Chapter 206-210

27 4 2
                                    


💮💮💮💮💮💮
FAYROZ
💮💮💮💮💮💮

https://www.wattpad.com/story/255808218?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_reading&wp_page=library&wp_uname=AsmaunanaLawalliman&wp_originator=O3VdfKPvbMhkEhpNrQgnRWE0eyLarV04bvF0OcQ31byoBx69%2BVCtUljiQ%2B7%2FftlgkxJ%2BBztqtG02hrj6EPgFVFyX1YzF3Q88zyRR4MN%2F2us9Nu0mxvker%2Bf39FaGN4b8
*******
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*********************
Page 206-210
'**************"******
JAHMEEL ya fuskanci rayuwa iri daban-daban yadda, a haka ya dinga rayuwa da daɗi da ba daɗi be taɓa bari AIDAH ta fuskancin wahala ko rashi ba, bata taɓa neman abu ta rasa ba ko yaya ne, sannan ya bata tarbiya dai-dai gwargwado, MAHBOOB ma yana iya kar ƙoƙarin shi kafin ya girma ya fahimci yana da iyaye, lokacin ne ya koma gurin dangin shi, mahaifiyar shi kawai ta rage mishi.

Amma lokaci zuwa lokaci yana zuwa gurin su AIDAH.

Kamar wasa JAHMEEL ya samu wasu kuɗi na tallafi, da waɗannan kuɗin ya fara gina wata ƙaramar ma'aikata, sannan ya zuba masu aiki, abun kamar wasa hanyar arziki da buɗe mishi.

Watarana yana office zaune Mahaifin shi LATEEF ya zo gurin shi, "JAHMEEL ɗana ya kamata ka dawo gareni ", JAHMEEL ko kallon shi beyi ba, shi a rayuwar shi ko ganin Pappy baya so yana yi, dan hakan na tuna mishi da ranar da ya jefo Mammy daga sama.

"JAHMEEL, idan bazaka saurari Pappyn ka ba to ka mishi wata alfarma, ka karɓi kyautar da ya baka, na gina maka ma'aikata ka koma can, wannan is to local for you " Pappy ya faɗa, JAHMEEL da yake haɗa takardu ne ya ɗago, da wani mugun kallo yake bin shi sannan yace " kai ba Pappy na bane, sannan ni bazan karɓi kyauta daga gurin ka ba sai dai na siya, kayi min list ɗin kuɗin da ka kashe na biya ka", bayadda Pappy ya iya dole ya yadda JAHMEEL ya siye ma'aikatar agurin shi, akan farashi mafi sauƙi.

Rayuwa na tafiya agurin JAHMEEL yadda ya so, yanzu yayi kuɗi saboda haka ne ya buɗe babbar ma'aikata, wadda a duk faɗin Saudi Arabia ba irinta, tare da taimakon Ummien FAYROZ ya zuba manya-manyan ma'aikata masu inganci, sannan ya siyar da ma'aikatar da mahaifin shi ya gina mishi .

Tun daga lokacin hanyar arziki ta buɗewa JAHMEEL, amma masu karatu kun san JAHMEEL akwai zafin rai, nan kawai AIDAH ke samun matsala amma duk da haka yana kula da ita ɗari wanda hakan yasa bata damu ta tambaye shi ina iyayen su ba, wani lokacin idan yaga dama shi da kanshi yake bata labarin iyayen su, a lokacin ne ta san mahaifiyar ta, ta ɓata ba'a san inda take ba, tun da Mammy ta ɓata ba ranar da JAHMEEL baya zuwa neman ta, rashin Mammy yana ɗaya daga cikin dalilin da ke sa JAHMEEL saurin fushi.
Wannan kenan akan JAHMEEL 🍶

CIGABAN LABARI 👇

Dakin da aka shigar da Mammy nake kallo, Kamar yadda naga JAHMEEL yayi, aiki akeyi, wanda aikin ya ɗauke su lokaci mai tsawo sannan suka gama, bayan angama ne likita yake sheda musu cewa zata farka nan da kwana biyu, dan tana buƙatar hutu da lokaci tayi regaining memory ɗin ta, idan aka ce za'a takura ta to zata manta komai har ƙarshen rayuwar ta, zai fi ku jira ta har ta farka da kanta, JAHMEEL be yi musu ba dan ba abunda yake gudu irin rayuwar ta ɓaci, rashin tuna komai zai wargaza mata rayuwar ta.

Haka kuwa yayi be bari kowa ya dawo asibiti ba, shi kan shi baya zuwa.

Bayan kwana biyu, ya shirya zuwa asibiti, shiga yayi ɗakin, ido ka kafe shi dashi, tabbas wannan ɗanta ne JAHMEEL, har abada fuskar shi bazata ɓace mata ba, zuwa yayi ya kama hannun ta ya rungume, kuka ya fara yi, shafa kanshi take yi, "JAHMEEL ɗana ya kake", ta faɗa tana murmushi, shima murmushi yayi wasu hawayen na bin kuncin shi, tashi tayi zaune ta rungume shi, AIDAH ce ta shigo ɗakin tana kallon Mammy, ɗagowa Mammy tayi sannan tace "JAHMEEL wannan AIDAH ce ƴata? ", "eh Mammy ita ce" ya faɗa, murmushi tayi tace "zo mana ƴata", runguma su tayi su biyu tana jin son yaranta aranta, ita bata bambamta ba, duka so ɗaya take musu.

*********************
KOREA
Faisal ne kwance akan gado tare da wani babban mutum suna sana'ar su, Faisal ya shahara yanzu, manyan mutane ke harka dashi, kuɗi yake samu sosai, banda hormosex ma yana shan giya, shi baya son mace, sana'ar nan ta lalata shi, da ƙanƙancin shekarun shi.

Bayan sun gama ne Alhajin ya ɗauki kuɗi ya bashi masu ɗinbin yawa.

NI KUWA QUEEN NACE ALLAH YA BAKA ARON LOKACI, INA TSORON RANAR DA RESHE ZAI JUYE DA MUJIYA.

**********************
Faheem ne ya shigo gidan, kai tsaye part ɗin maman twins ya wuce, a parlor ya same ta zaune, FAYROZ na mata gyaran gashi, zaunawa yayi "ina wuni maman twins ", "lafiya ƙalau Faheem ya gida", "wallahi gida Alhamdulillahi, ya ƙarin haƙuri ", "haƙuri an gode Allah" ta faɗa can ƙasan maƙoshi dan har yanzu tana jin ciwon kisan da aka ma ɗanta, bawai dan bata yadda ana mutuwa ba, a'a kawai dai saboda kisan, kuma ma ɗan uwan ka, Faheem ya fahimci haka, "Maman twins ina mai baki haƙuri ko kaɗan ban ji daɗi ba ", murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo tace, "Faheem ba komai haka Allah ya tsara bamu isa mu kauce wa hakan ba", shi Faheem duk kunya ta kama shi dan gani yake yi kamar shi ya aika ta kisan kan, FAYROZ ce ta shigo ɗauke da tire ta aje mishi gaban shi sannan suka gaisa.

Ya jima a part ɗin suna fira, ya ji daɗi ba ƙarami ba yadda suka yi fira, dan shi yana son ƴan uwanshi, tare da FAYROZ suka fita, suna fira "yaushe zaki zo gida na "ya faɗa, murmushi tayi tace "duk lokacin da ka shirya koda yanzu ne ni zani", "to shikenan kije ki shirya bari naje na gaida mama sai mu wuce "ya faɗa yana wucewa, haɗa kayan ta tayi.

Parlorn maman shi ya shiga amma bata nan, saboda haka ya wuce ɗakin ta tura ƙofa yayi ya same ta kwance tana barci, zaunawa yayi a hankali yana yana matsa mata ƙafa yana mata tausa, buɗe ido tayi sannan tace "nagode Faheem, Allah ya maka albarka "murmushi yayi yace "ameen ya rabbi"

DARASI :DUK YADDA HALIN MAHAIFIYAR KA YAKE KAR KA GAZA GURIN MATA BIYAYYA DOMIN ALJANNAR KA NA HANNUNTA, ITA KUSKUREN TA DABAN WANNAN TSAKANIN TA DA MAHALICCIN TA NE, KAI MA KA GYARA TAKA ALAƘAR DA UBANGIJI TA HANYAR MATA BIYAYYA KODA BATA SO.

"Ashe ka shigo ni ban ma sani ba "ta faɗa tana saukowa daga kan gado, "eh na shigo ban same ki", fira sukayi kafin yace zai wuce, to kai gyada min mai gida na Jaalal (daddy), cewa da jikanta wanda yaci sunan kakan shi amma suna ce mishi daddy, to zai ji insha Allah.

ANAN ZAN DASA AYA MASU KARATU✍️..........
MU HAƊU A NEXT CHAPTER.

LOVE U ALL.💃💞💞💞💞
SADAUKAR WA GARE KI MRS JAMEEL ❤️💓💓ALLAH YA BAR TARE.

ALQALAMINA NE💃💃💞

TSARA LABARI: QUEEN NASMERH 👑💞💞💞💞

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️💓💓💓💓💓💓💓💓💓

FAYROZ❤️❤️Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt