Chapter 86-90

27 3 0
                                    

💮💮💮💮💮💮
FAYROZ
💮💮💮💮💮💮

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Page 86-90

****************

Haɗe rai yayi ganin Faheem, duk duniya ba wanda zai iya yin haka idan na shi ba, fuskar shi ɗauke take da murmushi yace "Farooq ka koyi girma mutum ko ina yake, ko da kuwa baka sanshi ba", Farooq kuwa da ya ƙule yace "senior Faheem ka daina min haka, sanin kanka ne bana son irin abun nan "ya faɗa tare da fizge hannun shi, yau da ba Faheem bane ya mishi abun nan ba wanda zai hana ya mishi cin mutunci.

FAYROZ dake tsaye tana kallon ikoh Allah tace "nagode", murmushi ya sake yi, sannan yace "babu komai ", wucewa sukayi zuwa gurin taron inda kowa a parlorn ya taru yana jiran shigowar Abbu.

Faisal haushi duk ya cika shi, yasan dai wannan taron bazai wuce akan FAYROZ ba.

Suna zaune, sunfi awa biyu sannan, Abbu ya shigo, maman Fahad, ita zaune kan kujera, maman Fateema ce kusa da ita, dama duk wani munafurci tare suke yin shi, maman twins kuwa tana daga gefe tare da yaran ta.

Fahad , , Farooq ,Fareeda ,Fawad, Faisal suna guri ɗaya, Faisal da Fareeda na basu labarin FAYROZ
Faheem da Fadeela kuwa sunyi nesa dasu dan su acikin yaran hajiya munawwara sune kawai ba ruwan su.

Fateema ,Fawaz ,Farhana ,Fu'ad ,Fiddausi,su ma tare suka zauna dama kowane ɗaki tare ake zama.

Faiha , Fareeha, Farzana , Farhan da Fareed, sai maman su tare suka zauna kusa da FAYROZ, wanda agidan Abbu yasan bai da matsala da Maman twins da yaranta dan ita macece mai tunani.

Banda su munawwara masu kwakwalwar kifi.

Abbu zaunawa yayi sannan ya gyara muryar shi, "assalamu alaikum, dafatan duk kun iso lafiya ", amsawa sukayi duk da wasu sun badan ransu ya so ba.

"dama na tara ku nanne saboda ganawa da juna, da kuma ƴar uwarku kuma yayar ku, FAYROZ, wadda itace babba ƴa agareni, kuma babba yaya ga duk kan ƴan alhalin nan"

Murmushi Faiha tayi, zatayi magana kenan Abbu ya dakatar da ita, dan ƙa'idar shi ce baya magana cikin magana, sai ya gama sannan ya ba da damar yin magana.

"sanin kanku ne, duk wanda ya tashi agidan nan yana jin ina maganar FAYROZ, ƴar lele na kenan, ba wanda be san irin yadda nake burin ganin ta, sannan ba wanda be santa a hoto ba "

Gyaɗa kai Fareeha da Farzana sukayi, sannan Abbu ya cigaba da magana "to yanzu ciki iyawar Allah ta dawo gare ni, ina so dukkan ku kusani, FAYROZ yayarku ce, sannan kuma dole ne ku bata wannan girman na zama yayar ku, idan na samu saɓanin haka ranku in yayi dubu sai ya ɓaci "Faisal ya haɗe rai, Abbu da ya lura dashi yace "kai kuma Faisal, na ji abunda kayi, duka duka shekarar ka nawa da zaka fara yiwa mutane rashin kunya, to dan Allah kar ka fasa".

Maman Fahad ce tayi magana tace " A'a fa your excellency bazan yadda da wannan cin kashin ba, ya za'a yi ka dinga ma yaro na faɗa, ai ɗa ba fin ɗa yayi ba "
Kallon ta yakeyi dan ko kaɗan beyi mamaki ba, wannan yana ɗaya daga cikin halin ta 🙄, ita a rayuwar ta ɗanta baya laifi.

"to shikenan, kar ku fasa abunda zakuyi" Abbu ya faɗa, FAYROZ kuwa kallon ikon Allah takeyi, ita bata taɓa ganin haka ba, ace ba girmamawa tsakanin mata da miji.

Abbu yace " FAYROZ, waɗan nan sune ƴan uwanki, Fahad shi yake bi miki,yana da Shekara 30 a duniya, wannan ce mahaifiyar shi, shine ɗana na farko a maza, sai Fateema, ya nuna Fateema, shekarar ta 29, ƴar Bilkisu ce itace mata ta ta uku, Fateema ce ƴar ta ta farko, ana ce mata ummu Fateema ya nuna Ummu Fateema, sai kuma Faheem ɗakin su ɗaya da Fahad yanada shekara 28,Fawaz yake bi mishi, shekarshi 27 ƙanin Fateema ne, sai Farooq yana da shekara 26,shima maman su ɗaya da su Fahad, sai kuma Farhana, sherarta 25 ƴar Bilkisu ce wato ummu Fateema, sai Fareeda, shekarata 24 ƴar maman Fahad, sai kuma sai kuma Fu'ad shekarar shi 23 ɗakin su ɗaya da Fateema, sai Fawad 22 years gareshi, ɗan maman Fahad ne, sai Fiddausi mai sunan mamana kenan Kuma autar ummu Fateema, shekarar ta 21, sai Fadeela ƙanwar su Fahad, 20 years gareta, sai kuma Faiha itace ƴar farko gurin Salima, Amaryata ana ce mata maman twins, Faiha is 19 years, sai kuma autan maman Fahad wato Faisal, shekarar shi 18, sai kuma Fareeha, farzana, Farhan da Fareed duk yaran Maman tweens ne, Fareeha is 17years old, Farzana na da shekara 15, sai twins, Farhan da Fareed shekarar su uku "

Murmushi FAYROZ tayi, taji daɗi sosai da Allah ya bata tarin ƙanne har haka, cikin harshe ta da Hausa bawani zama tayi abakin ta ba tace "Abbu, naji daɗi sosai da nasan su, amma meyasa bamu zama tare", murmushi yayi yace "ai yawancin su sunyi aure, Fareeda, Faisal, Faiha, Fareeha, Farzana, da twins kawai ne basu yi aure ba ", gaɗa kai tayi tace "masha Allah", Fareed yace "Abbu baka faɗa mana shekarunta ba, amma naji kana faɗa mata namu ", dariya FAYROZ tasa tace "Fareed am 32 years old", washe haƙora yayi yace "Ke ina mijin ki ", murmushi tayi tace "bani da shi", Fahad ne ya tashi zai fita, "kai zo nan ina zaka "Abbu ya faɗa, "ai naga ka gama nuna mu gara na tafi ni na ɗauka ma wani abu ne mai mahimmanci, ashe wannan yarinyar ce zaka nuna mana", Farooq da yake zaune ya tashi yace " ni wallahi da ganin wannan gara Inyi hasara", Abbu zai yi magana kenan, Fawaz ya tashi yace "nima kunga tafiya na, wannan bitch ɗin za'a nuna mana, me kama da aljanu shine za'a sa mutum ya baro gurin aikin shi"na ɗakin ya hau hayaniya kowa da abunda yake cewa, "kaiiii! " suka ji an daka musu tsawa, Faheem suka gani, "ku miyasa baku da hankali" Faheem ya faɗa, "ai ko ba komai ku girmama Abbu, shi ɗin mahaifin mu ne, Abbu kayi haƙuri ni kam zan wuce "ya faɗa tare da barin ɗakin taron, ya tsani irin halin nan na ƴan uwanshi.

MU HAƊU A NEXT CHAPTER DAN JIN YADDA ZATA KAYA.

LOVE YOU ALL MY READERS.💋💞💞💞

TSARA LABARI :QUEEN NASMERH ✍️💞💞💞

ALQALAMIN MU NE :QUEEN NASMERH & MOM MUSAYYID 💃💞💞💞💋

ALQALAMI YAFI TAKOBI 🖋️💓💓💓💓💓💓💓💓💓💓

FAYROZ❤️❤️जहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें