Chapter 401-405

22 3 0
                                    

💮💮💮💮💮💮
                     FAYROZ
           💮💮💮💮💮💮

Tsara labari da rubutuwa :Queen Nasmerh
https://www.wattpad.com/user/QUEENNASMERH08?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
Chapter :401-405
************************************

Kamar yadda aka tsara haka ta kasance ƙarfe biyar aka ɗaura auren Jalal da Ghushan inda aka ɗaura auren a masallacin gidanta, duk su Jahmeel suna gurin, tare aka haɗa shagalin auren dana Janeesa, inda aka ƙawata wani babban hall da ke cikin gidan su Fayroz, anci ansha an gode ma Allah.

    Yanzu Jahmeel ya gane miyasa yake jin yana so ya kusanci Fayroz ashe ƴar uwar shi ce, zaune take akan wata kujera dake bayan gidan, dan idan taga taron mutane hankalin ta tashi yake yi, haka yasa bata zama a gurin da taro yayi yawa, Jahmeel dake cikin gida wayar shi tayi ringing fitowa yayi da niyyar ansa wayar dan hayaniya tayi yawa sosai, wannan dalilin ne yasa ya za gaya bayan gidan domin yin waya.

   Da ido ta kafe shi, jin kamar ana kallonshi yasa shi saurin juyowa, karaf suka haɗa ido da juna, kallonta yake bai sauke ido ba kuma bai ƙaraso inda take ba, har yanzu waya yake yi, yayinda kunya ta rufe Fayroz ta durƙusar da kanta, murmushi kawai ta ke yi wanda ita bata ma san tana yi ba, ɗagowar da zata yi taga babu kowa gurin har ya gama wayar ya tafi abun shi, wani haushi taji miyasa zata kalle shi, gashi shi be ma damu da ita ba, tashi tayi cikin fushi ta bar gurin juyawar da zata yi taji tayi karo da mutum buɗe idon ta ta shiga yi a hankali ta sauke su akan fuskar Jahmeel, da sauri ta sake rufe ido, a hankali yace “ki riƙa lura da hanya ", rufe fuskarta tayi tare da barin gurin cikin sauri, shi kuwa gogan na mu Jahmeel ɗage kafaɗa yayi irin shi be damu ba.

    Da sauri ta shiga cikin gida, ɗaki ta nufa, “Fayroz" Abbu ke kiran ta, amma taƙi tsayawa, Jahmeel ne ya shigo dai-dai lokacin yana kallon inda Fayroz ta bi, Mammy ce ta bi Fayroz da kallo sannan ta kalli Jahmeel, murmushi tayi tace ma Papa “ya kake ganin auren Jahmeel da Fayroz ", murmushi yayi yace “abunda na ke tunani kenan", Abbu ma magana yayi wa Ummie yace “kin lura da Fayroz kuwa, anya ba wani abu tsakanin su da Jahmeel ", Ummie tace “bansani ba, amma tayi aiki a ma'aikatar shi ai", Abbu yace “wannan abu ne mai kyau, zai iya yuyuwa sun ƙulla alaƙa", Ummie tace “wace alaƙa kenan ", Abbu yace “soyayya mana, ke baki ga yadda ya ke kallon ta ba, ita ma ɗin kunyar shi take ji", Ummie tace “haka zai iya yuyuwa", Jahmeel ne ya zo ya zauna inda su ke, Mammy sai kallon shi ta ke yi, Mahboob ne da ke zaune yace “ka gama soyayyar da me kyau " da ƙarfi yayi maganar yadda kowa zai iya ji, Mammy tace “wacece mai kyau?", murmushi yayi yace “Fayroz mana ", Jahmeel yace “ka kama kanka fa", Abbu yace “ƙyale su ɗana in ma soyayyar ce ai kun kai ", Mammy tace “soyayyar ma ce", Abbu yace “ya aka yi kika sani? ", “shi ne ya faɗa min" ta faɗa tana kallon yanayin Jahmeel, “kai Mammy ni yaushe na yi da ke "Jahmeel ya faɗa, Mahboob yace “ko baka faɗa mata ba ai ka faɗa min a gurin aiki, ka tuna ranar", tsabar takaice kasa yin magana yayi, “ku bar min yaya na fa "Aidah ta faɗa, Lateef yace “ki bar su sun samin yaro gaba", tashi Jahmeel yayi ya bar gurin, dan in ya cigaba da zama ran kowa zai ɓaci, har ga Allah shi ba son Fayroz ya ke ba, a taƙaice ma mamakin yadda take jin kunyar shi yake yi.

   A ɓangaren Fayroz kuwa, kan gado ta faɗa tare da rungume pillow, murmushi ta saki mai sauti, a hankali tace “ƙamshin shi mai daɗi ne"rufe ido tayi lokacin da take jin kamar yana ko ina ta gefen ta, bata san miyasa ba amma bata taɓa jin irin yanayin nan ba, to me haka ke nufi, kenan?.

   FAISAL*****************

Rayuwa tayi wa Faisal zafi, Maman shi ma yanzu ta fara damuwa , sai kuɗi ake kashewa domin samun lafiyar shi amma ina abun yaci tura, ta tura shi ƙasashe da dama domin neman lafiyar shi, haka yasa ta yanke hukuncin Fahad yaje can ya ɗauko mata shi, amma fir Fahad ya ƙi zuwa, gashi Faisal ba abunda zai iya yi, kuɗi ta biya akan a dawo da shi, wanda yau insha Allah yana hanya.

   Yau su Ummie zasu dawo Nigeria inda Abbu ya bar Fayroz gidan Janeesa akan next week zasu zo ita da Jahmeel.

Saukar jirgi ke da wuya yayi dai-dai da zuwan motar ƴan sanda, inda su ka samu labarin Faisal zai dawo yau, saboda haka suka nufi can kai tsaye, mutane ke fitowa, inda aka riƙo Faisal ko tafiya baya iya yi, idan ku ka ga Faisal za ku rantse bashi bane, yayi baƙi ya rame, yayi muni, ji kawai yayi ance “you are under arrest ", ba musu ya miƙa hannun shi aka kama shi, dan yasan ƙarshen shi ta zo yanzu.

     Maman Fahad ce zaune taji ringing ɗin wayar ta da sauri ta ɗauka cikin murnarta dan ita duk tunanin ta ace mata jirgin su ya sauka, wani irin ihu ta watsa, cikin kuka take faɗin “a'a bazai yuyu ba, bazan bari a hukunta ka ba, dole ne na karɓo ka, ko da, haka yana nufin zan bada rayuwata ", sai kuka take yi, jin horn ɗin mota yasa ta fito dagu, “Alhaji ka dawo Alhaji sannu da zuwa dan Allah alhaji ka taimaka min, Alhaji ka rufa min asiri yadda Allah ya rufa maka ka ƙwato min auta na" , his excellency Jalal kuwa be kula ta ba, dan shi ne ya tura a kama Faisal, tun ranar da Faisal ya bar gidan, yasa ana bibiyar shi kuma yana sane da duk wani motsi nashi, kawai dai yana shiru ne dan yasan ko yayi magana ba ji yaran ke yi ba, kuka kawai ta ke yi, Ghushan ce ta matso tana ƙoƙarin tada ita tsayi, gabanta ne ya faɗi ganin Ghushan haka na nufin Ghushan ta dawo ɗakinta.


Anan zan dasa aya.............✍️💕💕💞💞💞

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️✍️✍️💞💕💕

FAYROZ❤️❤️Where stories live. Discover now