Chapter 56-60

27 3 0
                                    

💮💮💮💮💮💮
FAYROZ
💮💮💮💮💮💮

MALLAKIN ;
ASMA'U NAANERH (NASMERH) 💗💗💗💗💗💗💗
&
FATIMA USMAN BAUCHI 💕💕💞💞💞💞💞






✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*
************

Page: 56-60

Wanka FAYROZ tayi, kayan ta da aka shigo mata dasu ne ta buɗe, wata doguwar riga ta saka, sannan ta fito parlor, abinci ta samu an jera mata kala-kala, murmushi tayi, sannan ta fara buɗe kulolin abincin , zuba wa tayi sannan ta fara ci, bayan ta gama ne aka haɗa komai masu aiki suka fitar dashi.

Abbu ne ya shigo, tana zaune a ƙasan kujera tana danna waya, zaunawa yayi ta bayan ta ya ɗaura hannun shi yayi akanta yace "love kin gama ".

NI KUWA ASMA'U MAMAKI NE YA CIKA NI, WAI LOVE, KAI ABBU AKWAI IYAYI.

Gaɗa kai tayi alamun eh, murmushi ya saki mai sauti yace " ki daki jikinki nan kamar gida kike", itama ɗin murmushi ta sakar mishi tace"insha Allah Abbu ", "yauwa love yanzu kije ki kwanta, zuwa gobe zan baki labarin, yanzu ankira ni meeting ne, dafatan ƴata batayi fushi ba ", "ba damuwa Abbu, adawo lafiya "tashi yayi ya tafi badan yaso ba.

Fitowa tayi daga part ɗin ta, yaran da ta gani jiya tweens ne ta samu a compound ɗin gidan, kamar jiya dai yau ma wasa sukeyi.

Zuwa ta zauna tana kallon su, sun burge ta matuƙa, faɗa suka fara yi, dasauri ta tashi, "little tweens, me yake faruwa nan "ta faɗa, da kallo suke binta, murmushi ta sakar musu, yaran mamaki sukeyi ina suka samu wannan matar me kyau, anya mutum ce, Fareed ne yace wa Farhan "Farhan ni dai mu gudu baruwana kar ta sace mu" Farhan takaici duk ya kama shi, "kai Fareed kacika tsoro, ya za'a yi ta sace mu ", faɗaɗa murmushinta tayi tace "ni aunty ku ce, suna na FAYROZ", "laaaa aunty ke Balaraba ce, wannan sunan lararabawa ne ", Farhan yace "ina ruwanka da inda take".

FAYROZ tace "duk ba wannan ba, yanzu ku, faɗa min me ya haɗa ku faɗa ", Fareed yace "Aunty Farhan ne yake tsokana na, wai banda kyau", murmushi tayi saboda abun su abun ayi dariya ne, yaran da suke kama ko minene na faɗa dan ance baka da kyau, shafa kan Fareed tayi tace "Injiwa, u are d most handsome boy on earth "(kafi kowane namiji kyau a duniyar nan),kallonta yakeyi, tace "dukanku kuna kama kuma kuna da kyau", Farhan yace "amma aunty nafi shi kyau ko? ", "kowa yafi kowa kyau, yanzu ku daina faɗa ba kyau", Fareed yace "aunty zaki bani ice cream ", "eh zan siya maka, amma ku dai na faɗa, "zaki siya min chocolate" Farhan ya faɗa ", FAYROZ tace "duk abunda kuke so zan siya muku amma da sharaɗi bazaku sake yin faɗa ba", amsawa sukayi da eh a tare.

*****************
Ummie damuwa ta dameta, Allah yasani tana kewar FAYROZ amma ba yadda ta iya, wannan itace gaskiyar, yanzu FAYROZ ta mallaki hankalinta, duk inda take zata iya kula da kanta.

Hawaye ne ke bin kuncin Ummie, ta yanke hukuncin da yanzu yake damunta, bata san ya akayi ba, amma abun yana damunta.

*****************
DALEEL

Yau yayi wata ɗaya kenan a Cyprus, amma ba abunda ya canza na soyayyar da yake wa FAYROZ, me maimakon abun yayi sauƙi, abubuwa ƙara jagule mishi kawai sukeyi.

Kwance yake wata kujera da aka ajiya agurjn swimming pool, wata yarinya na gani budurwa, tafiya takeyi da alamu ba ƴar ƙasar bace itama zuwa tayi.

Ta bayan DALEEL ta zagayo ta rungume shi, rufe idon shi yayi dan ji yake kamar ana zuba mishi wuta a jikin shi, shi duk macen da zata raɓe shi, in dai ba FAYROZ bace to baya so.

Haleematu kuwa tun ranar da ta ɗaura idon ta akan DALEEL, ta kasa samun natsuwa, bata da wani burin da ya wuce ta samu zuciyar shi.

Amma ko kaɗan baya bata lokaci, ballantana ayi maganar samun zuciya.

"My man, ashe kana nan, kasani wahala tun ɗazu ina ta faman neman ka ",ko kallo ta beyi ba dan shi abunda ke damun shi ya ishe shi, "haba DALEEL, gurin ka fa nazo, amma kake min wannan abun" Haleematu ta faɗa tana zaunawa kusa dashi, "kiyi haƙuri Haleematu, bana jin daɗi ne "ya faɗa, dan baya so yaga ya cutar da me sonshi, saboda yasan yadda ake ji idan aka cutar da mutum.

*****************************
Ta ɓangaren JAHMEEL kuwa yayi tafiya India gurin haɗa kayan bikin ƙanwar shi, dan acewar shi komai shi zai haɗa.

Yau zai dawo, dan saura kwana biyu ayi Arabian night.

***********
Aidah da MAHBOOB kuwa, suna ta faman shirye - shirye, biki ne za'ayi na kece raini acewar MAHBOOB, banda JAHMEEL da shi aure ko ajikin shi.

Aidah ce zaune a parlor tana tunanin yadda zatayi ta ba yayanta last gift of her life, dan ya dinga tunawa da ita, tashi tayi ta fita, wani mall taje ta haɗa mishi wani gift na flowers, flowers ɗin are very expensive, masha Allah, sannan ta siya mishi wani wrist watch, shima agogon mai tsada ne sosai .

******************
Da daddare jirgin JAHMEEL ya sauka, alhamdulillahi, ya sauka lafiya.

Yana zuwa gida ya tadda varieties ɗin abinci kala-kala, (masha Allah masu karatu ko ni kaina I can't wait naci).

Wanka yayi sannan yazo yaci abinci, kaɗan ba wani sosai ba.

Yaji daɗi matuƙa, saboda yadda ƙanwar shi ta tarbe shi, murmushi yayi amma be kai ciki ba, yace "Aidah, kice MAHBOOB ya huta kin ƙara ƙwarewa ", "hmmmm, wai ya huta, harda kai ka huta ai", murmushi kawai yayi, sannan ya ja ta suka shiga cikin ɗaki, kayan daya siyo mata yanuna mata, sannan ya shaida mata, kayan da ɗakin ta an wuce dasu Dubai, kasancewar can zata zauna, "ohk nagode sosai kai ɗin ubane a gare ni, nagode da kulawar ka gare ni ", "shafa kanta yayi yace "karki damu wannan ɗawainiya ce akaina, Allah ya barki ke da mijin ki", "ina zuwa akhi "Aidah ta faɗa sannan ta wuce zuwa ɗakin ta, wani box nagani yayi kyau anyi rapping ɗin shi in black and white, yayi kyau sosai sai ƙyalli yakeyi.

Ɗakin ta dawo, miƙa mishi tayi tace "wannan na ka ne", da murmushi yace "wow! 😯 duk ni kaɗai ".

"eh mana yaya u deserve more than this" (ka can-can-can-ci fiye da haka "

Rungume ta yayi "I love you so much Aidah", "I love you more, and am gonna miss u"Aidah ta faɗa.

*******

FAYROZ

Tana zaune..........

VOTE
SHARE
AND COMMENTS
PLSSS 🙏

HAƊIN GUIWAR
QUEEN NASMERH & FATY USMAN 🌼🌼🌼🌼🌼.

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂

FAYROZ❤️❤️Where stories live. Discover now