Chapter 706-800

56 2 0
                                    

  💮💮💮💮💮💮
                     FAYROZ
              💮💮💮💮💮💮

Tsara labari da rubutuwa :Queen Nasmerh

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
https://www.wattpad.com/user/QUEENNASMERH08?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

Chapter 706-800
**********************************

  Yau ya kama kwana biyar da yin auren Fayroz, wanka tayi cikin doguwar riga tayi matuƙar yin kyau, rigar lilac colour ce me stones purple, gyalen rigar ma purple ne, flat shoes ta saka, wayoyinta guda biyu ta ɗauka ta saka a jaka sannan ta rataya jakar, fitowa tayi tana tafiya cikin takunta, Parlor ta sami Jahmeel zaune, masu karatu da farko naso in rikice, na kasa yadda kwana biyar yin aure yasa mutum ya canza haka, ya ƙara ƙiba yayi wani fari irin na kwanciyar hankali, sanye yake da wani yadi baƙi, ɗinki yayi mishi kyau sosai, jin ƙamshin turarenta yasa shi ɗagowa ya kafe ta da ido, da murmushi a fuskarta har ta isa gabanshi.

  Tashi yayi “ NURUL AYN "ya faɗa cikin wata murya me daɗin sauraro, mai ratsa zuciya, “ kinyi kyau" ya sake faɗa, “nagode Nurul ayn "ta faɗa, hannunta cikin na shi su ka fita.

Saudi basic industry suka nufa, mutane ne tsaye  a gaban ma'aikatar, fitowa daga motar inda mutane suka sha jinin jikinsu ganin Jahmeel, zagayowa yayi ya buɗe mata ƙofa, a hankali ta fito, hannunshi ya haɗa da nata, a hankali yana murzawa, kowa kallonsu yake yi, yau za'a yi taron taya Jahmeel murnar auren shi da Fayroz.

Wani Babban hall suka shiga, wanda yasha decoration, gurin cike yake da mutane, 4 person per table, gurin ya tsaru, guri suka samu suka zauna inda mutane suka shiga displaying talent ɗin shi yake yi, wasu suka yi rawa, wasu kuma suka yi short drama, da larabci ake maganar, dan haka masu karatu ban fahimci komai ba.

  Mc da aka kira gurin ya fara magana akan Jahmeel ya fito, cikin ƙasaita ya nufi kan tsage ɗin, inda wutar gurin ta fara canzawa cikin kaloli, magana ya fara yi kamar haka, “ da farko ina godiya gare ku duka, nagode sosai "murmushi yayi, sannan yace “bazan daina gode miki ba, kin bani farinciki, kin bani duk abunda nake so, a yau ɗin nan a gaban kowa ina so na faɗa miki kece rayuwata, kin cika ni, dan ki kawai nake rayuwa, bazan iya biyan ki da soyayyar da kika nuna min ba, sai dai in miki addu'a Allah ya saki aljanna, sannan kuma na mallaka miki saudi basic industry duka", hawaye suka zubo a kuncinta, hawayen farinciki, kiranta yayi akan ta tako kan tsage ɗin, buɗe mata hannu yayi ba tare da ɓata lokacin ba ta faɗa jikinshi, sun fi minti uku a haka, sannan ta ɗago ido tana kallon shi, hannun shi duka biyu akan kafaɗunta, cikin kuka take magana“ nagode, kai ɗin nan ka bani soyayyar da wani bai taɓa bani ba, ka kyautata min ta hanyoyi daban-daban, bazan iya biyan sadaukarwar da ka min ba, ƙaunarka kawai zan iya yi har ƙarshen rayuwata, ina sonka Jahmeel da zuciya ɗaya da rayuwata duka, bazan juri rashinka a kusa dani ba, rayuwata mallakinka ce kai kaɗai", hannunshi ɗaya sauko da shi zuwa saitin fuskarta ya share mata hawaye, “yanzu lokacin kuka ba naki bane, kinyi kuka ya isa haka, yanzu lokaci rayuwa ne mai tarin soyayya, farinciki da kulawa har abada ", sake rungume ta tayi, gurin aka hau taɓi, ko ina na gurin flash kake gani, sosai mutane suka ji daɗin ganin su tare, kyauta ya dinga yi gurin, dan Jahmeel ya tara kuɗin da ko ba saudi basic industry, abune me wahala yayi rashi, nunawa mutane sabuwar mai company ɗin yake yi, kowa na farinciki.

   Ba'a watse taron ba sai bayan isha'i, da yake akwai gurin sallah, dan haka can suke zuwa suyi sallah sannan su dawo cikin hall ɗin da ake taro, mota ya buɗe mata suka nufi gida, lokacin duk sun gaji, kanta a kan kafaɗar shi, da hannu ɗaya yake driving, yayin da Fayroz ta rungume hannu ɗaya, shi kuma ya riƙe hannunta, ko da suka isa gida tayi barci, dan haka cikin salo ya jaye jikinshi daga nata, sannan ya zagaya ta ɗaya ɓangaren ya ɗauke ta, ɗaki ya kwantar da ita, sannan yayi ma motar key ta Window dake ɗakin shi, dan bazai iya fita ba.

   Kayan jikinshi ya cire, sannan ya ɗaura towel, itama kayan jikinta ya cire mata, sannan ya ɗaura mata towel, ya nufi toilet da ita, jin ta da tayi cikin ruwa yasa ta buɗe ido, murmushi ya mata ganin tana kallonshi, rufe idon ta tayi, a hankali yace “kina so na", buɗe idonta tayi , “faɗar ina sonka ɓarnan magana ce, ni ɗinnan ina sonka fiye da rayuwata ".

ALHAMDULILLAHI ALA KULLI HAL.

A YAU NA SAMU NA KAI ƘARSHEN WANNAN LITTAFIN 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

NAGODE MUKU DA SOYAYYAR DA KUKA NUNA MA LITTAFIN NAN.

TUNDA NA FARA WANNAN LITTAFIN BANSAN YA YAKE BA, A TAƘAICE MA BANSAN FARKO BA BANSAN TSAKA BA, BALLANTA ƘARSHE, AMMA CIKIN IYAWAR ALLAH NA SAMU NA KAMMALA LABARIN DUK DA BASO BARIN RUBUTUN, AMMA SOYAYYAR KU GA LITTAFIN YASA NA CIGABA DA YI.

INA SONKU DA ZUCIYA ƊAYA, KAMAR YADDA KUKA SANI A FARKON LABARIN MUN FARA SHI NE DA WATA AMMA  SAI TA ƘI RUBUTUN, WANDA YASA NA CIGABA, KUMA ALHAMDULILLAHI NA SAMU NA KAMMALA.

MASOYAN HAJNA MA KU SHIRYA, RANAR MONDAY INSHA ALLAH ZAKU JI, SHIMA INSHA ALLAH NA KUSA KAMMALA SHI.

KURA-KURAN DA NAYI A CIKI ALLAH YA YAFE MIN.

TAKE KISS😘😘😘😘😘MY FANS💕💗💗💗💗
TAKU HAR ABADA :QUEEN NASMERH 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

   

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 16, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

FAYROZ❤️❤️Where stories live. Discover now