Chapter 221-225

56 4 3
                                    

      💮💮💮💮💮💮
                   FAYROZ
             💮💮💮💮💮💮

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶  *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*
************************
Page 221-225
**************************

Kallon ta yake yi, cike da mamaki, shi ya manta ma yana da ƴa mace, Jahmeel kallon yanayin mahaifin shi yake yi, Aidah ce ta ƙaraso gaban su, “ina wuni Pappy "ta faɗa muryar ta na sarƙewawa da alama cikin firgici take da fargaba, murmushi yayi mata sannan yace “lafiya lau, dama kina nan", murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo, wato ma ya manta da ita, Lateef kama hannun Jahmeel yayi yace “my son mu shiga ciki ", Jahmeel ya kalli Pappy irin shi kaɗai ya gani, Pappy ya halbo jirgin Jahmeel, dan haka ya juyo ya kalli Aidah dake tsaye tana kallon su, “mu shiga daga ciki" Pappy ya faɗa ciki-ciki, dan har yanzu yana da aƙidar shi ta rashin son ƴa mace, sai dai yanzu yayi sanyi sosai, ya rage tsanani.

    Cikin parlor suka shiga, wanda yake ɗauke da hotunan Jahmeel a bango gida, ko ta ina ka juya zaka ga Hoton shi lokacin da yana ƙarami, kallon parlorn Jahmeel ke yi, bazai ɓoye gaskiyar ba shima yana son Pappy, amma baya son halin shi ne, Aidah ya kalla duk a takure take ta kasa sakewa, duk sai yaji ba daɗi, ƙanwarshi da yafi so akan komai ke jin haka, da akwai damar da zai maida son da mahaifin su ke mishi da ya juya shi gare ta, amma yanzu ma akwai damar insha Allah zai dai-daita komai.

   Wasu ma'aikata ne suka shigo da abinci kala-kala, Jahmeel yace ya ƙoshi, Aidah ma bata ci ba, dan a ganin ta wanda aka kawo domin shi be ci ba, to miyasa ita zata ci, Pappy ne ya shigo ɗauke da wani ƙaton box mai kyau, miƙawa Jahmeel yayi yace “masoyin ɗana wannan naka ne ", buɗewa yayi yaga wani tsadadden agogo wanda mallakar shi ma wani aiki ne, kallon shi kawai Jahmeel ke yi, Pappy ya ɗago ya kalle shi cike da zumuɗi ya ke magana “Jahmeel na daɗe ina jiran zuwan ka gashi dai yau ka zo, wannan ajiyar ta jima tana jiran ka, dan Allah ka karɓi kyautar da Pappyn ka ya aje maka ", “Pappy bazan karɓi kyautar nan ba, saboda bani kaɗai ka haifa ba, idan har kana so na karɓa, to ka ba ma Aidah haƙƙin ta na zama ƴa gare ta, ni bana so ranar gobe ƙiyama ka tashi da laifin nuna bambanci tsakanin ƴaƴan ka", maganar Jahmeel yayi tayi matuƙar taɓa Pappy, shiru yayi sannan yace “to shikenan Jahmeel, idan haka kake so zan yi ", Aidah ce ta tashi ta bar parlorn, waje ta fito , Jahmeel ne ya tashi yace “Pappy ni zan wuce" be jira me zai ce ba ya wuce.

      Waje ya same ta tsaye gaban mota, idon ta sun cika dab da hawaye, rungume ta yayi ta baya yace “ me ya sami ƴar ƙanwata, jinin jiki na "rugumar da ya mata ne yaba hawayen ta damar zubowa, jin saukar su a hannun sa ne yasa yayi saurin juyo da ita, hawaye duk sun wanke mata fuska, yace “haba Aidah, can da baki yi kuka akan haka ba sai yanzu, kina so naji ba daɗi ne ko?", girgiza kai tayi alamar a'a, hannun shi ya sa yana share mata hawaye, sannan yace “oya naa, muje kinsan zaku wuce yau", murmushi tayi wanda bai kai ciki ba, dan tana matuƙar jin ciwon abun.

  A mota Jahmeel ya lura da yadda ta ke ba haka ya saba ganin ta ba, kallon ta yayi, sannan ya maida hankalin shi kan titi, yace “to sai me dan Pappy baya kula ki, ba ga ni ba, kuma ga Mahboob, ga Mammy, kuma kin kusa samun baby itama zata kula ki ", murmushi tayi har zuciyar ta taji daɗin maganar musamman da yace babyn ta, dan yaddan take jin son abunda ke cikin ta bama kaɗan bane, shafa cikin tayi sannan ta rufe idon ta, a hankali tana jin damuwar ta na wucewa, tabbas tasan Jahmeel kamar uba yake a gareta, wani lokacin ma kamar uwa, a taƙaice ma Jahmeel ya fi mata komai, da haka suka wuce gida.

************************************
  Fayroz  tana zaune ta tuna da Ummie, wayar ta ta ɗauka ta kira Ummie, bugu bigu wayar tayi Ummie ta ɗaga, “hello Fayroz yakike ", “Ummie ina lafiya alhamdulillah, ya Saudi Arabia", “Fayroz dafatan kina jin daɗin nan "murmushi Fayroz tayi tace “eh ina jin daɗi, yaushe zaki dawo nan mu zauna tare", shiru Ummie tayi, jin shirun yayi yawa yasa Fayroz tace “Ummie kinsan Abbu yana sonki ko? Kuma kinsan ko yaushe hanya a buɗe take gare ki, duk lokacin da kika shirya dawowa ni da Abbu zamu zo mu tafi dake, kuma nasan kina son Abbu har yanzu, bayan haka ma Abbu baya da wani laifi na komai, kawai dai wani kuskure ne da ɗan adam baya wuce su ", Ummie ta san duk abunda Fayroz ta faɗa gaskiya ne, “to shikenan zanyi tunani akai" ta faɗa, murmushi Fayroz tayi saboda tasan daga ƙarshe amsar Ummie bazata zama a'a ba, sun jima suna fira a waya sannan tayi mata sallama.

        A ɓangaren Faisal kuwa kwanannan baya jin daɗi, wasu ruwa ne masu wari ke fitowa daga jikinsa, saboda yawan amfani da yakeyi da al'aurar shi, gurin wannan haramtacciyar sana'ar da yake yi ta homosexuality, ya rame yayi baƙi, source of income ɗin shi ya tsaya, yanzu bai da hanyar samu, wayar shi ya ɗauka ya kira  maman shi, ɗagawa tayi “ɗana na kaina, ɗan lele na faɗa min akwai wata damuwa ne ", “mama an samu matsala fa, kuɗi na sun ƙare, kinsan baba ya rufe min hanyar cirar kuɗi ta family accout ɗin mu, kuma banda lafiya, wasu ruwa na zubar min a jiki wanda haka ya janyo min rashin kuzari, bana jin daɗi", “subahanallah, garin yaya, kar ka damu zan turo maka da kuɗi kaje a maka magani, kamar nawa kake buƙata ", “irin one billion(biliyan ɗaya)" murmushi tayi tace “baka da matsala ɗan lele na, sai ka ji ni "kashe wayar yayi.

NI KUWA NASMERH IMANI YA CIKA NI, WATO BAKA SHIRYA YIN NA DAMA BA FAISAL.

*******************
A parlor suka sami Mammy ta gama haɗawa Aidah kaya, Mahboob ma fitowar shi kenan daga ɗaki su Aidah suka shigo, zuwa yayi ya tari matar shi, sannan suka yiwa Mammy bankwana suka wuce.
  “Jahmeel ya kuka sami Pappyn ku", “Mammy ba daɗi, kamar kullum har yanzu Pappy be canza ba, duk da ya rage tsauri ", murmushi Mammy tayi tace “yadda ya rage tsauri haka zai bar duk wani halin shi, zai so Aidah kai dai kawai ka tsaya ka gani", kallo Mammy yayi yace “to Allah yasa", “Ameen "Mammy ta faɗa, Jahmeel yace “na lura kina son kare Pappy", kallon shi tayi tace “in banda abunka, idan ban kare uban ƴaƴana ba wa zan kare ", murmushi Jahmeel yayi wanda yasa dimples ɗin shi na kowane ɓangare suka lotsa, sannan yace “in tambaye ki? Zaki faɗa min gaskiya", gaɗa kai tayi alamar eh, “kina son Pappy har yanzu, kuma idan yace ki dawo ɗakin ki, zaki dawo ", shiru tayi sannan tace “Jahmeel nima bansani ba amma ina son Pappyn ku, kuma zanso na koma ɗakin shi, amma bani da ƙwarin guiwa, kuma ina tsoron abunda ya faru baya ya sake faruwa, shiyasa bana tunanin zan koma ɗakin shi", tunda Mammy ke magana Jahmeel ya kafe ta da ido, gaskiya Mammy macece ɗaya tamkar dubu, duk da abunda Pappy ya mata amma har yanzu tana sonshi, kallon ta yayi sannan yace “Mammy insha Allah watarana Pappy da kanshi zai neme ki "murmushi ta mishi, sannan tace “bari na kawo ma masoyin ɗana abinci", kitchen ta shiga, tayi kukan ta, har sai da ta gaji sannan ta haɗo kayan abincin a try ta kawo mishi, ci yayi sannan ya wuce ɗaki don yin wanka.

MASU KARATU BARKA DA WARHAKA, DAFATAN DUK KUNA LAFIYA.
INA GODIYA A GAREKU.
KUYI HAƘURI YANZU BA KO YAUSHE NAKE SAMUN YIN TYPING BA, SABODA JARABAWA DA NAKEYI.

I LOVE U ALL.

TSARA LABARI :QUEEN NASMERH👑💞💞💞💞💞💞

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️💕💕💕💕💕💕

FAYROZ❤️❤️Where stories live. Discover now