Chapter 606-700

39 5 0
                                    

            💮💮💮💮💮💮
                   FAYROZ
           💮💮💮💮💮💮
https://www.wattpad.com/user/QUEENNASMERH08?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
Chapter 606-700
***********************************
Dukan su ɗakin Fayroz suka shiga, banda kuka ba abunda take yi, taji duk abunda Jahmeel ya faɗa, Mammy ce ta ƙarasa gabanta “Fayroz kina son Jahmeel? ", cikin kuka tace “eh da dukkan nin zuciyata", cikin tausayawa tace “kiyi haƙuri da abunda kika ji, yanzu za'a shirya miki kayanki, jirgin da zamu bi zai sauka soon, dan haka zamu wuce ",share hawayenta tayi tace “ina Jahmeel", Mammy tace “duka tare zamu wuce ", fita suka yi duka ya rage Fayroz da Ummie a ɗakin, guri ta samu kusa da Fayroz ta zauna tare da ɗaura hannunta a kafaɗar Fayroz tace “Habeebty kina farinciki da auren nan?", “Ummie ina farinciki da duk abunda kuke so, amma a wani ɓangaren ina jin ba daɗi da zan auri wanda baya so na", Ummie tace “na yadda dake, zaki iya sa shi ya so ki, abunda kawai nake so a gurinki shine ki mishi biyayya", gaɗa kai kawai tayi.

   A ɓangaren Jahmeel Abbu ne a ɗakin yana jiran yaga fitowar shi, ya ɗauki kusan awa ɗaya a ciki, sannan ya cire kayan jikin shi yayi wanka, a ɗakin ya sami Abbu, cikin jin kunya yace “Abbu kayi haƙuri ", murmushi Abbu yayi yace “kai da Fayroz duk ɗaya ne a gurina, bazan so a tilasta wanin ku ba", zuwa Jahmeel yayi gaban shi, durƙusawa yayi yace “ni ba wai an min tilas ba ne, kuma ba wai bana son Fayroz ba, ina sonta, amma kuma bazan iya aure ba, ni ban shirya ba ", Abbu yace “idan har haka ne zan sa a bar min Fayroz nan har ka shirya", Jahmeel yace “ai rashin shirina na har abada ne, Abbu maganar rayuwata ba na lokaci bane, ni aure baya tsari na, kawai ni ban shirya son kowa ba, idan nace na zauna da Fayroz to haka na nufin na tauye ta, ni kuma abunda bana so kenan ", Abbu yace “to so kake ka sake ta", Jahmeel yace “a ƙa'ida ta ban yadda da saki ba ", Abbu yace “to ya kake so ayi?", Jahmeel yace “ni kawai ban sani ba, amma zan zauna da ita, Allah ya bani ikon sauke nauyin da ya rataya a kaina ", Abbu yace “Ameen, ni bari na je", fita Abbu yayi, duk ranshi ba daɗi, burin shi Fayroz ta zauna cikin walwala, ya zata zauna da mutum mai tsats-tsauran ra'ayi irin Jahmeel, Jahmeel kuwa shiryawa yayi cikin wata riga har zuwa guiwa, duk rigar aiki ne irin na, maza, rigar Maroon ce, wando baƙi ya saka wanda yayi matuƙar mishi kyau, rawani ya ɗaura wanda yayi kyau sosai, dan rawanin ba irin namu bane, sai yanzu ya tuna abunda Mammy ta faɗa mishi jiya da rana lokacin da ta kawo mishi kayan nan “ka saka wannan kayan nan idan za'a kai amarya, nasan zaka fi angon kyau", takaici duk ya cika shi, ashe ma shine angon kawai shashantar da shi su ke yi shiyasa.

   A ɓangaren Fayroz kuwa Mammy ta shirya ta cikin wata doguwar riga Maroon, rigar ta matuƙar zama a jikinta, duk rigar tun daga gabanta har bayanta duk stones ne, rigar tayi matuƙar zama a jikinta, wanni net shima maroon aka rufe mata fuska da shi bayan an mata light make up, daga cikin net ɗin zaki iya ganin fuskar amaryar da hawaye suka wanke ma ido, gashi tayi mutuƙar yin kyau, “Masha Allah "Mammy ta faɗa, murmushi Fayroz tayi, Mammy tace “ki zauna nan, bari na dawo", fita Mammy tayi, ɗakin Jahmeel ta shiga inda ta ganshi tsaye gaban madubi, murmushi tayi a hankali tace “masha Allah, ɗana yafi kowa kyau ", juyowa yayi da ɗan murmushi a fuskar shi, matsowa tayi gaban shi tace “Jahmeel kaje ka kama amaryarka ku fito tare, kar ka manta ƴan uwan Papa suna nan, saura ka nuna musu baka son amaryar", ta ƙarasa maganar tana shirin barin gurin, Jahmeel yace “Mammy ", juyowa tayi “minene" ta faɗa tana ɓata rai, “yanzu bazan samu albarkarki ba ", “Allah ya maka albarka" ta faɗa tare da barin ɗakin, sosai Jahmeel yaji ba daɗi, kai tsaye ɗakin Fayroz ya nufa, dan yasan yanzu Mammy zata iya ɓata rai tayi mishi faɗa kamar ɗazu.

   Tana zaune Jahmeel ya shiga ɗakin, wani irin sanyi daɗi me haɗe da ƙamshin Fayroz me daɗin shaƙa ya daki hancin shi, haka ya janyo tsayawar numfashin shi, da ƙyar ya samu ya daidaita numfashin shi, a hankali ya isa bayan Fayroz, dake duƙe bata ma san da shigowar shi ba, jin hannu a kan kafaɗarta ya tabbatar mata da Jahmeel ne ba kowa ba, da sauri ta rufe idonta, a hankali taji yace “tashi mu fita, su Mammy na jiran mu a parlor ", ƙoƙari tashi take yi, lokacin da taji a ɗaga ta sama cak da hannun shi biyu, in bridal style, fuskatar dab da nashi tana jin numfashinta na shirin ɗaukewa, shima ɗin kallonta yake yi, ya rasa dalilin da yasa idonshi basu iya kauda kai akan Fayroz, rufe idonta tayi, a lokacin da take jin wani irin shauƙi yana kamata, bata da feelings ma kowa sai Jahmeel, shine kawai wanda take jin irin yanayin nan a kanshi, shi ma Jahmeel ɗin ji yake ko ina na jikin shi na buƙatar Fayroz, a karo na farko da ya ji zai iya canza ra'ayin shi akan Fayroz, cikin taku da nuna isa yake tafiya, yayin da rigar Fayroz ta baje ko ina har ƙasa, duk da ɗaukar ta yayi, yana saukowa parlor ya fara jin ruwan Flowers na sauka kanshi, wanda yayi dai-dai da kawowar hasken fitilar da ke kashe, da sauri suka kalli junansu, wanda camera mana ya fara ɗaukar su hoto, Mammy ba ƙaramin daɗi taji ba, haka su Ummie ma sunyi farinciki, da fatan Allah ya basu zaman lafiya, har waje aka bisu ana zuba musu Flower, gaban wata mota ya tsaya, wadda aka rubuta MR & MRS  JAHMEEL LATEEF, motar tayi kyau sosai fara ce sol, motocin cin gurin duka baƙaƙe ne banda ta amarya da ango, buɗe mishi motar Ummie tayi ya saka ta, sannan ya rufe da kanshi bayan ya saka ta a motar, zagayawa yayi ta ɗayan side ɗin, shiga yayi sannan ya rufe motar, cikin convey suka nufi airport, a ranshi yana ji ya fara sabuwar rayuwa, tunda har an ɗaura mishi aure da Fayroz dole ya bata duk wani farinciki da take so, saboda shi yana da bambanci da mahaifinshi bazai iya cutar da mace ba, kuma bazai juri ɓacin ran mace ba, saboda a gurin shi mace uwa ce, ƴa ce, mata ce, sannan kuma jika ce, ƙanwa kuma yaya!, to miyasa zai bar mace tayi ƙasa, yanzu yake dana sanin abunda yayiwa Fayroz a baya dan maganar gaskiya yana takura mata ne dan ya huce takaicin Papa a kanta.

Ko ya zata kaya tsakanin Fayroz da Jahmeel, ko zata yadda da Jahmeel bayan ya faɗa gaban kowa bazai taɓa sonta ba?.

Ki bi Alqalamina ƴar uwa idan kina son sanin duk abunda zai faru.

Anan zan dasa aya.

Kar ku manta kuyi following Wattpad account ɗin ta link ɗina dake sama.

   ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️✍️✍️⚔️

FAYROZ❤️❤️Where stories live. Discover now