Chapter 406-500

21 0 0
                                    

           💮💮💮💮💮💮
                     FAYROZ
           💮💮💮💮💮💮

Tsara labari da rubutuwa :Queen Nasmerh

Chapter 406-500
***********************************

Hukuncin kisa ta hanyar rataya aka yankewa Faisal, inda aka nufi gurin da za'a rataye shi da shi, Abbu yasha kuka saboda ɗan shi ne, duk yadda ɗa ya lalalace mahaifan sa suna son shi, amma ba yadda za'ayi dole doka ta fara da gida, bayan haka ma shari'a na kan kowa, dole a hukunta shi, kamar yadda kotu ta zartar haka aka yi rataye Faisal aka yi har sai da ya daina numfashi.

   Maman Fahad kuwa tasha kuka, amma duk da haka ba nadama a zuciyar ta, motarta ta ɗauka a zuciye ta fita daga gidan, ranta a ɓaci kai tsayi wani daji ta shiga, cikin kogo naga ta shiga ai kuwa ba shiri na bita domin ganin ƙwam, da mamaki naga wasu gardawa a tsaye, “so nake ku kawar da ita, ka kashe ta har abada "ta faɗa tana nuna musu hoton Ghushan (Ummie), fitowa tayi, inda ta shiga mota bayan ta basu bayani akan yadda zasu shigo cikin gidan gwamna wato hiss excellency Jalal, ta kuma musu bayani akan tana fitowa da daddare ta zagaye gida, sannan tana saka dogayen ruguna, gida ta dawo.

    

     A ɓangaren su Jahmeel kuwa, ba ruwan shi da Fayroz, shi dariya ma take bashi yadda take yi, yau zasu dawo Nigeria, kamar yadda ya canza ra'ayi dan shi ya gaji da ganin Fayroz, ko yana so ya fita sai Mammy ta hana shi wai ga Fayroz ina zai je, haɗa kayan shi ya gama yi, inda ya fito ya tarar da su Mammy a parlor, FAYROZ ce tsaye a gefen shi, “oya let's go "ya faɗa yana nuni da Fayroz, bin shi tayi su ka fita, sallama su ka yi da Mammy su ka tafi.

   Airport su ka nufa, ko da suka isa an gama kiran sunan mutane, dan haka da sauri su ka shiga ciki, jirgin su ya lula sararin samaniya, sai Nigeria 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻Nigeria ƙasar da tafi ta kowa, Nigeria ƙasar da mutanen cikin ta jajirtacci ne, a Nigeria zaka samu abun dariya, kuka, da takaici, a taƙaice ce dai Nigeria rayuwa ce 😂😂duk wanda yaji haushi ya koɗa ƙasar su ehe.

        Da misalin ƙarfe biyar na yamma Jirgin su ya sauka, ko da suka fito already Abbu yana airport su kawai yake jira jirgin su ya sauka, hannu shi ya buɗe, Fayroz ta rungume shi cike da farinciki, Jahmeel ma zuwa yayi ya rungume shi, murmushi ɗauke a fuskar shi yace “dana sannu da zuwa "Abbu ya faɗa, Jahmeel yace “yauwa barka dai Abbu", murmushi ya sakar mishi sannan su ka shiga mota, Jahmeel yana ta kallon Nigeria, mamakin yadda aka yi Nigeria ta zama ƙasa ya ke yi, ai wannan ko state be ci ace ta zama ba,( ni kuwa nace kadai faɗa, ai Nigeria tafi ko wace ƙasa kyau), gidan Abbu su ka nufa, idan Jahmeel ya manta ya shigo Nigeria tsabar kyau, (ni kuwa nace kana sane Nigeria ce).

   Gate aka buɗe musu, suka shiga, a harabar gida su Fareed suka tare Fayroz dan sun yi kewar ta, duk su Faiha, Fareeha da Farzana suna gurin, farinciki ta ko ina ranta ga ƴan uwan ta, Ummie da Momy ne tsaye, rasa tayi wa zata runguma, a tare ta rungume su, “nayi kewarku, sosai " ta faɗa, Abbu yace “yanzu dai ba surutu za kuyi ba, ku je kuyi wanka, ku ci abinci, Ummie ta dafa muku abinci mai daɗi ya faɗa, duk su Faiha part ɗin Ummie su ka nufa, suna ta yaba kyan Jahmeel, da yadda ya ke da kamala, ɗaya daga cikin ɗakunan part ɗin Ummie ta kai Jahmeel, “ɗana kayi wanka ka fito mu ci abinci ", murmushi kawai ya mata sannan ta fita, toilet ya shiga yayi wanka, ya fito.

   A ɓangaren Fayroz ma wanka tayi su Fareed su na zaune su na jiranta ta fito, sai fira su ke yi, suna labarin makaranta. Fitowar ta daga wanka kenan ta shirya, sannan ta fito parlor, murmushi Ummie ta sakar mata tace “je ki kira yayanki", ta juya kenan sai gashi ya fito, wata shadda ce yasa tayi mishi kyau, da ƙyar ta samu ta fitar da numfashi, kasa sauke idonta tayi a kan shi, bata taɓa gani Jahmeel cikin irin shigar nan ba yayi kyau sosai abin shi, jin ana kallon shi yasa ya ɗago ƙaraf su ka haɗa ido, cikin takun shi na ƙasaita ya ƙaraso gabanta, haɗa cikin shi da nata yayi a hankali yayi ƙasa da bakin shi zuwa sai tin kunen ta “ki rage kallon mutane kar su yi tuntuɓe " ya furta yana kallo cikin idonta, kallon ƙwayar idon shi take yi a lokacin da take jin numfashin ta na shirin ɗaukewa, su Faiha kuwa sai kallon su suke yi, Ummie ce tayi gyaran murya, da sauri Fayroz ta jaye jikinta cikin jin kunya, abinci su ka ci, duk kunya ta kama ta, dan ita har ta manta da su Ummie a parlorn, murmushi Jahmeel ya saki mai sauti dan shi ko a jikin shi, to miye a ciki, take wani jin kunya kamar shi saurayinta ne.

  Bayan sun gama cin abincine su ka zauna parlor suna fira, FAYROZ da su Fareed na labari, Farzana da Ummie suna fira, jefi-jefi Jahmeel yana sa bakin shi a firar su Ummie, wani lokacin kuma firar su Fayroz,sallah aka kira dan haka kowa ya nufi masallaci domin yin sallah, Ummie kuwa ɗaki ta nufa, Jahmeel kuma yace bazai je masallaci ba, a gida zai yi, Faiha tace “to ka ja mu sallah ", haka kuwa aka yi kowa yayi arwala suka shiga wani ɗaki sallah su ka yi tare, sannan aka buɗe ƙur'ani a tare su kayi karatun, sannan su kayi shafa'i da sufuri banda Jahmeel da yace shi sallar dare zai yi.

    Bayan sun gama ne kowa ya wuce ɗakin shi, Jahmeel kuma ya ɗauko system ɗin shi ya fara aikin ma'aikata ta online, Ummie kuwa jin motsi a bayan ɗakin ta yasa ta zira takalmin ta ta fito, sanye take da rigar da Abbu ya siya musu haske-haske ta gani, jin muryar su tayi, haka ya tabbatar mata da ba na gida bane, cikin sauri ta laɓe wani guri, su kuwa ƴan dabar jin motsi yasa su ka fara haske-haske, can su ka ga wata mata tana leƙe, daga gurin da take yayi nisa su gane wacece, haka yasa su ka zagaya ta bayanta, wuƙa suka soka mata ta baya, wata irin ƙara ta sake, wanda yasa suka ruga da gudu suka dira domin barin cikin gidan.........

Anan zan dasa aya....... ✍️

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️⚔️⚔️⚔️

FAYROZ❤️❤️Where stories live. Discover now