Chapter 306-400

21 1 0
                                    

  💮💮💮💮💮💮
                     FAYROZ
              💮💮💮💮💮💮

Tsara labari da rubutuwa :Queen Nasmerh

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
https://www.wattpad.com/user/QUEENNASMERH08?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

Chapter :306-400
************************************
Ɗakin da aka gyarawa Abbu ya shiga, mai aiki ce ta shigo da kayan shi ciki. Kallon ko ina na ɗakin yake yi tare da mamakin yadda Ghushan ta iya aje hotunan nan yake yi, ya ɗauki lokaci  yana kallon hotunan, duk yawancin hotunan na yarintarta ne, wasu kuma lokacin da take budurwa, wasu hotunan kuma nasu ne shi da ita, murmushi yayi lokacin da ya kai hannun shi kan wani hoto  bazai manta wannan ranar ba, wato ranar da aka ɗaura musu aure, kallon hutunan yake yi lokacin da idon shi ya sauka kan wani hoto, wani taro ne Ghushan tayi lokacin basa tare da Jalal, kallon hoton yake yi a hankali har idon shi su ka sauka akan wata mace, wacce nima a hankali na ƙare mata kallo sai na gano Ibjihal ce, kallonta yake yi, ya rasa miyasa amma ta mishi kama da sistern shi wato Janeesa, kallon hoton yake yi, ciki da mamaki, daren ranar barci gagarar shi yayi.

   A ɓangaren Jahmeel kuwa yaji daɗi sosai da Papa ya yadda zai dawo gare su, kuma ya kira Aidah ya sanar da ita, Aidah taji daɗi sosai ba kaɗan ba, dan gobe jirgin safe zata biyo insha Allah, gobe za'a sake ɗaura auren Ibjihal da Lateef, wanda auren zai kasance a gidan su Jahmeel, kuma tun a daren ranar aka fara gayyatar mutune, abun ka da harkar manya.

    Washa gari da safe Fayroz ta shiga ɗakin da Abbu ya sauka, zaune yake akan sallaya da alama tunda yayi sallah be tashi ba, wani hoto ne hannun shi, shigowa tayi, “good morning Abbu "ta faɗa tana zama gefen shi, murmushi yayi lokacin da ya ɗago fuskar shi “mrng love ya daren jiya" ya faɗa yana kallon ta, “Alhamdulillah ala kullu hal" ta faɗa, “Fayroz kin san mutanen da ke jikin hoton nan? "Abbu ya tambaya yana nuna mata “wannan hoton ya ɗauki shekaru da dama, domin Ummie ta faɗa min cewa tun kafin ta haife ni aka yi shi" Fayroz ta faɗa, Abbu yace “to bata faɗa miki mutanen da ke ciki ba ", FAYROZ tace “ta faɗa min, a lokacin sun yi wani taro ne da matan manyan mutanen da ke faɗa a ji saudi arabia, ta faɗa min this are the wives of the top ten richest people in saudi arabia, masu faɗa a ji", Abbu yace “miye sunayen su? ", murmushi tayi tace “Abbu tambayar ta minene", Abbu yace “ke dai kawai ki faɗa min ", “ohk wannan itace Inbihaj matar Lateef kenan" ta faɗa tana nuna mishi maman su Jahmeel, “wannan ma ya isa dama ita nake so na sani ", da mamaki take kallonshi “Abbu me yasa kake son sanin ta?", Fayroz nima  ban sani ba ", “ohk Abbu mu je mu ci abinci",aje hoton yayi suka fito.

   Zaune Ummie ta ke kan kujerar da aka tanada domin cin abinci, kallon su ta ke yi har suka ƙaraso, da murmushi a fuskarshi yace “good mrng habibty ",, “mrng" ta faɗa tana me jin kunya, abinci su ka fara ci, su na fira, “Ghushan! ", Abbu ya kira sunan Ummie, ɗagowa tayi tace “na'am", “a ina Inbihaj matar Lateef take zama? ", kallon shi tayi da mamaki tace “miyasa ka tambaya?", “nima bansani ba, yanayi ne kawai zai warware komai, ke dai kawai ki faɗa min ", “gaskiya ban sani ba, kawai dai na san gidan Lateef ɗin" ta faɗa, Abbu yace “idan mun gama cin abinci za mu je", Fayroz tace “amma Abbu auren fa? ", “Fayroz ba zamu jima a can ba, kawai za muyi magana ne, bayan haka ɗaurin auren ai ƙarfe biyar ne na marece", Fayroz tace “to shikenan ", abinci su ka ci, bayan sun gama ne suka shirya domin fita.

    Tun ƙarfe 10:00 Aidah ta iso, da tsohon cikinta da yanzu yake da wata 6,gidan ko ina ya cika da mutane masu kai da kawo, sai shiga da fita ake yi cikin gidan ko ina na gidan cike yake da mutane ba masoka tsintsiya, can ta hango su Mammy da ke sanye da wata riga doguwa tayi matuƙar yin kyau Jahmeel ne ya mata order daga india, daga gefenta kuma Papa ne sanye da riga fara da wando baƙi, yayi matuƙar yin kyau, hannun shi cikin nata, murmushi Papa yayi lokacin da ya ga Aidah, cikin sauri ya buɗe mata hannu “zo da sauri ki rungume Papanki ", faɗawa tayi jikin shi tare da fashewa da kuka, wannan shine karo na farko da Papa ya karɓe ta a matsayin ƴar sa, gaisawa su ka yi da su Jahmeel.

   Yanzu za'a ɗaura auren dan haka, kai tsaye aka fara komai, lokacin da su mammy suka shiga cikin gida, Papa da su Jahmeel su ka shiga masallacin gidan, inda duk girman gurin sai da aka cika shi da mutane wasu har waje, ɗaurin auren bai wani ɗauki lokaci ba aka ɗaura.

    Mutane sai barka da arziki su ke yiwa Lateef, kowa a garin sai mamaki yake yi yadda su ka ga Lateef ya canza, su basu ma taɓa sanin Jahmeel ɗan sa bane, amma ba abun mamaki bane dan Jahmeel halin mahaifin shi ya bi gurin tsauri da fushi, amma suna da bambanci dan shi mahaifin shi baya son mata ya tsani mace, amma Jahmeel ba haka yake ba.

  Mammy ta kasa ɓoye farincikinta dan sosai taji daɗi, ko dan yaranta ma, waje su ka fito inda aka shiga yin hotuna da, wasu kuma sai ci su ke yi, kowa da abunda ya ke yi, dai-dai lokacin su Jalal suka shigo cikin gidan, Ghushan ce a gefen shi  na dama, ɗayan gefen kuma Fayroz ce, a hankali su ke tafiya, daga can gefe kuma su Mammy sai dariya su ke yi da alama firar da su ke yi tana mata daɗi, kamar ance ta juya, kawai su ka haɗa ido da Jalal da shigowar shi kenan, har abada bazata manta da fuskar shi ba tun suna yara, cikin karkarwa ta furta “Jal..... Jalal", da sauri ya matso kusa da ita “Janeesa! ", kafin ya iso ta faɗi ƙasa sumammiya.

Jahmeel da ke kallon Fayroz da mamakin me ya kawo ta gidansu, jin faɗuwar Mammy ne yasa yayi saurin ɗaukarta, kai tsaye ɗaki da ake duba mara lafiya su ka nufa dake cikin gidan, duba ta aka yi, likita ya faɗa musu ta firgita ne, amma yanzu zata farka. Ba'a wani ɗauki lokaci ba ta farfaɗo, kuka ta fara yi “Yaya na Jalal, ka faɗa min kai ne "ta faɗa tana miƙa hannunta, riƙe hannunta Jalal yayi yace “ki faɗa min ke ce Janeesa ba Inbihaj ba", a wannan karon kanta taji ya sara, tsaf sai yanzu asalin sunanta ya dawo kanta, tabbas Inbihaj ba shine asalin sunanta ba, dafe kanta tayi a lokacin da duniya ta shiga juya mata, yau tuna komai na ta tsaf, tun daga ranar da aka ɗauke ta a mota, har zuwa yau.

  Kallon shi tayi tace “eh nice Janeesa ", Jalal yace “ina kika tafi tsawon shekarun nan, ina kika shiga na neme ki", Mammy tace “labari ne mai tsawo ", Jahmeel yace “ban gane ba ku fahimtar da mu", Mammy tace “mu je parlor za ku ji komai ", Lateef kuwa ya rasa abun cewa, addu'a ya ke yi kar a ce wannan mijin Mammy ne, kenan aure tayi bayan rabuwar su, ko kuwa kafin haɗuwar su.

    Parlor su ka nufa, zaunawa su ka yi, Ghushan kuwa ta matsu tasan wacece Janeesa a gurin Jalal ɗinta.

  Jalal ne yayi gyaran murya, ganin tambaya a fuskar kowannen su, sannan ya fara magana “Janeesa ƙanwata ce, wadda ita kaɗai ta rage min bayan mun rasa iyayen mu ", nan ya kwashe labarin komai da komai ya ba su har ma da rasuwar iyayen su da kuma ranar da aka sace Janeesa lokacin da ya je siyayya da ita ya barta a mota har ya dawo ya neme ta ya rasa, Jahmeel ne cikin tausayawa yace “to Mammy Ina kika je a lokacin? ", “wasu mutane ne su ka sace ni da niyyar yimin fyaɗe, su ka buga min wani abu a kai, wanda yayi sanadiyyar faɗuwa na, tun daga lokacin ban sake tuna inda nake ba, wanda haka yayi sanadiyyar rasa tunanin na, sai watarana na farka naganni a wani gida, a lokacin ne wani mutum yake faɗa min shine ya ɗauke ni, ba tare da ya bari an min fyaɗe ba, a lokacin ne na fuskanci rayuwa kala-kala a gidan dan matar shi bata sona, kwatsam sai ga rasuwar mutumin da ya ɗauke ni, bayan ya mutu ne matar shi ta kore ni daga gidan shi, a lokacin ne na haɗu da Lateef a hanya, wannan shine " ta ƙarasa maganar tana kuka, Lateef ne ya rungume ta tare da furta “kiyi haƙuri da na ƙuntata miki" hawayen ta ya shiga share mata hawaye. Fayroz da Ummie ma duk sun tausaya musu.

Anan zan dasa aya............. ✍️

KAR KU MANTA KUYI FOLLOWING WATTPAD ACCOUNT ƊINA TA LINK ƊIN DA KE SAMA, INA SONKU, SO NA HAR ABADA.

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️⚔️💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

FAYROZ❤️❤️Where stories live. Discover now