ku, Abbu na jiran mu ", tashi su ka yi, part ɗin Mommy suka nufa, ko da su ka iso Abbu da Mommy su na zaune a parlor suna jiran zuwan su Fayroz, rungume Abbu, FAYROZ tayi ta baya “u are welcome Abbu" ta faɗa, tare da neman kujerar kusa da shi ta zauna, “thank you baby "ya faɗa, su Faiha suka mishi sannu da zuwa, Mommy tayi serving ɗinsu, sannan su ka fara cin Abinci.

******************************
JAHMEEL

A ɓangaren Jahmeel kuwa yau Aida ta wuce kamar yadda su ka shirya.
    Jahmeel kuwa yau aiki yake tuƙuru a ma'aikata, ga yunwa yana ji, amma bazai iya shan coffee ba, dan Fayroz kawai yake tunawa, aiki kawai yake yi, dan haka ya duƙufa agurin aikin shi, ba shi ya dawo gida ba sai bayan magrib, ko da ya dawo a gajiye yake, Mammy na zaune ya faɗa a jikinta, “karya ni za ka yi kowa ya huta " Mammy ta faɗa, Jahmeel yace “ni na isa na karya Mammy na, yunwa ma na ke ji", Mammy tace “subahanallah ka daina zama da yunwa fa, bana so ", Jahmeel yace “bazan iya cin komai a can ba", Mammy tace“ miyasa", “saboda ta barni da....... "da sauri ya rufe bakin shi be ƙarasa ba, cikin rashin fahimtar shi tace “Jahmeel wacece ta bar ka?", cikin basar da zance yace “Mammy ki bani abinci mana, ko sai yunwa ta kashe ni ", tashi tayi tace “bari na kawo maka, ka je ka yi wanka",  ɗaƙi ya shiga da niyyar yin wanka.

-----------------------------

FAYROZ
Ita da Abbu kawai ne a parlor, Faiha da sauran yaran sun kwanta, Mommy kuwa tana ɗakin Fareed tana ta faman lallashin shi yayi barci yana mata rashin ji .

    “Abbu mun yi magana da Ummie fa" Fayroz ta faɗa, Abbu yace “me tace miki ", “haka tace za ta yi tunani", murmushi yayi yace “ina fata ta dawo gare ni ", “ameen, amma Abbu mu za mu je mu ɗauko ta ko?", Abbu yace “eh mana, ai dole ne ma, ina kewarta fa ", rufe fuskarta tayi alamun taji kunya, “kar ki damu da Abbunki baya jin kunyar yaran shi", murmushi tayi dan ita a gurin ta wannan ba wani abu bane, Mommy ce ta fito tace “wash! Da ƙyar na samu yayi barci, kwanannan Fareed baya ji", Abbu yace “yauwa sannu da zuwa ƴar Aljanna zo ki zauna muyi fira ", murmushi Fayroz tayi tace “bari na wuce ni zan kwanta", Mommy tace “Allah yasa bani na kore ki ba, ki dawo ki zauna ", “a'a Mommy, kawai dai barci nake ji" ta faɗa, Abbu yace “to shikenan, love ki kwana lafiya ".


   Ɗaki ta nufa kai tsaye, tana shiga wayarta ta shiga ringing, “hello Ummie ya gida" ta faɗa, “lafiya ƙalau Fayroz, ina kewarki ", “nima haka Ummie I miss you", “ya kike "Ummie ta faɗa, Fayroz tace “ina lafiya Ummie, kin yanke shawara", murmushi tayi tace “eh Fayroz na amince zan dawo ɗakina ", “wow Ummie that's amazing, wallahi na ji daɗi sosai, zan faɗawa Abbu sai mu zo mu zo", “to shikenan "Ummie ta faɗa, Fayroz tace “nagode sosai da sosai Ummie, ina alfahari da ke , kin ga yanzu ahalin mu ya cika", Ummie tace “shine burina Fayroz, ahalina zai cika ", sun jima suna fira, sannan su ka yi sallama ta kashe wayar, Ummie farinciki ya kama ta, ji take yi ina ma ta baro ƙasar tun yau, lokaci yayi da zata kasance tare da iyalanta, Fayroz ma tsabar farinciki barci gagarar ta yayi, ta matsu safiya ta waye.

SAI MUN HAƊU A NEXT CHAPTER.

TAKU HAR ABADA QUEEN NASMERH ✍️✍️✍️✍️

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️⚔️💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

FAYROZ❤️❤️Where stories live. Discover now