Chapter 02(Wata halitta)

168 18 2
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

written by ❤️❤️sadi-sakhna❤️❤️(the legendary novelist)🌄🌄🖌️🖌️
  
💎💎WATA  RAYUWA 💎💎

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

(02)
Daukar tulun tayi cikin sanyin murya ta fita izuwa ga rafin tana sake-saken yanayin rayuwar tasu itada umminnata,da i0rin halin matsin da ta so ta tsincesu aciki,duk da karanci shekarun fariyah amma takasance mai kaifin tunani dakuma basira,sannan tanada sanyi dakuma hakuri,yarinyace mai son taga tana da abokai dazata dinga wasa dasu ,saidai a yanayin data tsinci kanta yasa ta fuskantar tsangwama da kyama daga wajen su ,wanda hakan yasa sha'awar wasa da yaran yafara fita mata akai sai yazamto rayuwanta yazama tamkar ita kadai takeyi ,sanaddiyyar aiki da mahaifiyartata takeyi bata samun lokacin ta sai sanda zasu kwanta,a lokacin kuma yanayin gajiya yashiga jikinsu basu da lokacin tattauna matsalarsu.Dahaka tana cikin tunanine har ta iso ga babban rafin dayake nesa kadan da muhallinnnasu na tsarauni,zaunawa tayi a bakin wan dutsi gefe da rafin tana karewa wajen kallo,zuwanta baifi a kirgaba wajen saidai bata tba cinkaro da abinda ake cewa na hatsarin wajen bawanda hakan yasa wajen yake bata sha'awa matuka ,domin wajen nadauke da wasu irin tsuntsaye masu kyan gani harma da yan dabbobi dasuke kiwo a wajen ,sanadiyyar kyawun wajen dakuma iskar dake kadwa a wajen ga kuma ruwa sai hakan yafara kwantar mata da hankali sabanin da da ko ambatar sunan waje ke sa hantar cikinta kadawa sanadiyyar zuzuta hatsarin wajen datake ji daga bakin mutane daban daban,ta dan debi dakika a zaune wajen kana daga bisani ta tashi tanufi wajen deban ruwan da tulun a hannunta,tsugunnnawa tayi a gaban ruwan amma saita dagata da diban ruwan sanadiyyar ganin wata yar halitta mai matukar kyau na linkaya acan nesa da ita a wani bangare na kogin,shagala tayi da kallon wajen wanda har batasan lokacin data fara murmushiba,abin yadau hankalinta sosai sanadiyyar yanayin halittarsa data bata dariya sosai(abin na dauke da idanuwa manya kaman idanuwan yaro idan tsorita yaro,sannan jikinsa kuma mai kalar shudi da kore a hade,yana daukar hasken rana ,zuyawa yakeyi cike da wasa acikin ruwan yayinda itakuma ta shagala sosai da kallansa,tashi tayi ta kara matsawa kusa ganin yagama wasa da ruwan dayakeyi,ganin ya nufi wani hanyane zai bacewa ganinta yasa ta binsa a hankali batare da gantaba,basu yi tafiya mai nisaba taga yayi wata kwana inda itama tabishi da sauri,saidai yin kwanar nata keda wuya ta nemeshi tarasa.Juyowa tayi cikin rashin jin dadin bacewar tasa tadawo wajen gun tulunta,deban ruwan tayi da sauri ta nufi gidannasu zuciyar ta nadukan tar-tara,tun daga bakin kofar gidan taci karo da aryana na wani harkar tata daban,saidai ganin dawowar fariyahne ya tuno mata da ta aikata ma deban ruwa,sai asannane tafara masifar rashin dawowarta dawuri,idan da sabo tasaba da masifa dakuma azabar aryana wanda takasance tamkar abincin ta ,batare da taace kaala ba tawuce ta juye ruwan a randar uwar gidan tasu,kana tajuya tanufi dakinnasu da na kare yafishi kyan gani a ta fuskar fasali.A zaune take a dakinnasu tayi tagumi tana tunanin rayuwar tasu sannan dakuma kyakykyawar halittar da idanta yai arba da ita a rafi,tambayar kanta tafarayi kamar haka "ita a yanda ake mata bayanin jejin wajen da kuma halittunsa a tabbatar mata dacewa wajene mai hatsari da kuma abin tsoro,amma sabanin haka ita wajen ya birgeta matuka,wanda har tana sha'awar gobe tayi domin ta koma kozata hadu da hallitar datayi arba da ita a yau,duk tana tunaninne ita kadai harda murmushi akan fuskarta mahaifiyar tata tadawo daga aikin da aryana tasakata take mata akowane rana,tsugunnawa huda tayi tana kallan murmushin dake kan fuskar yar tata wanda a take ya wanke duk wata gajiya da ta dawo da ita,duk da batasan menene yasaka yar tata farin cikiba amma tayi na'am dashi matuka azuciyarta,daga kai tayi wanda sai a sannan takula da mahaifiyartata a gabanta tana tayata murmushin data gani a fuskarta,"ummi"shine abinda tafada kana kuma tace"sannu da dawowa ya aiki ummi?" "lafiya kalau fahriya ya kema aikinki da kuma rayuwar hakuri?nasan kina cikin WATA RAYUWA DA bazata ta ba yimimki dadi ba ,sannan kuma kuskuren mune nida mahaifinki,dakuma nawa laifin dabansan asalin danginsaba dana turaki wajensu,duk da suma ina tsoran dakyar su karbeki sanadiyyar keba cikkeken irnsu bace,sannan nikuma bani da ikon barin wannan kasar sanadiyyar abinda yafaru dani,amma kiyi hakuri fahriya cinaji ajikina dasannu rayuwarki zatayi kyau bakamar tawa ba kinji"da haka huda ta kai karshen maganarta cikin kuka wanda hakan yasa itama fahriya yin kukan,sannan tafara maida magana ga mahaifiiiiyar tata"ahahhh ummi ki daina fadar hakan domin ba laifinkubane kaddararkune hakan dakuma sanadin samuna ,sannan nima hakan kaddara tace kuma na karbeta hannu bibbiyu,sannan koda kinsan inda dangin mahaifin suke bazan taba tafiya nabarki ke kadai ba ummi,zan zauna dake BAZAN BARKIBA,"bayan gamam magananr taane huda tajawo yar taata ta rungume suka cigaba da kukannasu da ba wanda zai rarrashesu.

To haka rayuwar su fahriyan takasance cikin dadi da babu dadi,wanda rashin dadin yaninka dadin yawa,a bangaren fahriya kuwa tun lokacin da taga wannan halittar sai yazaman kullum sai taje gefen inda ta taba ganinsa domin dubashi,saidai ko mai almaar kamarsa bata sake ganinba tun ganinta na farko dashi,tun tana damuwa da hakan har ta fara mntawa da batunsa amma hakan ba wai ya fita a zuciyartaba.
,
Shekaru har guda biyu sun ja a inda fahriya takai shekara yanzu 16 a duniya,sai yazamana rayuwar ta yakara wuya sosai domin yazamana aikin gidan aryana kaso 80%itane taketi,domin a ganinta yakamata mahaifiyar ta tahuta a yanzu tunda ta taso,saidai huda kwakwata bata son barinta yin aiki sosai domin ita hakan a ganinta zata shiga hakkin yarinyarne sosai.Yanzunma hudane a tsugunne tana wanke kayan hidimar gidanna aryana da baya rasa mutane dasuke ziyar tar wajen,kwalamata kira ta taji uwar gidannata tayine yasata juyowa,kyawuntane yatafi dani matuka,wai hakanma cikar budurcinta bai gama fitowa ba sannan gakuma wayewa da wuya daya dafar da fatarta,amsawa tayi kana ta tafi inda kiran yake fitowa,zuwa tayi tatsaya agabanta dan taji yanzu kuma dame tazo,karkada hannu tafarayi tana yatsina fuska wanda a jikin mutanen na bardugu ma ita fuskarta da yanayinta abin tsoro ne,"maza kije ki debomin ice a jeji kuma kidawo da wuri kafin uwarki ta dawo ta min girki,dan ku tamkar karnuka na ne ,naciyar daku kumin aiki baku da wani amfani bayan hakan,wuce kiyi sauri kitafi da wani fari da jar fuska kaman fatalwaa,"takarisa maganarta tan nuna mata hanya cikin fada.Kama hanya tayi cikin kunar zuciya na maganr da aryana ta fada mata,hakika duk da tana kokarin jure duk wata magana da ta zuba mata to wannan din daban ne da sauran domin ya shigeta sosai,saida gama kukanta sannan ta kama hanyar zuwa deban icen wanda batasan takamamai hanyar ba domin lokacin da mamarta ta bari ta koma yin hidimar dukkan gidan kuma da zuwa saye da siyowar sana'ar aryanar,wani yarone shima datake azabtar dashi ya cigaba da aikin deban icen,tashi daya su fahriyah suka nemeshi suka rasa kuma basu da ikon tambayar inda yake.
   Bayan fitarta daga gidane ta kama hanyar wani jeji nesa da anguwar tasu,wanda take da tabbacin zata samu icen a wajen,tafiya takeyi tana kara kallon wajen sosai ,har takai ga wani waje da take tunanin zata samu icen a wajen,har ta juya zata cigaba da tafiya sai hankalinta yakai ga wani waje a gefe mai ruwa akwance zuwa tai domin kallon kyawawan tsuntsayen dake wajen sai kuma idonta ya kallo abinda yafi komai ba ta mamaki ,wato halittar da ta dade tana neman inda take tsawon shekara da shekaru,karisawa wajen da take tayi a hankali domin jin tsoron kar ta sake bace mata irin na ranar data ganta,saidai abinne yabata tsoro matuka ganin halin da abin yake ciki,👣👣...........
      written by ❤️❤️SADI-SAKHNA ❤️❤️AKA the legendary novelist🌄🌄🖌️🖌️

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now