Chapter 506-600

21 0 0
                                    

💮💮💮💮💮
                     FAYROZ
           💮💮💮💮💮💮

Tsara labari da rubutuwa : Queen Nasmerh
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

Chapter 506-600
***********************************
    Kowa a parlor sai farinciki yake yi, Abbu yayi gyaran murya, sannan yace “ kuma ina so na ƙara sanar da ku wani albishir ", Farzana tace “mu na jinka Abbu", murmushi yayi yace “ina so na sanar da ku auren ƴata Fayroz satin nan mai zuwa ", dummmmm! Gaban Fayroz ya faɗi, Faheem yace “Abbu wanene mijin nata", Papa yace “wani saurayi ne kyakkyawa muka samo mata, yana cikin nigeria", dariya aka sa duka, Abbu yace ma papa “kai kuma sai ƙoda shi kake yi ", Ummie tace “ya bazai ƙoda mana surukin mu ba", Abbu yace “yanzu dai shikenan, abunda nake so ku sani shine kowa ya fara shirye-shiryen biki, kowa ya siye kayan biki, ranar biki ta fara daga yau, zuwa jibi za'a ɗaura aure ", Jahmeel yace “amma Abbu sai kace auren ƴar tsana, to saurin me ake yi, ni fa ban yadda da auren ba sai naga mijin, in na yadda da halin shi to za'a yi auren, idan ban yadda ba baza'a yi ba", FAYROZ kuwa tuni idonta ya kawo ruwa, tashi tayi ba tare da kowa ya lura ba ta fita, Abbu yace “sannu mai ƙanwa, to mijinta ba wanda ya kai shi hali mai kyau, ka tsaya ka gani kai ma zaka ji daɗi haɗin da za'a yi, Jahmeel yace “idan be min ba ni dai na faɗa muku bazata aure shi ba, Mahboob zan bawa ", Mahboob yace “ka manta biri zaka ba, ba Mahboob", duka ɗakin aka sa dariya, Mammy tace “kai fa Mahboob baka jin magana ", Ummie tace “surukin nawa ne baya jin magana", Faheem yace “Abbu to wace rana za'a ɗaura auren? ", Abbu yace “ranar Juma'a", nan aka dinga labari ana fira.

Jahmeel ne ya fara tashi ya fita, part ɗin Ummie ya nufa, duk jikinshi na mishi ciwo, da sauri ya nufa ɗakin shi, wanda ɗakin yake kusa da na Fayroz, sautin kuka yake ji, kamar bazai buɗe ɗakin ba, sai kuma ya canza ra'ayi ya buɗe, shiga yayi inda ya ganta tsaye gaban Window, sai kuka take yi, “Fayroz "ya kira sunanta a hankali, juyowa tayi dan bata yi tunanin zata ganshi a irin lokacin nan ba, “kukan me kike yi?" ya sake tambaya ganin tayi shiru ba amsa, da sauri ta share hawayenta tace “ babu komai ", kallonta Jahmeel yayi yace “idan kika ɓoye min damuwar ki wa zaki faɗa ma?", shiru tayi bata ce komai ba, yace “ faɗa min kina farinciki da auren", cikin rashin sani taji wasu hawaye masu zafi suna zubo mata a fuska, girgiza mishi kai tayi alamar a'a, Jahmeel yace “miyasa baki faɗawa su Abbu ba ", cikin kuka tace “saboda naga suna farinciki da haka, bana so na ɓata musu farincikinsu" hannun shi ya kai kan fuskar ta ya share mata hawaye, “yanzu faɗa min wa kike so? ", shiru tayi bata ce komai ba, dan ita Jahmeel take so kuma kunya bazata bari ta gaya mishi, da sauri ta juya, juyo da ita yayi da ƙarfi, ta matso daf da shi har tana iya shaƙar numfashin shi, yace “na fahimta", FAYROZ tace “me ka fahimta? ", Jahmeel yace “na daɗe da fahimtar kina so na" dummmmm! Taji gabanta ya faɗi, Jahmeel yace “bazaki iya zama dani ba, saboda ni ba soyayya a zuciya ta, dan haka ki manta da ni ki auri zaɓin su Abbu, zai fi miki", wasu hawaye ne ke bin kuncinta tsabar takaici ta kasa cewa komai, Jahmeel yace “ni zan wuce ki kwana lafiya ", wucewa yayi tare da rufe mata ɗaki.

    Tun daga wannan ranar Fayroz ta sa a ranta zata haƙura ta auri zaɓin su Abbu, amma can ƙasan zuciyar ta tana son auren Jahmeel, amma miye amfanin auren wanda baya sonka, ita ta san Jahmeel baya sonta, dan ko a jikinshi auren da za'a mata, a ƙarshe ma shi ne yake kawo kayan da za'a raba ma baƙi, kuma shi ya ɗauki nauyin abincin biki, a cewar shi su Abbu na da yara bai kamata su kashe kuɗin su ba, kuma duk su Fahad sun yadda da haka, shiyasa suka saki jiki suna ɓarnar naira yadda su ke so, ba wasu baƙi bane, ƴan uwan su ne na saudi arabia, yau za'a yi arabian night, kuma Abbu yace banda ango, kawai da amarya ce, tunda angon malami ne shi bazai iya zuwa irin event ɗin ba, basu damu ba, amarya tasha kyau, dan takanas ta Kano aka yi order daga saudi arabia, rigar tayi matuƙar yin kyau ash ce mai duwatsu ta ko ina black, ƙasan rigar kuwa ya baje sosai, sosai take ja a ƙasa, amarya tayi kyau sosai, rolling tayi kamar yadda su ka saba a saudi arabia, haka kuma ba ƙaramin kyau ya mata ba, mazan gidan duka ash ɗin kaya suka saka, mata kuma black, sai haka ya ƙara ƙayatar da gurin, decoration ɗin gurin kuma fari ne da ɓaki, gurin yayi matuƙar yin kyau, sai waƙoƙin Larabawa ke tashi, Mahboob kuwa bai san lokacin da ya fara rawa ba, ai kuwa nan take kowa ya hau rawa, Jahmeel ba mutum bane mai son rawa dan haka kuɗi kawai yake watsa musu, dollars da naira dan yasa an mishi canjin nerori, amarya ta fito gaban stage ɗin aka shiga watsa mata kuɗi, gurin an taru sosai, a government house aka yi taron, hotuna aka shiga yi, ko ina flash kake gani, bikin ya ƙayatar sosai, Jahmeel sai tsokanar su Fahad yake yi wai ƴan nigeria sun ga bikin Larabawa sai zaƙewa su ke yi (ni kuwa nace Nabi Larabawa da gudu........ 😂) anci ansha an gode ma Allah, abun yayi matuƙar yin kyau, kuma an zuba kuɗi, dan Abbu yana gurin, ba'a watse ba sai ƙarfi uku na dare , a haka ma ba dan anso ba, dan ko ni ban so aka watse ba naso mu kai asuba gurin, amma gajiya da barci fa, gashi gobe za'a ɗaura aure , taron mutanen da ke gurin yasa Alƙalamina faɗuwa idan na tsaya ɗauka za'a iya take ni musamman Mahboob da naga sai rawar kai ya ke yi, saboda haka zan dasa aya anan............✍️

ALQALAMI YAFI TAKOBI

FAYROZ❤️❤️Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin