Chapter 46-50

26 3 0
                                    

💮💮💮💮💮💮
FAYROZ
💮💮💮💮💮💮

MALLAKIN
ASMA'U NAANERH (NASMERH) 💕💕💕💕💕
&
FATIMA USMAN BAUCHI 💕💕💕💕💕

💃💃💃💃💃💕

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*



**********************
PAGE 46-50
*********************

Jirgin DALEEL ya sauka Cyprus lafiya, da isar sa ya wuce hotel already yasa an Mishi komai, wanka yayi ya shirya cikin pajamas ɗin shi.

Kwanciya yayi kan gado, rufe idon shi yayi a hankali yana tunawa da Saudi Arabia, FAYROZ ce ta faɗo mishi arai, ko da daƙiƙa ɗaya be taɓa tunanin irin lokacin nan ba, ace wai shi ɗin ya haƙura da FAYROZ ba, amma that's his fate 😢, idon shi yaji sun kawo ruwa, alamun ƙwalla zata zubo, hannun shi ya saka ya tare su.

Ahaka DALEEL ya dinga tunani har barci ɓarawo ya sace shi.

NI KUWA NACE KAZO DAN KA MANTA DA ITA, AMMA HAKAN YA GAGAREKA.

******************
After five days.

FAYROZ ce zaune aparlor tana kallon favorite film ɗin ta, Ummie ta shigo, da murmushi FAYROZ ke binta har ta zauna kusa da ita "FAYROZ ina so zamuyi magana dake ".

Dummmmmm gaban FAYROZ ya faɗi, dannewa tayi cikin ƙarfin hali tace "ina jinki Ummie", "maganar akan mahaifin ki ne ", murmushi FAYROZ tayi wanda be kai ciki ba sannan ta gaɗa kai alamun tana jinta.

Gyara zama Ummie tayi, sannan tace " FAYROZ kiyi huƙuri, tsawon lokacin nan na nisanta ki da mahaifinki, kina da damar da zaki juya min baya saboda na cutar da ke ta hanyar hana ki mahaifin ki", shiru FAYROZ tayi,

Ji tayi zuciyar ta ta tsananta bugawa "Ummie duk abunda kikayi ni zan ɗauke shi amatsayin ƙaddara karki manta komai muƙaddarine daga Allah "

FAYROZ❤️❤️Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz