Chapter 51-55

28 4 4
                                    

💮💮💮💮💮💮
FAYROZ
💮💮💮💮💮💮

MALLAKIN ;
ASMA'U NAANERH (NASMERH) 💗💗💗💗💗
&
FATIMA USMAN BAUCI 💗💗💗💗💗




✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*


Page 51-55

***************
Washe gari da safe.

FAYROZ ce kwance, amma tun jiya barci bai ɗauke ta ba, tunani takeyi anya mahaifinta nada rai? , shin idan mahaifin ta na da rai zai karɓe ta hannu bibbiyu? , miye dalilin Ummie na nisanta daga mahaifinta?, da wannan tunani ta gagara barci , kasancewar bata sallah yasa bata sauko daga kan gado ba, Ummie kuwa tunda tayi sallah ta koma barci bata tashi ba.

Sai ƙarfe 11:00 Ummie ta farka ɗan ta gaji, ta jima batayi tafiya ba.

Wanka suka yi suka shirya, sannan tace "FAYROZ mahaifinki ɗan Adamawa ne, dan haka yanzu ma jirgi zamu hau mu wuce ", gaɗa kai FAYROZ tayi tace" to shikenan badamuwa".

Mota suka shiga sannan suka nufi airport, jirgi suka hau zuwa adamawa, alhmdllh sun isa lafiya.

Guards ɗin Ummie ne da dama sun biyo fligt ɗin safe zuwa Adamawa, suka zo suka take musu baya, basu wani sha wahala ba suka iso, kasancewar yanzu mahaifinta shine Gwamnan Adamawa.

Wow! 😯, masu karatu wani gida na gani haɗadɗen gida, banyi tunanin a Nigeria akwai gida mai kyau haka ba.

Gate ɗin gidan aka buɗe musu, bayan an musu bincike, ɗaya daga cikin me gadin ya gane Ummie hakan ne yasa shiga cikin gidan be musu wahala ba.

Aharabar gidan naga wasu yara da aƙalla basu wuce shekara uku ba, daganin su ƴan biyu ne, kamar su har ta ɓaci, shekarunsu zasu kai 7 a duniya wasa suke yi hankali su kwance, kallon su FAYROZ keyi cike da ruɗani, ta kasa fahimta cewa wai yau ita ce agidan su, dan bazata ɓoye gaskiyar ba, gidan mahaifinta shine gidan su, koma ta yaya ne.

Shiga Suka yi cikin gidan, buɗe ƙofar sukayi, a parlor suka zauna, wata budurwa ce nagani zaune, Ummie ce tace "Fareeda shiga daga ciki ki kira min mammar ki ", bata yi niyyar tashi ba saboda bata son Ummie ko lokacin da tana nan, dan da alama yarinyar ta girmi FAYROZ.

Ɗaki ta shiga tace "Mama, Ummien FAYROZ tana parlor tana jiran ki", gaban mama ne ya faɗi ba dai Ummie ta dawo ba.

Gyale ta ɗauka ta fito, aparlor ta sami Ummien FAYROZ, da FAYROZ a zaune, zaunawa tayi hankalinta duk a tashe, gaisaws sukayi sannan Ummie tace "ina his excellency yake ", murmushin ƙarfin hali mana tayi tace yana ɓangaren Amarya yau ba ɗaki na yake ba, amma yau zan karɓi girki", Ummie FAYROZ tace "to ba damuwa zamu jira shi nan ", Mama dake kallon FAYROZ tace "Ummien FAYROZ wannan fa wacece, kunyi kama", jawo FAYROZ Ummie tayi tace "FAYROZ ce hasken idona ", dummmm gaban mama ya faɗi inalillahi ba dai FAYROZ ce ta girma haka ba, amma tsabar munafurci ta dake sannan tace"kaii masha Allah ƴata ashe kin girma, zo na rungume ki", ba musu FAYROZ ta tashi taje gaban Mama, rungume ta tayi, ita kuwa Ummie kallo Mama take a ɗage dan agidan ba wanda bata san halin shi ba.

Suna zaune agurin har magrib, Ummie kawai ce ta shiga ciki tayi sallah, bayan sun gama sallah ne, Fauziya ta kawo musu abinci da snacks da lemu suka ci, Abbu ne yashigo wato mahaifin FAYROZ,murmushi yayi da yaga Ummie dan yasan zai ji labarin ƴarshi, lokacin FAYROZ tana kitchen gurin kai abinci.

Gasaiwa sukayi da Ummie sannan ya tambaye ta ina FAYROZ take "FAYROZ tana kitchen tare muka zo, yanzu lokaci yayi da zata zauna agidan ka ",ba ƙaramin daɗi yaji ba, dan ya daɗe yana jiran ranar nan, Mama kuwa duk hankalinta ya tashi.

Murmushi ya sake yi, masu karatu gaskiya mahaifin FAYROZ wato his excellency Jaalal kyakkyawa ne duk da ya tsufa amma kyan shi a bayyane yake.

Shigowa FAYROZ kenan ɗakin ya ɗaga kai da kallo yake binta duk da ba'a faɗa mata ba jikin ta ya bata wannan ne mahaifin ta, taji wani irin daɗi tambayar kanta takeyi dama haka ake ji idan aka ga mahaifi, to wannan ma kaɗan kenan ina ga ta samu soyayyar shi.

Buɗe mata hannu yayi alamun ta zo , zuwa tayi ta rungume shi, sai taji kamar su mutu ahaka, ji takeyi tasamu komai, duk farincikin da ta rasa to yanzu ta samu.

NI KUWA ASMA'U KAMAR NA TAKE KAN ƊAN JARIRI DAN MURNA, DAN NAGA SONTA DA ƘAUNA A IDON HIS EXCELLENCY JAALAL.

Shima sonta yake ji har cikin jikin shi, tabbas FAYROZ ita ce ƴar shi da yafi so fiye da komai.

Duk wani company da mahaifinta ya buɗe to da sunan ta ne, kuma har yau har gobe duka companies ɗin shi da sunan ta ne FAYROZ JAALAL.

Ɗagowa tayi tana kallon shi, "yace yanzu kin kaji muje ki huta "hannun ta ya kama suka fita daga side ɗin, wani part naga anbuɗe, irin sauran part ɗin ne, dan gidan His JAALAL unguwace ko ma ince gari, daga lefe side akwai four part na matanshi mai fenti pink, right side akwai four part mai fenti blue na yaranshi maza each part akwai 4 bed room, Sannan daga tsaka kuma akwai wani tanƙamemen gini, mai fenti fari, sai kul titi, da garden, banda gurin wasar yara da gurin sai da snacks, da gurin gyaran kai, masu karatu duk wani abu da kake buƙata acikin gidan zaka samu, har ma da gidan kwalliya, amma na ƴan gidan kawai.

Part ɗin da nake tunanin na Ummie ne ya buɗe mata, komai agyare duk da ba mutane amma kullum be cire rai ba, yasan ko wani lokaci zata dawo saboda haka ne kullum sai an gyara part ɗin, kuma lokaci zuwa lokaci yana sa a canza kayan ɗakin.

"FAYROZ nan shine ɓangaren Ummien ki lokacin da tana nan, ki zauna anan, mallakinki ne, idan har kinga wani abu da bai miki ba to ki min magana zan sa a canza miki".

Murmushi tayi mai sanyi tace "Ummie fah ", "karki damu ƴata, watarana komai zai wuce kamar yadda kika dawo, haka itama zata dawo, amma yanzu har ta wuce", kallon shi takeyi cikin rashin fahimta, miyasa Abbu yake magana kamar yana da tabbas ɗin ta wuce, "nasan me kike tunani, kina tunanin yadda aka yi nasan ta tafi ", gyaɗa kai tayi alamun eh.

" muna fitowa tabi bayan ƙofar Maman FAHAD ta wuce" kuma naga lokacin dan bamu fita, bata so ta miki sallama ne saboda tasan zaki ce sai ta kwana anan ", shiru FAYROZ tayi, sai can ta ja dogon, dafa ta yayi yace "ki huta ƴar lelena, insha Allah gobe zaki san asalin labarina da yadda na auri Ummienki", murmushi tayi tace "ohk Abbu thank you ".

MASU KARATU KUNJI YADDA MAHAIFIN FAYROZ YA KARƁETA HANNU BIYU DA ALAMU ƳAR GABAN GOSHI CE

INSHA ALLAH, IN ALLAH YASA MUNA DA RAI ZAN KAWO MUKU ASALIN LABARIN.

VOTE
SHARE
AND COMMENTS.
PLSSSS🙏🙏

HAƊIN GUIWAR
QUEEN NASMERH & FATY USMAN 🌼🌼🌼🌼🌼🌼
ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️💗💗💗💗💗💗💗💗💗💗💗

FAYROZ❤️❤️Where stories live. Discover now