Chapter 106-200

29 2 0
                                    

💮💮💮💮💮💮
FAYROZ
💮💮💮💮💮💮

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*
***********************
Page 106-200
***************************
Likita ne ya shigo, JAHMEEL yana tsaye gaban gado, magana sukayi da likitan, sannan nurses suka shigo, ɗaukar matar sukayi zuwa toilet.

Wanka aka mata, wow matar kyakkyawa ce ba kaɗan ba, fitowa sukayi da ita, JAHMEEL da ke zaune gefen gado, tashi yayi a firgice, kallon ta yakeyi har abada bazai iya mantawa da mahaifiyar shi ba, wannan ita ce mahaifiyar shi da ya jima yana nema.

Zuwa yayi da sauri ya rungume ta, da mamakin shi sai yaji ture shi, hawaye suka zubo mishi, yanzu ace mahaifiyar shi ma bazata iya gane shi ba.

Fita yayi daga ɗakin, wuce wa yayi ɗakin likita ya sannar dashi matar ta farka, amma kuma bata gane shi ba meyasa.

Likitan yace " eh munyi gwaje - gwaje, kuma sakamakon gwajin ya fito, abunda gwajin ya nuna shine, tana da matsalar taɓin hankalin, dalilin buguwa da tayi da wani abu ", JAHMEEL yace "amma likita ya ciwon yake da sauƙi ko kuwa", "gaskiya babu sauƙi, dan ciwon ya ɗauki shekara 29 tare da ita, haka yasa ciwon ya tsananta, dan haka za'a mata aiki "likitan ya faɗa, cikin rashin amincewa JAHMEEL yace "dole sai an mata aiki zata warke", likitan yace "eh shine hanya mafi sauƙi da zata samu sauƙi", shiru JAHMEEL yayi kafin yace " zanyi shawara ", fita yayi ɗakin ya koma, wannan karon zaune ya same ta, da kallo take bin shi, a ranta tana ji kamar jininta ne, matso wa yayi ya zauna kusa da ita, a hankali yana jin tsanar mahaifinshi, saboda mahaifin shi shine dalilin da yasa mahaifiyar shi take cikin yanayin nan.

Wayar shi ya ɗauka ya kira AIDAH ya sanar da ita cewa ya ga Mammy, baƙaramin farinciki AIDAH tayi ba, ita bata ma san wacece mahaifiyar ta ba ,tana jaririya suka rabu.

MAHBOOB ta faɗama cikin gaggawa suka fara haɗa kayan su, dan ta sha alwashin komin dare sai ta bar dubai.

*************************************

FAYROZ❤️❤️Where stories live. Discover now