Chapter 81-85

30 2 0
                                    

💮💮💮💮💮💮
FAYROZ
💮💮💮💮💮💮


✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

************

Page 81-85

*********
Da ƙarfi ya tura ƙofar ya shiga, Kwance take hankalinta kwance, taji ƙarar buɗe ƙofa, tashi tayi ta zauna gefen gado tana kallon Faisal, murmushi ta sakar mishi, "dallah minene, zaki wani tsare ni da ido kina murmushi kamar wata tsohuwar munafuka" Faisal ya faɗa a tsawace, murmushi FAYROZ tayi dan ita kafin mutum ya ɓata mata rai aiki ne, "zuwa nayi na miki albishir da tashin hankali, wallahi ko ki koma ƙasarku ko na lahanta ki, na miki tabon da har ki koma ga mahaliccinki bazai goge ba ", mamaki duk ya kama FAYROZ, ji wani abu ta girmi yaron nan fa, amma bayada tarbiya, ko dai ƴan Nigeria ne haka.

Juyawa yayi ya fita, Farhan da yake tsaye tun ɗazu yana jin su, Abbu na dawowa ya kwashe ya faɗa mishi, da sauri Abbu ya wuce part ɗin ta, FAYROZ na zauna aka three seater tana kallo, ya shigo, duƙawa tayi har ƙasa, "sannu da zuwa Abbu ", murmushi yayi yace "yauwa love, ya gidan", "alhamdulillah "ta faɗa, yace "yanzu naji abunda Faisal ya miki", murmushi ta faɗaɗa sannan tace "Abbu babu komai nice yayar su ai, dole zan fahimta ", "eh amma dan kina yayar su haka baya nufin su dinga miki rashin kunya, kuma ba haka ba ya kamata dukan su su sanki, saboda haka gobe da ƙarfe tara na safe zasu dukan su gidan nan, zan nuna miki ƴan uwanki"Abbu ya faɗa, "to shikenan Abbu", waya ya ciro daga aljihunshi da sim card yace "gashi kiyi amfani da wannan, na saka miki kati aciki ", karɓa tayi dama tana so tayi waya da Ummie amma bata da sim card ɗin Nigeria "thank you Abbu" ta faɗa.

Fita yayi zuwa ɓangaren shi.

**'****************

Wanka yayi zuwa saudi basic industry, yayi kyau kayan jikin shi su amshe shi matuƙa, tafiya yake guards ɗin shi na take mishi baya.

KAI JAHMEEL BA DAI IZZA BA.

Be san miyasa ba yana shiga gurin yaji ba daɗi , sai ya tuna da daya shigo zai hango FAYROZ a coffee office ɗinta, Allah sarki rayuwa.

Wucewa yayi, kai tsaye office ɗinshi ya wuce, ba'a fi minti 30 da shigowar shi ba, wata budurwa ta shigo ɗauke da kofin coffee, haɗe rai yayi yace "get out of my office, ni nace ina buƙata ne, daga yau kar wanda ya sake kawo min coffee ", jikin Fauzana yana rawa ta fita daga office ɗin.

Maida kanshi yayi kan kujera ya rufe idon shi, yanzu FAYROZ bata nan, bazai sake shan coffee ɗin kowa ba, saboda ba wanda yakaita iyawa, ya faɗa aranshi, tashi yayi ya fara gudanar da aiki sai magrib ya kammala, haɗa kayanshi ya fara yi sannan ya wuce gida, yanzun ma coffee office yake kallo, gani yakeyi kamar zata zo tace "sir your coffee is ready ".

NI KUWA NASMERH NACE HABEEBIE JAHMEEL, FAYROZ TA MAKA NISA😩😄

Mota ya shiga zuwa gida.

*************
MASU KARATU WASU NA TAMBAYA NA WACECE HALIMATUN DA DALEEL KE MAGANA KAI, IDAN BAKU MANTA BA, BAYAN ZUWAN DALEEL DUBAI, AKWAI WATA YARINYA DAKE ZUWA GURIN SHI AMMA KUMA BAYA KULA TA, TO ITA CE HALEEMATU.

Kallon ta yake ko ƙyafta ido baya yi, juya idon ta tayi tace " my love kallon duk na minene ", murmushi Daleel yayi yace "Haleematu I love you so much", dariya tayi, sannan tace "bayan ka gama ja min rai ", hannunta ya kama yace "nayi kuskure baby a yafe min", "an yafe maka masoyi na" ta faɗa tana kashe mishi ido

Abinci suka ci tare, sannan ya ajeta masaukin ta, ya wuce gida ciki da ƙaunar ta fal ranshi.

Sai yanzu FAYROZ ta faɗo mishi arai, gaskiya ya kamata ya neme ta ko ba komai anyi mutunci.

Bayan ya isa gida ne ya kira NAASHEETA, "hello ɗan uwa, yau an tuna dani kenan ", murmushi yayi yace"ba gara ni ba ina tunawa dake, amma ke tunda kikayi aure kin manta dani", "laaaaa, ayi haƙuri, ni ban manta da ku ba, amma zan gyara "NAASHEETA ta faɗa.

"yauwa ƴar uwa, wai ina FAYROZ" Daleel ya tambaya, "wallahi nima na ji ta shiru kwana biyu, naje gidan su , Ummien ta take sheda min ai ta bar ƙasar tana gurin mahaifin ta "NAASHEETA ta amsa mishi, Daleel da mamaki ya cika yace "dama mahaifin ta na raye", "nima fa bansaniba sai ranar da Ummie ta faɗa min ", "ohk to, amma da kin tambayi number ta"Daleel ya faɗa, "eh zanyi, insha Allah, ranar ma mantawa nayi" NAASHEETA ta faɗa, "idan kin samu ki min text ɗin number mu dinga gaisawa "ya faɗa, nan suka yi sallama ya kashe wayar shi.

💞**Q***U***E***E***N***-***N***A***S***M***A***H**💞
💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕

**********
Ta ɓangaren Mahboob kuwa amarya na ta zuba mishi shagwaɓa, shi kuwa sai akin lallashi, shigowa ta kenan gidan, na gashi ya ɗauko tiren abinci ya kawo gabanta, "baby tashi kici wannan ", turo baki tayi tace "ni bazan iya ba".
KAI WANNAN AMARYA AKWAI RAKI.

Daƙyar Mahboob ya lallaɓata taci abinci, sannan ya kamata ta tafi ɗaki, dan zazzaɓi ya rufe ta, shi ya gyara gidan, sannan ya dawo ɗaki dan taya ta jinya.

************

WASHE GARI DA SAFE.

Wanka FAYROZ tayi ciki wata abaya me kyan gaske ash, tayi matuƙar, karɓar jikin ta, duwatsun rigar sai wani ƙyalli suke yi masha Allah, tayi kyau sosai, duk da ba kwalliya tayi ba, kwalli ne kawai da lip bam, amma masha Allah tayi kyau matuƙa.

Yanzu agogonta ya nuna mata ƙarfe 8:30, Leƙewa tayi ta window, mutane tagani suna shigowa da alama ƴan uwanta ne da bata sani ba.

Fitowa tayi daga ɗaki zuwa ɓangaren Abbu inda yayi karo da Farooq wanda ita kanta bata sanshi ba, ɗagowa yayi yana binta da wani mugun kallo, "sorry" ta faɗa sannan ta juya zata wuce, hakan da tayi yayi matuƙar ƙona mishi rai, hannun shi ya ɗaga zai mareta, ciki rashin sa'a yaji an reƙe mishi hannu ta baya, juyowa yayi dan yaga wanene, haɗe rai yayi gani.............

MU HAƊU A NEXT CHAPTER DAN JIN WANENE YA HANA FAROOQ MARIN FAYROZ.

TSARA LABARI:QUEEN NASMERH✍️ 👑💕

ALQALAMINMU NE🖋️🖋️🖋️ :QUEEN NASMERH & MOM MUSAYYID ❤️❤️❤️❤️

ALQALAMI YAFI TAKOBI 🖋️✍️💕💞💞💞💞💞💞


FAYROZ❤️❤️Where stories live. Discover now