Chapter 501-505

22 0 0
                                    

           💮💮💮💮💮💮
                     FAYROZ
           💮💮💮💮💮💮

Tsara labari da rubutuwa :Queen Nasmerh

Chapter 501-505
*********************************
Ƙarar ihun da Jahmeel ya ji a waje yasa shi saurin rufe system ɗin shi tare da fitowa da sauri, inda suka yi karo da Fayroz ita ma ta fito zata nufi waje, da sauri suka fita, Abbu ma fitowa yayi dan ma'aikatan shi sun mishi waya akan cewar sun ji ƙarar mutum kuma wasu sun dira, fitala Jahmeel ya haska, da sauri Fayroz ta zare ido ganin Maman Fahad cikin jini, Ummie da ke laɓe a ɗayan bango ita ma da sauri ta fito, ta nufo gurin, tsats-tsaye suka yi suna tunanin yadda aka yi wannan aika-aika, wa zai kashe ta a irin lokacin nan, Maman twins ma tana gurin, Ummu Fateema kuwa ko a jikinta, magana ta fara yi “sai da nace karta fita, wai ita a dole sai taje ta ga yadda za'a kashe Ummien Fayroz ai gashinan ta gani a barzahu"Ummu Fateema ta faɗa tana wucewa cikin gida, sojojin da ke gadin bayan gidan ne su ka shigo riƙe da ƴan ta'adda, “your excellency mun kama su "ɗaya daga cikin sojojin ya faɗa, Abbu yace “great job, ku tsare su har sai sun faɗi gaskiya kafin safe", “ohk sir "su ka faɗa su na sare mishi.

   Ɗaukar ta Jahmeel yayi su ka shiga cikin gida da ita, tun cikin dare Abbu ya kira su Fahad, da Faheem, da Farouq,da Fawad, kiran Mijin Fadeeda yayi yace su taho gobe da sassafe, sannan ya kira Fareeda da tayi tafiya yace itama gobe ƙarfe goma ta mata cikin gidan nan, sune yaran maman Fahad da ya zama dole su kasance gurin, kiran su Fateema, Fawaz, Farhana, Fu'ad da Fiddausi yayi ya sanar da su rasuwar maman Fahad, sannan ya faɗa musu kar wanda us faɗa ma yaranta, a bari idan sun zo su gani.

   Rufe ta aka yi, Ummie da Maman twins su ka kwana da gawa, Ummu Fateema kuwa duk amintakar su barci ta koma tayi, Abbu da Jahmeel kuma suna gurin da ake ba ƴan ta'addan horo, har aka yi kiran sallah basu faɗi gaskiya ba, sallah su ka je yi, sannan aka barsu da sojojin da ba musulmai ba.

    Bayan an gama sallah Faheem ya iso, dan shi tunda Abbu ya kira shi hankalin shi yaƙi kwanciya, cikin gidan su ka shigo tare da Abbu da Jahmeel bayan sun gaisa, ɗakin horo su ka shiga tare, Abbu be faɗa mishi komai ba, sannan idan ka kalli Faheem zaka ga tarin tambaya a idon shi, ganin wasu maza ana dukan su yasa ya samu ya zauna yana so ya fahimci me suke faɗa, ganin yayi an jona electronic shock a ruwa, yasa shi ƙara matso wa, “bazaku faɗi gaskiya ba? "wani soja ya faɗa, shiru su ka yi, ƙafafun su aka danna cikin ruwa sai ihu su ke yi, ɗaya daga cikin su yace “zan faɗi gaskiya", kashe socket ɗin aka yi, sannan ya fara magana “Maman Fahad wato First Lady ita ce ta bamu umurni mu kashe wannan matar ", ya faɗa yana zaro waya daga cikin aljihu, nuna masu yayi da sauri Jahmeel ya zare ido yace “Ummie", Abbu da tuni ranshi ya gama ɓaci baice komai ba, sojan yace “muna jin ka", nan ya kwashe labarin duk yadda su ka yi da bayanin da ta musu aka matar, Faheem ne ya tashi “kuyi haƙuri nasan Mamana bazata taɓa barin wannan halin ba "ya juya zai fita kenan, Jahmeel yace“tsaya mu tafi tare", fitowa su ka yi gaba ɗaya har sojojin da ƴan ta'adda suka nufi cikin parlor inda aka aje ta, Faheem a rikice yake kallon Ummie ba yanzu aka ce an kashe ta ba, buɗe gawar Abbu yayi sannan ya juyo ya kalli ƴan ta'addan yace “cikin rashin sani kun kashe wacce ta saku aikin ", da sauri Faheem ya matso gaban gawar, tabbas mama ce wannan ya faɗa a ranshi, wasu hawaye masu zafi suka sauko a kuncin shi, ba abunda yafi mishi ciwo irin Maman shi ta mutu a lokacin da bata tuba ma ubangijin ta ba, gashi da mugun nufi a ranta, shi mutuwar ta bata mishi ciwo sosai ba irin yadda ta mutu lokacin da bata tuba ba, saboda yasan mutuwa tana kan kowane mumini, amma ba irin wadda Maman Fahad tayi ba, inda yau kashe ta aka yi da gayya to da komai zai zo cikin sauƙi, amma wannan muguwar manufar ta ce ta dawo mata.

  Abbu sawa yayi aka kama su, kafin ƙarfe 10:00 duk yaran sun iso, har Fareeda, dan hankalinta a tashe yake kar ace wani abu ya faru bata sani ba, mummunan saƙon da suka tarar ya fi komai ciwo, dan ko wane irin hali uwa take da shi idan aka ce yau ta rufe ido tabar duniya to dole ƴa ƴanta zasu yi kukan rashin, duk yadda uwa take muguwa a wani ɓangaren zata so ƴa ƴanta da dukkannin zuciyarta, Fadeela ma kukan halayen da Mamanta ta mutu dashi take yi ba mutuwar ba, duk da akwai zafi rasa uwa, amma zafin uwar ta mutu kuma ta fuskanci azabar ubangiji yafi komai ciwo.

   Ummu Fateema bata fito ba har aka yiwa maman Fahad wanka aka kaita gidan gaskiya, kai duniya ina zaki kai mu, duk mugun aikinka kana da ƙarshe, yau ina Faisal yake, ga mamanshi ita ma ta bishi, duk ɓarnar da suke yi an wayi gari babu ko ɗayan su, Abbu kuwa har su Janeesa ya faɗa ma, haka yasa suka biyo jirgin safe zuwa nigeria.

   Da misalin ƙarfe 2:30 na rana su Janeesa suka iso, tare da su aka yi zaman gaisuwa, inda Janeesa ta sauka ɓangaren Ummie, shi kuma Lateef ya sauka ɓangaren Abbu, Aidah kuma ta sauka a ɗakin Fayroz, Mahboob kuma a ɗakin Jahmeel, shi Jahmeel mamaki yake duk gaisuwa ce ta kawo su nan ko kuwa, haka yasa ya tambayi Mammy, inda tace tazo ne taga ahalin ɗan uwanta, shiyasa suka taho tare da Aidah bayan kwana uku da rasuwar Abbu ya tara su babban parlorn shi, magana ya fara yi kamar haka “bayan duk abunda ya faru ina mai ƙara miƙa gaisuwa ta zuwa ga ahalina, sannan ina so na gabatar muku da ƴar uwata Janeesa da na daɗe ina nema, sai zuwan da nayi saudi arabia wannan karon na gano ta "ya ƙarasa maganar yana nuna ta, dukan su sunji daɗin ganin ta, Abbu yace “wannan shine babban ɗan ta Jahmeel, waccan kuma Aidah, wannan ne mijin ta" ya faɗa yana nuna Mahboob, kowa a ɗakin yayi farinciki, dan yanzu har Fahad ma yayi sanyi akan mugun halin shi, dan ya fahimci ba inda zai kai shi, yanzu mutuwar Maman Fahad ta zama wa'azi a gare su.

IDAN ZAKA GINA RAMIN MUGUNTA KA GINA SHI ƘARAMI 💃🏻💃🏻💃🏻

ANAN ZAN DASA AYA.......... ✍️

I LOVE U ALL.

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️⚔️💃🏻💃🏻💃🏻♻️

FAYROZ❤️❤️Where stories live. Discover now