Chapter 91-95

27 3 0
                                    

💮💮💮💮💮💮
FAYROZ
💮💮💮💮💮💮

https://t.me/joinchat/nBavJtqJ_LA4NGE0

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*********'
Page 91-95
**************

Ran Abbu yayi matuƙar ɓaci sosai, miƙewa yayi yace "kuyi abunda kuke so tunda ni bani da girma a idon ku "fita yayi a fusace.

FAYROZ ma fita tayi zuwa ɗakin ta, imani duk ya cika ta, ita bata taɓa ganin irin rayuwar ba.

Wanka ta shiga tayi ta shirya sannan ta dawo ɗaki ta kwanta, bata tashi ba sai da taji ladan yana kiran sallah, arwala tayi sannan ta kabbarta sallah.

Bayan ta gama ta yi addu'a, haka kawai ta samu kanta da cewa "alkhairin Allah ya kai maka duk inda kake my boss"

MASU KARATU DAFATAN KUN SAN WAYE BOSS ƊIN FAYROZ (JAHMEEL NE).

Murmushi tayi tace "Allah sarki duk yadda kake takura min bazai kai yadda zan fuskanci matsala anan ba, Allah ya so ni ma na iya Hausa da abun ya fi haka ".

Tunawa tayi da lokacin da Ummie ta kira wani mutum yana koyawa FAYROZ hausa lokacin tana da shekara 7 a duniyar "Ummie miyasa kike so na iya hausa", murmushi Ummie ta mata tace " bazaki gane amfanin ta ba sai lokaci yayi, ni dai kawai kimin wannan alfarmar ki iya abunda za'a koya miki".

Hawaye ta share tace " I miss you Ummie bari na kira ki ".

Wayarta ta ɗauko tayi dialing number Ummie, bugu biyu kawai tayi Ummie ta ɗaga, da murmushi a fuskar ta tace "Assalamu Alaikum, FAYROZ", wani sanyi FAYROZ taji jin muryar mahaifiyar ta tace "Ummie ya gida, nayi kewar ki ", "ni ma haka FAYROZ, ya mutanen gidan, da fatan dai baki da wata matsala", sauke wata nannauyar ajiyar zuciya FAYROZ tayi tace " eh Ummie kowa na lafiya, ba wata matsala ", sun jima suna fira sannan tayi mata sallama.

Tunawa tayi da NAASHEETA, to ina zata samu number ta, tunawa tayi da, saudi basic industry, idan tayi searching a yanar gizo zata samu bayanan kowane ma'aikaci da number shi, dan haka ta shiga yanar gizo, nan tayi search NAASHEETA cikin iyawar Allah ta samu number ta.

Kira tayi, wayar na ringing amma ba'a ɗaga ba, sake kira tayi sannan NAASHEETA ta ɗaga da sallama a bakin ta, amsawa FAYROZ tayi, wani ihun daɗi NAASHEETA ta saki " besty dama ashe zaki neme ni", murmushi FAYROZ tayi tace " ina so na kira ki amma banda sim card ɗin ƙasar nan sai yanzu na samu ", ba ƙaramin daɗi NAASHEETA ta ji ba, tace "kai amma kin kyauta, ranar naje gidan ku, Ummie ta ce min kina gurin baban ki", "eh wallahi "FAYROZ ta faɗa.

NAASHEETA tace " amma baki taɓa bani labarin Abbu ba, kullum Ummie kawai nake ji", FAYROZ tace "yadda kika ji labari ƙwatsam nima haka ya same ni, ban taɓa tunanin mahaifina yana raye ba ", NAASHEETA tace "to shikenan, ina taya ki murna, da fatan dai duk kuna lafiya", "eh NAASHEETA duk muna lafiya ", nan suka ɗan taɓa firar gurin aiki, da yadda ta samu number ta, sannan suka yi sallama, akan NAASHEETA zata sake kiranta su gaisa da ADEEL, dan sai yau take jin NAASHEETA tayi aure.

MASU KARATU IDAN BAKU MANTA BA, LOKACIN AUREN NAASHEETA, FAYROZ WAS UNCONSCIOUS (BATA CIKIN HAYYACIN TA).

Wayar da tayi da NAASHEETA duk sai taji daɗi, an ɗan ɗauki lokaci basuyi magana ba.

*************
Daleel yana kwance yaji text message ya shigo wayar shi, number NAASHEETA ya gani, buɗewa yayi yaga number FAYROZ ce, kiran NAASHEETA yayi yace "good job, ya akayi kika samu number FAYROZ ", "kirana tayi" NAASHEETA ta faɗa.

Bayan sun gama waya ne, ya kira ta, "hello FAYROZ ", murmushi tayi jin muryar me magana, tabbas ko a mafarki taji muryar Daleel zata gane.

"hello Daleel" ta faɗa, murmushi yayi yace "how are u ", "ina lafiya" ta faɗa, "ranar na kira NAASHEETA take faɗa min ai kina Nigeria gurin mahaifin ki ", shiru tayi kafin ta ja dogon numfashi tace "eh wallahi tafiya ta zo min bazata, ya Dubai dafatan lafiya kake", "eh Alhamdulillahi, Dubai gatanan muna sha, ya Nigeria ", murmushi tayi tace "ga Nigeria nan, Alhamdulillahi", "to shikenan dama kira nayi mu gaisa, ki huta ", FAYROZ tace "nagode Allah ya bar zumunci, ka gaida su mama", "insha Allah, nima ki gaida min Ummie, sannan ki tambayar min ita miyasa ta hanani ke ", kashe wayar yayi ba tare da ya jira me zata ce ba.

Maganar da Daleel ya faɗa ta ɗaurewa FAYROZ kai, saboda haka ta sake kiran Ummie, Ummie dake zaune kan kujera taga wayar ta na ringing, ganin FAYROZ ce mi kiran ba ƙaramin mamaki tayi ba.

Ɗagawa tayi sannan tace "FAYROZ ina fatan dai lafiya? , kika sake kira! ", "eh Ummie, lafiya, dama ina so na tambaye ki ne", murmushi Ummie tayi tace "baki da matsala ", "miyasa kika hana Daleel aure na? " FAYROZ ta faɗa, Ummie tace "saboda ina tsoron ace waye mahaifin ki, aji ke ƴar Nigeria ce, ƴan uwan shi bazu yadda ya aure ki ba ", murmushi FAYROZ tayi tace "ohk Ummie shikenan dama, ki kula" kashe wayar tayi sannan ta fito parlor dan cin Abinci.

Abinci taci, sannan ta fita zuwa ɓangaren Abbu, da sallama ta shiga, yana parlor yana cin Abinci ta shigo, zaunawa tayi ta jira shi ya gama, sannan ta gaida shi tace "Abbu, dama na zo ne aka abunda ya faru ɗazu, kayi haƙuri ", murmushi yayi yace "zuwa yanzu nasan halin su, su ɗin yara na ne, ban isa na canza haka ba, na saba da waɗan nan halayar tasu, karki damu kinji, Allah ya miki albarka, sannan ki riƙa zuwa kina gaida matana, su ma ɗin iyayen ki ne, Kinji", "insha Allah, Abbu zan na zuwa "

Tashi tayi ta fita zuwa ɓangaren Maman Fahad, Fareeda da Faisal ne zaune a parlor suna kallo, tana shigowa suka ja wani dogon tsaki, zaunawa tayi bata kula su ba, dai dai lokacin Maman Fahad ta shigo parlorn, zaunawa tayi tace da yaran ta "me ya kawo wannan ƙazamar yarinyar nan gurin ", Fareeda tace "gatanan ki tambaye ta", FAYROZ dake zaune ƙasan carpet tace "Ina wunin Maman Fahad ", da harara Faisal ke binta yace, da bata wuni ba ai bazaki ganta ba", ita Kuwa maman Fahad ko kallon banza FAYROZ bata isheta ba, tashi FAYROZ tayi ta bar ɓangaren, part ɗin Maman Fateema ta nufa.

ANAN ZAN DASA AYA...... ✍️
MU HAƊU A NEXT CHAPTER

NAGODE SOSAI

VOTE
COMMENT
AND
SHARE
PLSSSSS🙏

TSARA LABARI :QUEEN NASMERH👑 ✍️💞💞

AQALAMIN MU NE: QUEEN NASMERH & MOM MUSAYYID 💓💓💕💕
ALQALAMI YAFI TAKOBI 🖋️✍️💕💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋

FAYROZ❤️❤️Where stories live. Discover now