Chapter 601-605

22 1 0
                                    

💮💮💮💮💮
                     FAYROZ
           💮💮💮💮💮💮

Tsara labari da rubutuwa : Queen Nasmerh

https://www.wattpad.com/user/QUEENNASMERH08?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

Chapter 601-605
***********************************

Cikin gida su ka nufa kan Jahmeel na mugun sara mishi kamar ya fashe, dan shi duk ya shiga taro mutane sai yayi ciwon kai, kayan jikin shi ya shiga ragewa sannan yayi wanka, kan gado ya kwanta yana mita “wai ace baza'a sauke ma mutum aiki ba, tun da safe za'a ɗaura aure kamar an gaji da mutum, su Abbu sai rawar kai su ke yi sai kace sun gaji da ita "ya ƙarasa maganar yana jan blanket.

    A ɓangaren Fayroz kuwa gwaggon ta wato Mammy ta mata wanka da ruwan madara, sannan aka sata lalle, sai kuka take yi wai ita ba'a sonta shiyasa za'a mata aure a gidan, ba wadda aka ma aure da wanda bata sani ba, ba wanda ya kula ta dan a cewar su ita  da kanta zata zo godiya.

Washe gari da safe, tun da misalin ƙarfe 9:00 ƴan mazan su ke fita sun ɗau wanka, kowa ya kashe kuɗi gurin auren, tare da su Abbu su ka nufi masallacin gidan, Jahmeel sai wani shan ƙamshi yake dan shi ya tsani shiga mutane, shi ya matsu ma a gama bikin nan yau ko gobe ya bar ƙasar, Nigeria ga cunkoson mutune kamar ƙudaje ya faɗa a ranshi.

   Cikin masallacin cike yake, Jahmeel sai raba ido yake ya ga angon amma ina, shi ya kasa gane wanene angon, gashi kusan kowa a gurin ya ɗau wanka, har ma da dangin mijin Fayroz kamar yadda yaji ana faɗa, zaunawa yayi kusa da Abbu, tare da jingina kanshi a bayan bango, rufe idon shi yayi, a hankali yana ji ana maganar waliyan amarya, dana ango, ji yayi ance an ɗaura auren ƴar lelen his excellency, ƴar gwamna wato FAYROZ JALEEL da angon ta JAHMEEL LATEEF, akan sadaki dubu ɗari bakwai, da sauri ya buɗe idon shi yana kallon ko ina, a rikice yake, cike da rashin lafiya fahimta yake bin mutane da kallo, su Fahad ma da kallo su ke bin su Abbu, duk a rikice suke suna so su san wane Jahmeel ɗin, ni kuwa Nasmerh nace ta faru ta ƙare sata a gidan me gari.

     Nan makiɗa da maroƙa suka yo ambaliya kowa yana abunda ya dame shi, Jahmeel kuwa miƙewa yayi tsaye, Abbu ne ya bishi,  Papa ma da su Fahad bin bayan su suka yi, mutane sai kirari ake wa Jahmeel, cikin ɓacin rai ya dinga musu ruwan kuɗi, kawai zuba musu yake yi dan shi be ga dalilin da yasa za'a mishi aure ba'a faɗa mishi, a cikin su ba wanda zai zauna mishi da mata, to miyasa zasu mishi aure, ranshi a ɓace ya shige gida, makiɗa da maroƙa kam kakar su ta yanke saƙa dan ba ƙananan kuɗi Jahmeel ya zubar ba.

   A ɓangaren Fayroz kuwa tana parlor zaune, sanye take da wani less golden yayi matuƙar yin kyau, takalmin ta da jakar ta ma golden ne, kamar yadda al'adar larabawa take, a ranar da za'a ɗaura aure amarya zata zauna a parlor tare da dangin ta, a yi ta kaɗe-kaɗe da bushe-bushe har ƙarfe huɗu, wayar Mammy ce tayi riging, “hello Papa Jahmeel ", banji me yace ba sai ji nayi tana cewa “alhamdulillahi, an ɗaura, to Allah basu zaman lafiya, Allah yasa su mana biyayya", Ummie da ke gefe tace “har an ɗau a? ", Mammy tace “an ɗaura" , FAYROZ kuwa ta rasa me ke mata daɗi, yau ya kamata ta zama ranar farincikinta amma idan ta tuna Jahmeel sai ta ji ina ma ace bata kawo yanzu ba, Mammy tace “Mrs Jahmeel LATEEF congratulations", da kallo Fayroz ke kallon Mammy, kamar yanzu taji ta kirata da Mrs Jahmeel Lateef, Mammy zata yi magana kenan, Jahmeel ya shigo ranshi a ɓace ya wuce, Abbu ne ya biyo bayan shi, dai-dai lokacin su Fahad su ka shigo, ɗakin da Jahmeel yake suka shiga, da sauri Ummie ta tashi ta bi bayan su Mammy na tashi tayi su ka nufi hanyar da suka bi.

     “Haba Papa ya zaku min haka "Jahmeel ya faɗa lokacin da Papan shi ke ƙoƙarin yin magana, Papa yace “kayi haƙuri kawai dai mun yi tunanin duk hukuncin da muka yanke dai-dai ne", Jahmeel yace “idan fa bana sonta ", Papa yace “nasan bazaka ƙi zaɓin mu ba", Jahmeel yace “ ni bana son........ "be samu ƙarasawa ba sanadiyyar wata razanannar tsawa da yaji Mammy ta daka mishi “eh na yadda ni da mahaifinka bamu muka raine ka ba, amma kuma mu muka haife kuma, ni ban haife ka dan ka ja dani ba, ni na bada shawarar yin auren ba tare da an faɗa maka ba, kai wanene da zaka ja da hukuncin mu, na zaɓi Fayroz a matsayin suruka dan haka ko kana so ko a'a dole ka zauna da ita, shashanci banza kawai ", wasu hawaye masu zafi suka zubo mishi a kunci, dan a rayuwar shi, ko lokacin da yana ƙarami Mammy bata taɓa ɗaga muryarta a kanshi ba, yau gashi saboda Fayroz Mammy tana mishi faɗa, wasu hawaye masu suka wanke mishi yace “ni bana sonta Mammy, kuma bazan iya son kowa ba, bana son kowa, kuma bazan so ba, ita ɗin kawai ƙanwa ta ce "ya, ƙarasa maganar tare da shigewa toilet, da ƙarfi ya rufe toilet ɗin tare da sa mukulli ya rufe, haka da kayan jikin shi ya sakar ma kanshi ruwa, hawaye masu zafi ne bin kuncin shi, amma saboda ruwan da ke sauka kanshi ba zaka ce yana kuke ba, cikin ƙunar rai da ƙunci yake, shi bawai baya sonta ba, amma bazai iya aure ba, ya kamata su Mammy su fahimta, shi baya so ya shiga haƙiƙƙin Fayroz dan yasan bazai iya kula da ita ba, shi kuma yafi so ta auri wanda zata ji daɗi shi, FAYROZ kuwa tana tsaye duk zancen da ake yi, ganin Jahmeel ya shige toilet yasa ta tura ƙofar ɗakin ta rufe, wanda haka yasa kowa juyowa, da gudu ta nufi ɗakinta, su Ummie ne suka bi ta da saurin su.


Anan zan dasa aya.............. ✍️

ALQALAMI YAFI TAKOBI.
   

FAYROZ❤️❤️Where stories live. Discover now