Chapter 211-215

52 2 0
                                    

💮💮💮💮💮💮
FAYROZ
💮💮💮💮💮💮

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*
**********************
Page 211-215
************************
FAYROZ ta shirya tsaf, tayi kyau sai ƙamshi take yi, Faheem ne ya fito daga ɓangaren mahaifiyar shi, tafiya yake yi cikin ƙasaita, kayan jikin shi sun wanku , yayi matuƙar yin kyau, Faheem yafi duk samarin gidan kyau, ɗauke da murmushi a fuskar shi ya ƙaraso.

"Muje "ya faɗa, mota suka shiga, "sister kin zo garin amma baki san wurare ba, gobe da safe zamu je yawon buɗe ido", FAYROZ ta ji daɗi sosai dan dama tana so tasan yadda gari yake, basu wani jima a mota ba, suka yi parking gaban wani katafaren gida, ƙerararre, da murmushi ya kalle ta yace "this is my house ", murmushi tayi itama, tace "masha Allah".

NI KUWA NACE HARKA TAZO GURIN LARABAWA DOLE ACE MASHA ALLAH 😂😂😘

---------------------------------
A parlor ya same matar shi, Rumaisa zaune, Adnan kwance a cinyar ta, "sannu da zuwa baban Adnan ", "yauwa, maman Adnan, hala rigima ya gama shine yayi barci", " kaima ka sani Adnan bai da aiki sai rigima ", murmushi yayi sannan yace "yanzu ba wannan ba, ga yaya ta da nake faɗa miki FAYROZ amma aunty za'a ce mata ", dariya Rumaisa tayi tace "ai dole muce aunty, bisimillah babba Aunty ga guri ki zauna ", zaunawa FAYROZ tayi, kusa da Adnan tana shafa fuskar shi, tashi Rumaisa tayi, kitchen ta nufa, dan ɗaukowa FAYROZ abun motsa baki.

*************************
JAHMEEL ne kwance a cinyar Mammy, sai shagwaɓa yake mata, AIDAH tace "ni fa yaya ka hanani naji ɗumin Mammy, sai wani liƙe mata ka ke yi kamar wani jariri ", yi yayi kamar be ji me take faɗa ba, Mammy ta shafa kanshi tace "zan so inga matar ka", MAHBOOB yace "waye zata iya da shi, sai dai mai coffee "ya ƙarasa maganar cikin sigar zolaya, Mammy tace "kai MAHBOOB bana son shaƙiyanci ɗan nawa kake cewa sai me coffee, ka fita ido na",murmushi MAHBOOB yayi yace "Mammy ai shi JAHMEEL ya san wacece me coffee ", JAHMEEL da ke kwance rufe ido yayi kamar bashi yake ma Mammy shagwaɓa ba.

AIDAH tace da MAHBOOB "HABEEBY wacece me coffee dama, akhi yana da budurwa", MAHBOOB riƙe dariyar shi yayi sannan yace "wata yarinya ce kyakkyawa ajin farko, saboda son da yayan ki ke mata, ya maidota office ɗin coffee, saboda ya riƙa kalle ta ", dariya AIDAH tasa, Mammy murmushi tayi tace " ɗana wacece ita da baka faɗa min ba", JAHMEEL yace "ni ba son kowa ce mace a raina, in fact ma ni ba aure a cikin tsarina "tashi yayi zai fita, MAHBOOB yace "kafi ruwa gudu in ka je, mutum sai zuciya kamar guguwa, ni na tausaya maka lokacin da me coffee zata gasa maka aya a tafin hannun ka", hakan ba ƙaramin ɓatawa JAHMEEL rai yayi ba, ranshi ya ɓaci, idon shi har wani ja suka yi, ɗaki ya wuce yana jin haushi, wacece FAYROZ har da zata gasa mishi aya a hannu.

Mammy tace "kunga muna firar mu kun kore shi ", dariya AIDAH tayi tace "ni dama ya tare min guri" dawowa tayi kan cinyar Mammy, gashin kanta Mammy ke shafawa, MAHBOOB yace "kin min kishiya kenan ", AIDAH tace "a'a fa, ai kai daban Mammy daban",fira suka yi, dare ya soma yayi ƙarfe 10:50 na dare, saboda haka AIDAH da MAHBOOB suka wuce ɗakin su, Mammy kuwa ɗakin JAHMEEL ta nufa.

Kwance yake, har yanzu yana jin takaicin abunda MAHBOOB ya faɗa, miyasa abun yake damunshi, shi be san meyasa ba, idan MAHBOOB be ɓata mishi rai ba, baya jin daɗi.

Jin motsin ƙofa yasa shi saurin rufe ido, zuwa tayi ta zauna, jin ƙamshin turaren Mammy yasa shi jin daɗi har cikin ranshi, da ya ɗauka MAHBOOB ne ya shigo.

Kanshi ta shafa, buɗe ido yayi, murmushi ya sakar mata, "JAHMEEL yaushe zaka rage zafin zuciya ", shiru yayi, shi kanshi baya son halin nan nashi, Mahaifin shi ne ya ja, Mahaifin shi ne ya wargaza mishi farincikin shi, yanzu abun ya zamar mashi jiki, shi kanshi be san lokaci ba.

"Zuwa yanzu ya kamata ka yafe wa Mahaifin ka ka koma gare shi" Mammy ta faɗa, "Mammy ni bazan koma ga Pappy ba, har sai ya karɓi AIDAH a matsayin ƴar sa, miye dalilin shi na ƙin mata ", shiru Mammy tayi na ɗan lokaci kafin tace, "JAHMEEL komawa gare shi yafi alkhairi, ba'a fushi da iyaye ko ya suke, shi ɗin mahaifin ka ne, sannan kuma zaka iya koya mishi son AIDAH, beside ma, AIDAH ba ƙarama bace, ta girma, kuma ta mallaki hankalin ta, itama yanzu zata gina ahalin ta, saboda haka ba dole bane sai ya so ta, tana da ni ko ba komai, kuma ai bata taɓa ƙorafi, ko lokacin da bana nan tana farinciki, saboda kai ka zame mata uba, ka zame mata uwa, ina alfahiri da kai, Allah ya maka albarka, nagode da tarbiyar da ka mata tun kuna yara AIDAH bata da hali mara kyau.

Ka bata farinciki da rayuwa, nasan har abada kai take kallo a matsayin mahaifi, to ya rage nashi ya so ta ko a'a, amma itama ta bi shi, kafin su wuce Dubai kuje kai da ita, ko be kula ta ba, ai ita ƴar shi ce, ta fitar da haƙƙin ta a matsayin ƴa, saura nashi, wanda nake da tabbacin zai karɓe ku hannu biyu ko ba yau ba, komai na rayuwa lokaci gare shi, rayuwa zata baka farinciki ta baka baƙinciki, rayuwa ba abunda bata sawa, duniyar nan cike take da mutane daban daban, ina so ka ɗauka haka taku ƙaddarar tazo kuma ko ba yau ba zaku wuce wannan, kar ka cire rai ".

Murmushi yayi tabbas yayi kuskure da ya ƙulla gaba da mahaifin shi, yanzu da Mammy ta tunatar da shi zai gyara "nagode Mammy", "ba komai JAHMEEL ka kwanta, asuba ta gari "ta faɗa tana mishi kiss a goshi, rufe ido yayi bece komai ba, lulluɓe shi tayi sannan ta kashe fitilar ɗakin, rufe ɗaki tayi sannan ta wuce ɗakin ta.

**************
FAYROZ tana zaune a parlor tana kallo, Adnan ya tashi, kallon ta yake yi yana mamaki ina suka samu me kama da Aljanu aranshi ya ke faɗa, kallon parlorn yake yi ba kowa ciki, daga shi sai FAYROZ, shi be taɓa ganin mutum me kyau da hasken fata irin ta ba, dan haka ya sa ihu, da sauri Faheem da Rumaisa suka fito daga kitchen, dan Faheem yanada wannan halin in dai yana gida to baya barin matar shi tayi aiki ita kaɗai.

Ihu Adnan yake yi ba tsaya, Rumaisa tazo ta rungume shi, "me ya same ka ɗana ", "aljana" ya faɗa yana nuni da FAYROZ, wadda tun da ya fara ihun take kallon shi, ta fahimci tsoron ta yaji shiyasa ta ƙi matsowa kusa da shi.

Murmushi Rumaisa tayi tace " waya ce maka aljana ce ", "to ba naga ita fara ba ce sosai kuma tana da kyau sosai" ya faɗa yana turo baki, Rumaisa tace "ai wannan Aunty FAYROZ ce, yayar baban ka ", washe haƙora yayi yace "dagaske", gyaɗa mishi kai tayi sannan tace "maza je gurin ta ku gaisa", Faheem da ke tsaye juyawa yayi, aranshi yana mamakin Adnan, shi dai burin shi kawai yayi kuka.

Rungume FAYROZ tayi tace "sorry Aunty ta tsorata ka ko ", shigewa yayi jikin ta, kamar me barci.

***
ANAN ZAN DASA AYA.........
SAI KUN JINI

LOVE YOU ALL
THANK YOU SO MUCH FOR THE COMMENTS MY READERS, KUNA ƘARAMIN ƘWARIN GUIWA.

NGD SOSAI 💞💞💞
KUSANI A ADDU'A PLSSSS INA EXAMS NE 🙏🙏

TSARA LABARI :QUEEN NASMERH 👑💗💗💗💗

ALQALAMI NA NE 💃💃💃💃💗🎉

FAYROZ❤️❤️Onde as histórias ganham vida. Descobre agora