Chapter 96-100

27 2 0
                                    


💮💮💮💮💮💮
FAYROZ
💮💮💮💮💮💮

TELEGRAM
QUEEN NASMERH
https://t.me/joinchat/nBavJtqJ_LA4NGE0

******
INSTAGRAM

Vist this account for Author Queen 2019 novels

https://www.instagram.com/p/CMKIf4kA8jw/?igshid=19bvhlohewk3a
********
WATTPAD ACCOUNT
ASMA'U NANA
https://www.wattpad.com/story/255808218?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_reading&wp_page=library&wp_uname=AsmaunanaLawalliman&wp_originator=O3VdfKPvbMhkEhpNrQgnRWE0eyLarV04bvF0OcQ31byoBx69%2BVCtUljiQ%2B7%2FftlgkxJ%2BBztqtG02hrj6EPgFVFyX1YzF3Q88zyRR4MN%2F2us9Nu0mxvker%2Bf39FaGN4b8

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Page 96-100
*************

Parlorn ta tarar ba kowa aciki, da kallo ta bi Parlorn ba laifin ya tsaru sannan ya sha gyara, ba abunda ke tashi sai waƙa, masu aiki ta gani suna zirga-zirga, ɗaya daga cikin masu aikin tayi wa magana, dan Allah Hajiya Bilkisu fa, dai dai lokacin Ummu Fateema ta iso kusa da FAYROZ, wani mugun mari ta sakar mata tace, ke a garinku haka ake girmama manya, dafe kuncin ta tayi, sannan tace "ina kwana ", ko kallon ta Ummu Fateema batayi ba ta wuce, wannan karon FAYROZ bata ji daɗi ba, fitowa tayi tana jin ba daɗi a ranta, tafiya takeyi tana tunani idan haka rayuwa take a Nigeria ta gwammace ta koma saudia Arabia.

Part ɗin Maman twins ta shiga, a parlor ta same tana wa Faiha kitso, dan yanzu hutu akeyi kullum suna gida, Fareeha da Farzana na game, Fareed da Farhan kuma suna barci a kan kujerakin.

Zaunawa tayi ƙasa, Maman twins tayi murmushi tace "FAYROZ kece yau gurin mu, yanzu nake ce ma Fareeha da Farzana suje suyi wanka su duba ki, ya gajiyar jiya", murmushi FAYROZ tayi tace "ina lafiya, ya yau ɗin ", "alhmdllh" ta faɗa, Faiha tace "ina wuni sister FAYROZ ", murmushi tayi ma Faiha tace "lafiya ƙalau, kitso ake miki?", "eh wallahi ", Fareeha tace "sister ina kwana", "lafiya Alhamdulillahi ", Farzana tace "sister FAYROZ ki zo muyi game tun ɗazu Sister Fareeha ke cutana", Maman twins tace "rufe mana baki, ba gaisuwa sai shegen surutu ", turo bakinta tayi, FAYROZ tace "babu komai ai yarinya ce, zo muyi", matsawa FAYROZ tayi kusa da Farzana suka fara game, dama FAYROZ gwana ce.

Ihu Farzana tasa, dan ta ji daɗin wasan, Fareed ne ya buɗe idonshi gani FAYROZ yasa shi dirowa daga kan kujera da ƙarfi ya rungume ta, "ka tashi kenan "FAYROZ ta faɗa, "morning sister" taji Farhan na faɗa, "morning Farhan, ya kake", "ina lafiya ", Fareed yace "mom ni yunwa nake ji", saka tayi aka kawo musu abinci, suka ci sannan suka fita.

FAYROZ kuwa ba ƙaramin daɗi taji ba, saboda an tare ta hannu biyu, ta jima a part ɗin sannan suka taho tare da su Faiha, twins kawai ne basu biyo ta ba wai su wasa zasuyi.

A part ɗinta suka yini suna bata labarin school, FAYROZ tana ta dariya, ɗaya daga cikin ma'aikatan ta ne ta shigo, Easter, "ma'am your lunch is ready "(ranki ya daɗe angama abinci ki" , "ohk to bring it here" (ki kawo min shi nan).

Fita Easter tayi bayan kamar 3 minutes da fita ta suka shigo tare da Juliet, abinci suka jera a dining table, tashi sukayi suka nufi dining area, FAYROZ ta zuba musu abinci suka ci.

Suna zaune a Parlor Fareed ya shigo da gudu yana kuka, duk ya rikice, cikin firgice FAYROZ ta tun karo shi, "Fareed minene ",muryar shi na rawa yace "sis....ter se....nior Faisal ne ya shigo da mota a guje ya kaɗe Farhan, baya numfashi" ya faɗa sai kuma ya fashe da kuka mai tsuma zuciya.

Fita tayi dagudu, waje ta sami Farhan cikin jini, Farzana kuwa zuwa tayi part ɗin mom ɗin su, "mom an kaɗe Farhan ", mom da take zaune tashi tayi da gudu ta fito, ko kafin su iso FAYROZ ta saka shi a mota dan dama tun da ta zo an bata key ɗin mota, saboda haka bata jira kowa ba ta fita, sai kiranta mom tayi, FAYROZ ta gaya mata bata san asibiti ba, kawai ita ta fita ne cikin firgici.

Mom ta mata bayanin asibiti, FAYROZ tayi amfani da car navigation zuwa asibiti.

Nan take aka karɓe shi emergency, dan yana zubar da jini sosai.

Likitoci sukayi kanshi, ana ta aiki, ko minti biyu ba'a yi ba sai ga su mom, gashi ta kira Abbu suna meeting da ƴan majilisa bai ɗaga ba.

Bayan kamar 30 minutes likita ya fito yana goge zufa, kan shi aƙasa, Mom tayi kanshi, "likita ina ɗana", shiru likitan yayi, mom ta sake maimaita "nace maka ina ɗana ", kallon FAYROZ yayi dan yaga zata ɗan fi fahimta yace "dan Allah ki same ni office ke kaɗai" gefen Mom ya bi ya wuce, sai da ta kwantar wa mom hankali da su Faiha sannan ta wuce zuwa office ɗin likitan.

Zaune ta sameshi yayi tagumi, zaunawa tayi, likitan ne ya ɗago yana kallon ta, sannan yace "nasan ke mai fahimta ce, kiyi haƙuri da abunda zan faɗa miki nasan tun ba yau ba kin san tunda akayi rayuwa dole akwai mutuwa, ba kan mu aka fara ba kuma ba kanmu za'a daina ba, har sai an wayi gari ba komai a duniya, ita kanta duniyar babu ta, tunda aka ɗauki ran manzon mu, kuma be dawo ba kinsan dole kowa zai tafi, da haka ina me baki haƙuri, Yaron da kuka kawo ya koma ma Allah, ma'ana ya riga mu gidan gaskiya, sakamakon jinin da ya zuba ajikinshi "

Jiki FAYROZ duk ya mutu, duk taji duniyar ba daɗi, hawaye ne suka zubo mata a fuska, ƙarfin hali tayi ta share hawayen ta sannan ta fita.

Tana fitowa ta tsaya, Mom tazo da gudu "FAYROZ faɗa min me likitan ya faɗa miki", shiru tayi, Allah yasani bazata iya faɗa wa mom saƙon mutuwar ɗan ta ba, mom zata sake yin magana kenan taga an turo Farhan akan gado an rufe mishi fuska, da gudu ta je gaban gadon, tace "me kuke nufi naga kun rufe min ɗa ", "mom ki yadda da gaskiyar", FAYROZ ta faɗa, hannu mom ta saka ta buɗe fuskantar Farhan hannun ta yana rawa ta ɗaura hannunta a fuskar shi tace " tun kan ƙaramin ka ka tafi, kai baka ma samu ka ji daɗin ƙuruciyar ka, Allah ya gafarta maka yasa hutune a gareka, ni kuma Allah yasa min dangana da rashin da nayi yau "hannun ta ta sa ta sare hawayen ta, Faiha da Fareeha suma kuka suke yi, FAYROZ ta rungume su tana lallashi, Mom baƙaramin tausayi ta bata ba, rashin ɗa ai ba ƙaramin abu bane.

Shirya gawar akeyi dan abasu ita su tafi da ita, FAYROZ tayi shiru tunanin take ya Fareed zai ji idan ya samu labarin rasuwar ɗan uwan shi.

Wayar FAYROZ tayi ringing, ɗagawa tayi ganin Abbu, "FAYROZ naga maman twins ta kira ni ina meeting yanzu kuma ina kira bata ɗauka ba, na kira su Faiha suma duk basu ɗauka ba ki kai mata plsss", shiru FAYROZ tayi sannan tace "Abbu muna asibiti kazo ka sake mu Farhan ne "ta faɗa tana kallon Mom da rufe idon ta tana hawaye, bata jira me Abbu zai ce ba ta kashe wayar.

MU HAƊU A NEXT CHAPTER DAN JIN WANNAN CHAKWAKIYAR.

LOVE U ALL MY READERS.

TSARA LABARI:QUEEN NASMERH👑💞💞💞
ALQALAMIN MU NE :QUEEN NASMERH & MOM MUSAYYID 💃💃💃💓💓💓

FAYROZ❤️❤️Where stories live. Discover now