Chapter 201-205

31 3 0
                                    

💮💮💮💮💮💮
FAYROZ
💮💮💮💮💮💮

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*
********************
Page 201-205
***************************

**WANENE JAHMEEL**?

A wani katafaren gida ne wanda aduk faɗin Saudi Arabia ba irin shi, gida ne da kowa yake alfahari da shi, gida ne da ba irin shi, wato gidan LATEEF, wani hamshaƙin me kuɗi ne, shi mutum ne da yake yawon ƙasashe, sannan mutum ne da ya tsani ƴa mace, idan aka ce mutum ya haifi mace ji yake da ƙarfin ikon shi dama ya kashe ta, amma ne ba zai iya ba saboda duk kuɗin sa be kai kuɗin ƴan ahalin Ghushan ba (wato mahaifiyar FAYROZ), saboda haka ne suka rinjaye shi, in ba haka ba da an kashe mata ba adadi a Saudi Arabia.

Saboda tsarin LATEEF na ƙin mace yasa ko aure beyi ba, kwatsam wata rana ya dawo saudiya sai ya haɗu da wata budurwa me kyan gaske, a lokaci ɗaya yaji ta mishi.

Zuwa yayi ya tunkare ta "ji mana ƴam mata "ya faɗa yana dakatar da ita, ita kuwa bata kula shi saboda sauri takeyi, hakan da tayi yayi matuƙar ɓata mishi rai, sawa yayi a bita agano inda take, sannan a shiga gidan su a sace ta.

Haka kuwa akayi, ranar bata kwana gidan su ba, cikin dare aka ɗauko ta, rufe mata fuska akayi sannan aka kawo ta gidan, kwanan ta uku bata saka shi a ido ba, ita bata ma san waye ya kawo ta ba, kuma bata san gurin wa aka kawo ta ba, sai dai kawai taga an kawo mata abinci sannan an wuce, ba aikin da take yi sai wanka da cin abinci sai kuma aikin barci.

Yau kamar kullum ta tashi, wanka tayi sannan ta dawo kan gado ta zauna, tunani takeyi ko wane hali iyayen ta suke, ji tayi an buɗe ƙofa, LATEEF ne ya shigo, da izza yake takowa har ya iso gaban ta, ita kuwa ji take yi zuciyar ta na bugawa dum-dum, zuwa yayi ya tsaya gaban ta kamar wani zaki, kallon shi take yi sai yanzu ta tuna fuskar shi, a ranar da aka sace ta da rana ta ganshi, Allah yasa ba kashe ta zai yi ba, "kin san me, ban damu na san sunan ki ba, ki riƙe shi akan ki, zaki dinga amfani da INBIHAAJ (a cheerful young lady), ya faɗa a hankali sannan ya fita, rufe idon ta tayi, bata san lokacin da hawaye suka fara bi a kuncin ta ba, wannan wace irin rayuwa ce.

FAYROZ❤️❤️Where stories live. Discover now