Chapter 66-70

27 3 0
                                    

💮💮💮💮💮💮
FAYROZ
💮💮💮💮💮💮



✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Page 66-70
**************
Janeesa 13 a duniya, Jaalal kuma yana da 17years a duniya, Allah yayi wa Alhaji Musa rasuwa sanadiyyar haɗarin jirgi, wanda ya kama shi hanyar shi ta zuwa Nigeria.

Jaalal da Janeesa sunyi kuka sosai wanda haka yasa suka kasance su ka ɗaine, abinci ma wahala yake musu, cikin ikon Allah gadon mahaifin su ya dawo hannunsu.
Dashi suke karatu, sannan aka raba gado, Jalaal yana juya nashi, amma ita Janeesa ya aje na ta sai ta mallaki Hankalinta.

Watarana sun fita tare da ita, "Janeesa ki zauna anan ni bari na shiga na siyo miki " ya faɗa yana nuna mata gaban motar da suka zo da ita, dama can Jaalal ya iya mota tun Alhaji Musa na da rai.

Zaunawa tayi, tana murmushi har ya shige shagon.

Bayan minti 6 ya fito daga shagon riƙe da leda, Jaalal ya ƙara girma duk da shekarar shi 18 amma idan ka ganshi sai ka rantse yayi 20.

Mamaki ya kama shi lokacin da ya tarar ba Janeesa a mota, hakan ba ƙaramin tada mishi hankali yayi ba.

Yayi neman duniyar nan amma be ganta ba haka ya haƙura ya dawo gida.

Tun daga ranar da Janeesa ta ɓata be sake ganin ta ba, kuma be cire rai ba, akan cewa wata rana zai ganta kuma zata dawo gareshi, amma shiru har yanzu.

Jaalal ya mallaki hankalin kanshi, yana so ya zo Nigeria amma be san kowa ba, saboda haka ya yanke hukuncin zama a Saudi Arabia, har zuwa ranar da Allah yayi ya ga Jaseena.

Bayan shekara 10

Lokacin Jaalal yana da shekara 28 a duniya, saboda haka ya fara tunanin yin aure da wata ƴar makarantar su da ke garin saudi.

Ummi ƴar gidan manya ce, be wani sha wahala ba saboda shima lokacin yana da kuɗi sosai.

Masu karatu ansamu matsala saboda Abbu (Jaalal) ya musu ƙarya akan cewa shi ɗan saudia ne, amma daga baya da suka gano gaskiya suka hana aure lokacin Ummie ta na da cikin FAYROZ, yayi juyin duniya akan su bashi matarshi, amma ita kanta Ummie ji tayi duk duniya ba wanda ta tsana, akan me zai mata ƙarya.

Iyayen Ummie sunyi iya ƙoƙarin su na gani Abbu ya sake Ummie amma yaƙi haka yasa suka shigar da shi ƙara, kotu ta raba auren, amma saki ɗaya.

Saboda tashin hankali a ranar Abbu ya bar Saudi Arabia.

Bayan ya dawo da wata huɗu ya samu labarin Ummie ta haifi ƴa mace, yayi farinciki sosai har, amma da ya je can sai labari ya canza zani.

Bayan ya dawo ne ya ƙara aure.

Ba yadda beyi ba amma Ummie ta hana shi zuwa, sunan ƴar tashi ma daƙyar ya samu aka faɗa mishi.

So da yawa yakan shirya yaje gani ƴar shi, har da tsaraba amma Ummie bata taɓa karɓar komai, ballantana ma yayi tunani gani FAYROZ, lokacin da ya dawo ne ya ke hukuncin bazai ƙara zuwa ba, yasani watarana FAYROZ zata dawo gare shi, saboda haka ya dawo ya cigaba da zama da iyalansa sannan ya ƙara aure.

Ya gina gida na ji na gani, sannan harda part ɗin Ummie, duk duniya ba wadda his excellency Jaala yake so irin Ummie yaranshi ba wanda be santa ba, saboda haka ne dukan su basa sonta hakama iyayen su.

Musamman FAYROZ da yake bin Page ɗin ta na yanar gizo.

Ya fito takarar gwamna a garin su cikin iyawar Allah yasamu nasara.

Ghushan itace matar shi ta farko wato Ummie suna da ƴa ɗaya FAYROZ.

Sai Munawwar (maman Fahad) Tana da yara 7 dashi, Fahad, Faheem, Farooq,Fareeda da Fawad, Fadeela da Faisal.

Bilkisu itace matar shi ta uku(ummu Fateema) , suna da yara 5. Fatima, Fawaz, Farhana, Fu'ad da Fiddausi ana ce mata (Fahna) .

Sai kuma Amaryar shi Salima (maman twins) yaran ta biyar, Faiha, Fareeha, Farzana sai twins Fareed da Farhan.

All in total yaran his excellency Jaalal 18.

FAYROZ nada 33 years

Fahad yayi aure, he is 30 years old, Faheem na da shekara 28,Farooq 26,Fareeda 24,Fawad 22,Fadeela 20, Faisal 18.

Fateema nada shekara 29,Fawaz 27,Farhana 25,Fu'ad 23,Fiddausi 21,

Faiha na da shekara 19, Fareeha nada 17, Farzana 15, sai twins Farhan da Fareed 3 years.

Yaran da suka yi aure agidan kuma Fahad, , Farooq,Fawad, Faheem da Fadeela rana ɗaya sukayi aure, yaran da suka rage wa maman Fahad sune Fareeda da Faisal.

Ɗakin Ummu Fateema kuwa, duka yaranta sunyi aure, dan mahaifin su baya wasa da kinsamu miji ko ka samu mata za'a maka aure ya huta

Maman twins kuwa bata aurar da kowa ba duka yaranta na gabanta.

Fareeda ma baƙin hali ne ya hanata aure dan she is 24 years old, Fadeela ma da take ƙanwar ta tayi aure Faisal kuwa yayi ƙanƙanta da aure 18 years .

"wannan shine labarina FAYROZ " Abbu ya faɗa yana can dogon numfashi, shiru tayi na ɗan lokaci sannan tace "insha Allah Ummie zata dawo gareka, Allah ya jiƙanta Baba da Mama", shafa kanta yayi yace "Ameen tuffan idona, Allah ya miki albarka ", "ameen Abbu, Allah ya bayyana Aunty Janeesa".

MU HAƊU A NEXT CHAPTER DAN JIN YADDA AUREN AIDAH DA MAHBOOB ZAI KASANCE DA KUMA RAYUWA FAYROZ A NIGERIA.

LOVE U ALL ❤️❤️❤️❤️

TSARA LABARI QUEEN NASMERH ❤️💕💕.

RUBUTAWA QUEEN NASMERH DA MOM MUSAYYID.

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️💞💞💞💞💞💞💞💞💞

FAYROZ❤️❤️Where stories live. Discover now