Chapter 301-305

23 3 0
                                    

💮💮💮💮💮💮
                     FAYROZ
           💮💮💮💮💮💮

Tsara labari da rubutuwa :Queen Nasmerh

Chapter 301-305
------------------
“Jahmeel wacece wacce ta tafi ta barka? " ta tambaya lokacin da ya fara cin abinci, sarƙewa yayi, da sauri ta bashi ruwa don ya samu ya tsayar da tarin da ya turniƙe shi, “zaka iya ɓoyewa Mammyn ka wani sirri?", gyara zama yayi yace “dan me zan ɓoye miki wani abu, kawai dai bansan ta ina zan fara ba, Mammy ita yarinyar kawai dai ba wa sonta na ke ba, amma zuciyata tana faɗa min ina da kusanci da ita, duk yadda zan tsaurara mata, Mammy sai na riƙa ganin kamar Aidah, na rasa me ya ke kusanta ni da ita ", Mammy tace “waya sani ko ita ɗin matarka ce",“ Mammy ni ban taɓa ji ina son ta ba, a taƙaice ma idan na ganta ji nake ina so na muzguna mata, bayan haka ma nasan ita ta tsane ni ", Mammy tace “wa zai tsani ɗana, ai kai namiji ne, mafarkin kowace mace", dariya yasa“Allah Mammy kin cika abun dariya, wai mafarkin ƴa mace, ai ba cikin barci nake ba, a duniya na ke ", “kai baka faɗa min sunanta ba ", “Fayroz Jalal sunanta ", dummmmm! Gaban Inbihaj wato mahaifiyar Jahmeel ya faɗi, Jalal ɗin da ya faɗa yau ya tuna mata da sunan wanda tafi ƙauna a rayuwar ta, “Jahmeel yanzu Fayroz tana ina", “ kwanannan na samu labarin tana Nigeria gurin asalin mahaifinta ", shiru tayi  dan sai yau ta fara tuna rayuwar baya, tashi tayi da sauri ta nufi ɗakin ta.

     A ɓangaren FAYROZ kuwa ta gayawa Abbu abunda Ummie tace, kuma yayi farinciki, insha Allah yau gobe zasu je, in ya so sai a sake ɗaura auren acan, su dawo tare.

Haka kuwa aka yi da sassafe su ka yiwa mutanen gidan sallama, Ummu Fateema da maman Fahad sai cika ake ana batsewa, maman twins kuwa da murmushi a fuskarta ta musu sallama, Faheem ya musu rakiya har airport, jirgi su ka hau zuwa saudi arabia.

A ɓangaren Jahmeel kuwa mamakin yadda Mammy ta canza kwana biyu ya ke yi, tun ranar da su ka yi maganar Fayroz da ita bata sake sakewa ba, ko dai bata son Fayroz ne?, Alhaji Lateef kuwa yanzu bayada wani buri daya wuce ya ga Aidah, yayi tunani da kyau, ya fahimci abunda yake yi be dace ba, bayan haka ma mace tayi sanadin zuwan shi duniya, da ba dan ita ba da bazai samu ƙarfin da zai ce sai ɗa namiji yake so ba, gashi Jahmeel na gudun shi saboda wannan dalilin, dan haka yau ya yanke hukuncin zuwa ya ba Inbihaj da Aidah haƙuri, a parlor ya same Jahmeel da Mammy, yana kwance a cinyar ta, sai shagwaɓa ya ke zuba mata wai ta  dai na kula shi saboda ya bata labarin Fayroz, ita kuma sai ƙoƙarin bayani take mishi amma yaƙi ya saurare ta, murmushi Alhaji Lateef yayi ganin yadda su ke wasa da dariya, sai yaji ina ma yana cikin su, gyaran murya yayi wanda haka yasa su ka san wani ya shigo gidan, dummm! Gaban Inbihaj ya faɗi gani Lateef, Jahmeel yace “ Abbiey kai ne nan ", murmushi Alhaji Lateef yayi ya rungume Jahmeel “eh nazo gurin Mammyn ku ne da Aidah", murmushi ya bayyana a fuskar Jahmeel dan ba ƙaramin daɗi yaji ba, “to Abbiey ni bari na shiga daga ciki" wucewa yayi ɗaki domin ya basu guri su daidaita.

     Guri Lateef ya samu ya zauna tare da ƙurawa Inbihaj ido, duƙar da kanta tayi dan bazata iya haɗa ido da shi ba, kallonta ya ke kamar zai maida ta ciki, sun fi ƙarfin minti 30 a haka, sannan ya ƙara gyara zama a hankali cikin sanyi murya yace “Inbihaj ", shiru tayi, dan zuciyarta ta mata nauyi, murmushi yayi yace “nasan kina fushi dani amma ki saurare ni, wannan sabon Lateef ne ba wancan da kika sani ba, na san na muzguna miki kuma na aikata laifin da ban cancanci a yafe min ba, amma ina me neman alfarma, ki bani dama ta ƙarshe na gyara kuskure na, wannan karon idan nayi kuskure ki nesanta yarana daga gare ni har abada ", shiru tayi banda hawaye na abunda ke bin kuncinta, tashi yayi daga kan kujerar da ya ke ya durƙusa gabanta tare da riƙe hannayenta biyu, a hankali ya shiga murzawa “kiyi haƙuri da na zama silar hawayen ki, wannan karon zan zama silar farincikin ki har abada ", shiru tayi, Lateef yace “shin zaki bani dama ta ƙarshe", gaɗa mishi kai tayi alamar eh, tashi yayi ya rungume ta, ita kuma sai kuka ta ke yi, da ƙyar Lateef ya lallashe ta tayi shiru.

   ************'****'*********
FAYROZ

Sun isa saudi arabia lafiya, kai tsayi gidan su Ummie (Ghushan) suka nufa, da murna ta tarbe su , taji daɗi musamman ganin Fayroz da tayi, rungume ta tayi tare da faɗin “I miss you Ummie", Ummie tace “I miss you more Fayroz ", Abbu yace “ni ba'a missing ɗina?", bata kula shi ba, suka shiga ciki, abinci kala-kala aka kawo musu, ci suka yi sannan Abbu yace zai wuce saboda dare yayi sai gobe zai dowa, FAYROZ ta marairaice fuska tace “ Abbu ka kwana nan, akwai ɗakuna isassu fa, Ummie a buɗe mishi ɗakin da ke kusa da ɗakina plss ", “Fayroz zai yi wani iri na kwana nan" Abbu ya faɗa , Fayroz tace “Abbu babu abunda zai faru fa, kuma ai mu yanzu mun zama ɗaya ", ba dan ya so ba ya yadda zai kwana, Ummie ce ta bada mukullan ɗakin domin a gyara shi ɗakin da Ummie ta fi so ne, kuma akwai hotuna ciki sosai a bangon, gyara ɗakin aka yi, a ka goge domin an jima ba'a shiga ciki ba.

   Fayroz kuwa farinciki fal ranta, sai washe haƙora ta ke yi, Ummie kuwa ta halbo jirgin Fayroz, dan haka da harara ta bi ta tace “za kiyi bayani ni da ke ne ", Fayroz tace “wai me nayi kuma Ummie", Ummie tace ban saniba", Abbu yace “Fayroz ƙyale Ummienki kinji ", murmushi tayi tace “ai nasan Abbu bazai bari Ummie  ta taɓa ni ba".

TO MASU KARATU KU BIYO NI NEXT CHAPTER DAN JIN YADDA WANNAN CAKWAKIYAR AHALIN NA ZAI KASANCE.

TAKU HAR KULLUM QUEEN NASMERH

KARKI MANTA KU YI FOLLOWING WATTPAD ACCOUNT ƊINA

QUEEN NASMERH'S WATTPAD ACCOUNT

Show me love and follow
https://www.wattpad.com/user/AsmaunanaLawalliman?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️✍️

FAYROZ❤️❤️Where stories live. Discover now