Chapter 76-80

25 3 0
                                    

💮💮💮💮💮💮
FAYROZ
💮💮💮💮💮💮


✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

************

Page 76-80
**********
Tafiya sukayi zuwa airport, kafin su shiga jirgi zuwa Dubai, dan Mahboob ba nan yake zama ba, kiran JAHMEEL, Aidah tayi suka sake bankwana kafin suka wuce.

*****------------******

Daleel ne kwance yana waya dagani firar tana mishi daɗi, murmushi kawai yake, " I love u so much Haleematu "ya faɗa, ɗayan ɓangaren naji ance "I love u more", ci za lips ɗin shi yayi yace "anjima kaɗan zan zo gurin coffee ɗin nan sai mu haɗu ", "ohk my love sai ka zo" ta faɗa, murmushi yayi sannan ya kashe wayar.

NI KUWA NASMERH MAMAKI DUK YA CIKA NI, WAI DALEEL HAR YA MANTA FAYROZ ANYA BA CIN AMANA CIKIN AL'AMURAN NAN🙄😂✍️.

*******************

FAYROZ

Tana waje da su Fareed, sai labari suke zuba mata, gate ɗin gidan aka buɗe wata danƙareriyar mota naga ta shigo, dagudu ta tsaya irin driving ɗin nan na wulaƙanci, wani saurayi ya fito, mai shekaru 18, fari ne yana da kyau ba laifi, Fareed ne yace "oyoyo senior Faisal ", Farhan ne ya harareshi "kai kullum baka iya kama kanka, ko ka mishi magana ba kula ka zai yi ba".
Turo bakin shi yayi yace "amma ai yaya na ne dole na mishi magana", FAYROZ tace " Fareed yayi gaskiya, ko ya yayanka yake to dole ka girma mashi,ko da kuwa talaka ne ko me kuɗi, mai mutunci ko mara mutunci , wannan girma ne Allah ya ba mutum, dole ka bashi shi, Farhan ka kiyaye sannan ka rage zafin rai ", Fareed yace "haka mama ke gaya mana amma duk da haka shi baya ji", FAYROZ tayi Murmushi tace "shikenan ni bana so kuna faɗa, kowa da halin shi ake zama dashi ".

Faisal da ko ta kansu beyi ba ya shiga ciki, Maman Fahad ya faɗa da ƙarfi yana kwallawa maman shi kira ba ko girmamawa na uwa.

Da sauri ta fito, "Autan mama ka shigo kenan" ta faɗa, "ba wannan na tambaye ki ba "ya faɗa yana zaunawa "me kika dafa", "fried rice and chicken aka dafa, zakaci ne "ta faɗa, Faisal yace "ki jiki da wata magana to me zanyi in banci ba, ki sa akawo min", murmushi tayi sannan ta tashi dan duniya cikin yaran ta ba me raga mata inba Fadeela da Faheem ba, duk sauran sun rainata, musamman Fareeda, Farouq da Faisal, sauƙi-sauƙi ma Fahad da fawad .

Bayan ɗan lokaci ta dawo da abinci atire, duk izzar ta idan aka zo maganar yaranta dole sai ta musu aiki.

Lemu ta kawo mishi da ruwa, sannan ya fara cin abinci, bayan ya gama ne yace "wacece wannan me idon mayun da nagane tare da twins ", Maman Fahad ko an sosa mata inda ke mata ƙaiƙayi tace "Ghushan ce ta Saudi Arabia wadda baban ku ke nuna muku, babba yayar ku", da sauri ya miƙe tsaye, "what! So kike kice min wannan FAYROZ ce ta gaban wayar Abbu ", "ita ce fa" maman Fahad ta faɗa, fita yayi ba tare da yace komai ba, da ƙarfi ya buɗe ƙofar parlorn ya fita.

A harabar gida ya sami Fareed da Farhan, "kai ina wadda kuke zaune tare ", Farhan ko kallon shi beyi ba dan duk duniya idan akwai abunda ya tsane to ƴan ɗakin maman Fahad ne dan sunfi kowa matsala in aka cire Senior Faheem da Sister Fadeela, Fareed yace "tana ɓangaren can" , yayi nuni da part ɗin da Abbu ya kai FAYROZ.

Juyawa yayi ya wuce, su kuma suka cigaba da wasa, da ƙarfin tsiya ya tura ɗakin FAYROZ ya shiga," ke..............

************
Amarya Aidah an isa Dubai lafiya, kowa gidan shi ya wuce, Mahboob ya ɗauki amaryar sa zuwa gidan shi dake nan Dubai.

Bayan tayi wanka, wanda shima shigowar shi kenan ɗakin ta dan ya shiga wanka, yace "wifeey ki shirya, sai muyi sallah ", Murmushi tayi tace to.

Sallah sukayi sannan suka haura kan gado, jawo ta yayi jiki sa ya rungume, addu'ar saduwa aure yayi sannan suka Lula duniyar ma'aurata.

NI KUWA QUEEN JIKINA RAWA YAKEYI, KUYI HAƘURI MASU KARATU BAZAN IYA ƊAUKO MUKU RAHOTO BA, SABODA ALQALAMI YA FAƊI NA KASA NEMOSHI😜😂

************

Kwance yake ya rasa abunda ke mishi daɗi, yanzu Aidah tayi aure ta bar shi da kewa, me zai hana kayi aure, yaji zuciyar shi na faɗa mishi, "a'a ina ni aure baya gabana ", ya faɗa da ƙarfi, sai yanzu FAYROZ ta faɗo mishi arai, dama ya jima be je gurin Ummie ba, dan lokaci zuwa lokaci yana zuwa, ko ba komai yana respecting matar, wannan yana ɗaya daga cikin dalilan da yasa ko yaji aranshi yana so ya kore FAYROZ gurin aiki sai ya tuna mutuncin da ke tsakanin shi da Ummie.

NI KUWA NACE KAI JAHMEEL KO DAI KO DAI 🤔🤔.

Da wannan tunanin barci ɓarawo yayi awon gaba dashi.

Asuba ta gari JAHMEEL ❤️❤️❤️❤️.

MASU KARATU MU HAƊU A NEXT CHAPTER DAN JIN ABUNDA ZAI FARU TSAKANIN FAYROZ DA FAISAL ƘANINTA.

CAN'T LOVE U LESS ❤️❤️.

NI NASAN CHAPTER YANA MIN KAƊAN AMMA KUYI HAƘURI MU ZAN TSAKA DA SEMESTER YANZU KARUTU ZAFI YAKE YI, INA ƘORINE GURIN MUKU TYPING.

THANK YOU FOR READING.

VOTE
COMMENTS
AND
SHARE
PLSSSSS

TSARA LABARI :QUEEN NASMERH.

ALQALAMIN MU NE :QUEEN NASMERH & MOM MUSAYYID ❤️❤️

ALQALAMIN YAFI TAKOBI ✍️❤️❤️❤️❤️❤️💕💕💕💕💕

FAYROZ❤️❤️Where stories live. Discover now